🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
(home of exquisite writers)*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD @-UMMU AMEER*
👉🏹💘🏹 *PAGE 10*
Kwance yake akan kyakkyawan gadon shi yana Danna system dinshi,Anwar na kwance a gefenshi ya tsurawa system din ido shima,wani research ne yake hankalinshi gabadai Yana wurin,Anwar yace"yah omair naji abbah da mammi suna magana cewar a kwanakin nan zaka wuce saudiyya wurin karatu,da farko mammi chose cyprus for you but abbah yace saudiyya zatafi maka musamman ka qara qwarewa a larabci da qarin ilmi akan addini........!Hannunshi yasa akai yace"oh my God Anwar! Abbah ne yace kazo ka gayamin wannan ko mammi??
Tabe baki Anwar yayi yace"none of them kawai dai I decide to tell you,ka fara ji daga gareni yah omair.
Kallon qofa yayi tare da mishi nuni yace"please leave!
Narai narai yayi da ido kamar zaiyi kuka yace"but yah omair.......!
Katseshi yayi da sauri yace"outt I said!Yana fita suka ci karo da arwa tace"kaikuma lafiya kake bata rai?
"Ba yaya omair bane,wai saboda kawai na fadamishi zancen tafiyarshi saudiyya shine yace nafita.Dariya ta fara tace"do you no your problem Anwar??ka iya gulma kamar wata mace,Kuma kafi kowa sanin yah omair bayason gulma.
Tana kaiwa nan ta shige dakin omair din tayi sallama sannan tace"yah omair mammi tace kazo abbah Yana jiranka.Da sauri ya miqe tare da rufe laptop din yace"muje toh, ina mutumin yayi fushi Koh??
Dariya ta fara tace"na hadu dashi yayiwa fuskar nan kamar an hada fulawa ansakata a rana.
Sai suka fashe da dariya yace"yazo min da wani amebonshi ne shiyasa nayi sending din shi away.
Firah suke har suka isa a farlourn abbah, fridge ya nufa tare da daukko gwangwanin maltina yazo ya zauna a kujerar ke kusa da abbah yace"Abba gani?
Cikin sigar zolaya yace"firstly wayace ka batawa yaron Abba rai.
Dariya yayi ya kalli Anwar Wanda yacika fim ya dauke kanshi Yana kallon window waishi yayi fushi yace"abbah yaron Abba bayajin magana,ko yanzu idan nagayamaka laifinshi kaima saika mishi duka but bari mu rufashi ko arwa?? Ya qare maganar Yana kallon arwa Yana dariya.
Itama tace"eh abbah.
A hankali ya zo ya riqe hannun omair yace"yah omair am sorry bazan sake ba.
Yace"toh shikenan yanxu munshirya kaje kayi game da phone dina zamuyi magana dasu mammi,ke Kuma arwa kije ki fara duba assignment din naki kafin inzo......!Abbah yace"no! to day hajiya will assist her,becoz zamu wuce kaduna anjima kadan,kabarsu can da Assignment dinnan.
"Omair daman maganar karatunka ce angama komai zaka wuce University of madina.....!
"Amma abbah munyi da fu'ad cewar Cyprus.....!Abba yace"babu ruwana da wata Cyprus,madinah zakaje final,kaje ka hada kayanka zaka rakani kaduna,idan muka dawo jibi zuwa next week zaka wuce.
Sai yanzu mammi ta dago kai tace"Amma dakta iyayen fu'ad bazasuji dadiba,ganin yanda omair yake da qoqari Yana taimakawa fu'ad sukayi tunanin suje qasa daya karatu zasu taimaki juna....!
"Ya salam hajiya kubra! Dan Allah kidaina wannan zancen,kowa fa da irin abunda Allah ya ke zabamishi,ba ruwana da wani fu'ad abunda naga yafi cancanta da rayuwar yarana shi zanyi.....!
