🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
(home of exquisite writers)*NA*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD@-UMMU AMEER*👍🏹💘🏹 *PAGE 12*
Tafe suke a mota sundawo daga school,wanda Imran ne ya ba daddy shawarar cewar a daure idan da hali a siya musu mota abun sai yafi sauqi saboda akwai nisa sosai tsakanin makarantar da cikin garin gusau,baba baiso ba amma mommy ta qarfafa guiwa tare da kawo references da dama na fa'idar da motar zatayi musu,da qyar suka amince amma koshi da sharadin daga school sai school,mommy tace sun amince.
Intisar ce mai driving din saboda ita imtihal tacika tsoro bata iya kaisu har makarantar,a slow suke tafiyar imtihal tace"other half wai miyasa bazaki saurari samari ba?? Kidaina biyemin ni mrs. Omair ce kin gane.
Dariya suka fashe da ita sannan intisar tace"nikuma mrs. Mai rabo ce,i won't listen to any guy for now,sai zuwa next year,Kinga next year ya rage some months mu kambala degree dinmu,,so alokacin I will find my sweetor kema daga nan omair dinki ya dawo sai muyi aure rana daya,but yanzu idan nafara sauraren gayu wannan yazo wannan yazo zan iya bata ran baba ko daddy ace in fidda wani muyi aure,ko ban tashi ba za'a matsamin.
Kallonta imtihal take baki bude saida ta Kai qarshe tace"wai Dan Allah are you serious kinaso muyi aure rana daya??
Murmushi tayi tace"am damn serious other half, Allah dai yakaimu lokaci.
"Ameen!****
Imran Dan Allah ka saurareni,zaman nan naka haka ya isheni haba!! Hannayenta ya riqe yana dariya yace"ohh! Mama Dan Allah kiyi haquri ki daina fushinnan.....!
"Haba imran dole inyi fushi, shekara nawa yanzu,tun yaushe ka gama karatunnan ka fara kasuwanci yanzu alhamdulillah ga aiki ya samu,ai dai angode Allah,babu abunda kake nema yanzu fa ce kasamu kayi aure,nima insami suruka.
"Oh mama na Dan Allah kiyi haquri naga yau kin dau zafi da yawa,insha Allah ba'a nesa mama,auren ya kusa.
Tace"toh Allah yasa da gaske kake amma gaskiya abun yana damuna.
****
Mammi wai wannan duk na miye haka?? Tsarin gidan za'a canza baki daya ne?
Murmushi tayi tace"anwar my boy!komai na gidannan za'a canja,buki ne za'ayi na musamman,kaga Kai ka gama jss class,arwa ta qarasa secondry,yayanku Kuma zai dawo ya kambala nashi karatun,ai kaga wannan babban abune wanda za'ayi murna akai.
"Allah dai ya bamu rai da lafiya,ya nuna min dawowar omair lafiya.
Yace"ameen mammi.
Arwa dai kwance take akan 3seater tana aikinta data saba na chatting,duk taji maganar da suka tattauna akai saidai ita abunda yake ranta daban.
Sai yanzu tayi magana yace"mammi wai ni Dan Allah ya labarin mota ta da abbah ce???Cikin jin haushi mammi tace"ke shashasha ce! Shi dakta ne ya gaya miki cewar zai saya Miki mota yanzu,andaiyi maganar but ba yanzu yake nufi ba,sai kinyi karatu kingama idan zakiyi aure.
Turo baki gaba tayi tace"Amma ai mammi shi Yaya omair tun bai karasa secondary ba ma ya fara driving,toh ni fa yanzu saura some months,ai ya kamata Nima a saya min,duk na riga na gama gayawa kawayena
Amma yanzu azo ace ba haka ba.Cikin mamaki mammi tace"ikon Allah! Yo nikejin 'ya,omair din sa'anki ne iyeh? hankalinki da nashi daya ne? Kada insake jin maganar mota a bakinki kinji nagayamiki,inba hakaba wllhy ranki zai baci,a sayamiki mota yanzu hauka ake kenan,Dan Allah ni tashi kije ki duba min tuwo na yamma nayi,kawayenki zasu Miki dariya sun dade basuyimiki dariyar ba.
