🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹*ADABI WRITER'S ASSO.*
(Home of exquisite writers)*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
👉🏹💘🏹 *PAGE 3*
Saida ta iso qofar gida sannan ta fara hawaye saboda tasan yau idan baba yakamata bazai ragamataba,Amma tunda har tasamu takaimishi alhamduillah ita ranta yayi fari.A hankali tashiga yin nocking a qofar gidan saboda yanzu bazata iya haurawa ba,Kuma tasan idan mama tayi noticing da cewar batanan zata saurari dawowarta.
Tanayin nocking na daya zuwa na biyu mama tazo ta bude,wiqi wiqi tayi da ido tace"Dan Allah mama kiyi haquri....!
Hade fuska mama tayi tace"zo ki shige?
simi simi tayi tashige da sauri tasamu wuri Kan cushion ta lafe.Abakin qofa tajiyo mama tafara yimata magana tace"yanzu imtihal abunda kikayimin kin kyauta kenan? Yanzu da ace malam ya dawo fa,qarya kikeso inyi komai,ko so kike ince mishi kin haura gini kinfita?ke yanzu duk abunda nake gayamiki kwata kwata baya shiga kunnenki ko??
"Dan Allah mama nah kiyi haquri,insha Allah bazan sake ba.
Girgiza kanta tayi tace"aa maganar haquri duk bata tasoba,kullum haka kike cewa,Kuma kisake wani laifin,shiyasa Nike cewa malam yadaina dukanki saboda ko anyi ga banza,yanzu shawara dayace shine,yazo yakaiki can gusau gidan qaseemu.......!
Cikin rudewa tazo ta rungume mama ta fashe da kuka tace"Dan Allah mama kiyi haquri,wllhy ni yanzu banason gidan baba qaseem na fasa zuwa,ni ba inda zanje...!
"Ah ah kam! Qarya kikeyi,ai daman tun can kin Sha roqata da cewar kinaso kije gusau gidan babanki kizauna dasu,toh kinga intisar na nan,ga Kuma imrana,saiki zauna kici gaba da yin makaranta a can,ko zamu samu kiriqa maida hankali,Nima kaina sai hankalina yafi kwanciya.
"Aa mama kece fa kike gayamin cewar bazaki iya rabuwa Dani ba,nikadai ke gareki,ke bazaki barni inyi nisa dake ba,ni wllhy babu inda zanje,aisu ma su intisar din suna zuwa nan ga sallah ko buki,wllhy ni bazanje ko Ina ba inbar omairr...!
Daki mama ta wuce tabar ta nan tana ta darzar kuka.
****
Imtihal H ibrahim......!
Diyace ga malam Ibrahim Halliru, dakuma mahaifiyarta hindatu Abubakar,asalin mahaifinta 'yan nan cikin garin Anka ne,yanada qani daya tal qaseem,su biyu kadai iyayensu suka haifa,bayan yayi karatun lafiya Amma bamai nisa ba yagama yafara aiki a nan asibitin anka,bayan ya fara aikin ya hadu da hindatu sukayi aure Amma ita daga garin gummi take,suna nan zamansu lafiya aurensu baifi shekara biyu ba,babansu yace yanaso qaseemu shima yayi aure,kada ya rasu baiga auren qaseemu ba,haka akayi ko qaseemu yayi aure da nafisa,basu jima ba Allah yabasu haihuwa aka sawa yaron suna imrana,toh bayan matarshi ta haihu malam ibrahim ya nema mishi admission ABU zaria yaje shima yayi karatun medicine, Yana can Yana karatu malam Ibrahim Yana nan Yana kula da matarshi da kuma ita matar qaseem din,sai da ya gama yasamu aiki nan asibitin yariman bakura specialist dake cikin gusau yana nan ahankali ya mayarda iyalinshi atare dashi,malam Ibrahim sundade suna neman haihuwa Basu samuba,saida suka shafe kusan shekara goma Sha bakwai sannan Allah ya azurta su da samun 'ya wato imtihal alokacin kuwa Imran yanada kusan shekara Sha biyar sosai sukayi murna qaseem ya nemi alfarmar malam ibrahim da ya sanya mata suna imtihal tunda su sunada imran,sunsan abun Allah bashida wuya amma qila rabon 'ya'yansu aduniya daya daya ne,tunda su biyu ne a wurin iyayensu,gashi yanzu dukkansu Allah yayi musu rasuwa,suna nan sai bayan anhaifi imtihal ne da shekara biyu nafisa ta qara haihuwa akasanya mata suna intisar,nafisa tana girmama malam Ibrahim sosai dashida hindatu,duk da cewar tasan hindatu tajima bata haihu ba, bata taba yimata gorin haihuwa ba,saboda dukkansu sunada ilimi sosai sunriga da sunsan cewar komai na Allah ne, kafin hindatu ta haihu alokacin duk imrana yasamu hutu nan qaseem ke kawoshi wurinsu sai Hutu ya qare yazo ya koma dashi,sunyi burin suma ace sun qara samun wasu saboda qaseem yayi qudurin baiwa malam Ibrahim Imran gaba daya,ko don yanda yake kula dasu sosai ya tsaya mishi tamkar mahaifinshi tun Yana yaro har yakai ga yin aure.
