CHAPTER FOURTEEN

30 1 0
                                    

🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹

*EXQUISITE WRITERS FORUM*
(home of exquisite writers)

*NA*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD@-UMMU AMEER*

🏹💘🏹👉 *PAGE 14*


Bayan wani lokaci.....!
Alhamdulillah komai ya daidaita acikin rayuwar omair,dukkan iyayen nashi bangare uku suna nuna mishi kauna ta musamman,da Inna batulu kawai ya zabi ya zauna saidai yace zai riqa zuwar musu akai akai,gefen soyayyar su da imtihal Kuma ta girmama sosai,shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninsu,bayan fu'ad yazo ganin omair sukaje gun imtihal nan suka hadu da intisar,yayinda omair da kanshi ya hada nimrah da yah imran,Wanda a yanzu ansaka auren su gaba daya sati biyu masu zuwa.

Dukkan bangarorin shiri suke na musamman babu kamar mammi,kamar arwa ce zatayi auren,bukine aka shirya na musamman, walimah aka shirya sai wunin buki,babu wasu event,kayan anko anyisu kala kala,mutane ne zasuzo masu yawa kowa da nasa mutane, daurin auren yakama gusau da Anka,sai anfara zuwa Anka daga nan adawo gusau wurin daura auren nimrah da Imran.
Duk wasu munafukai sunji kunya,idan sukaga omair saisu fara kame kame,suna neman gafararshi.

Ranar walima ansha walima lafiya Lou,da imtihal da intisar,can gefen nimrah kuwa itakadai akayiwa ta ta,domin ba gari daya bane,Masha Allah anyi walimah lafiya anqare,mammi kuwa sune a gaba itada mommy nafi,komai Masha Allah,sosai arwa tashiga ran imtihal suna mutunci sosai da ita.

Ranar asabar qarfe Sha daya na safe,qofar gidan malam ibrahim cike take tam da Dan mutum, manyan mutane ne sukazo daga gefen Dr. Hisham, Abbie,baba,daddy qaseem da sauran mutane,Mai karatu ka qiyasta a ranka girman wannan taron a ranka,qarfe goma Sha daya aka daura auren, imtihal Ibrahim da omair Tahir Aaram,sai intisar qaseem da fu'ad Muhammad Kabir,daga nan suka kwasa suka koma gusau qarfe uku na Rana aka daura auren,nimrah Tahir Aaram da Kuma Imran ibrahim.

Anci ansha alhamdulillah an watse taro lafiya,su imtihal baki abaya rufuwa,sai farinciki.
Qarfe shida da rabi,aka fito dasu zuwa gidajensu aurensu dake garin gusau,saida aka biya gidan Inna batulu da imtihal tayimata addu'ah da fatan alheri sannan aka fito da ita,tanata rusa kuka

Koda suka isa gusau gidan ummie aka wuce da ita,yayinda aka wuce da intisar gidan iyayen fu'ad,ummie tana matuqar qaunar imtihal, musamman akan irin kulawarda ta bawa omair lokacin da yake cikin damuwa,dukkan 'yan uwan omair sun nuna Mata qauna kowa rigi rigen yimata magana yake,suna nan tare da nimrah daki daya saboda ita nimrah ba'a wuce da itaba sai gobe.

Qarfe Tara aka dauketa zuwa gidan ta itada masoyinta omair, washe gari Kuma aka dauki nimrah,saida aka biya Anka da ita wurin mama,daga nan aka wuce da ita sokoto.

Lafiya Lou suke zaune, soyayya da shaquwa tashiga tsakaninsu Mai tsabta,kowa qoqari yake yaga cewar ya kyautatawa Dan uwansa,babu wani sabani a tsakaninsu,bayan aurensu da wata biyar suka wuce Riyadh wurin dangin ummie ga baki dayansu, har da Inna batulu,daman azumi ya kusa saura kwanaki kadan,nan sukayi azumi sukayita ibada har aikin hajji yazo sukayi daga nan suka dawo gida Nigeria.

Bayan sundawo gida,Abbie ya ginawa su Inna batulu qaton gida anan gusau suka dawo baki daya har malam sa'idu da rahane masoyiyar asali,harda yaranta.

Bayan shekara biyar....!
Imtihal ta haifi yara biyu,Islam da aslam,sunan Inna ne da Abbie suka sanyawa yaran.aslam ne babba sannan islam.
A yayinda itama nimrah ta kammala karatunta da take a madinah,yanzu tana nan zaune sokoto tare da masoyinta Imran da Kuma 'yarsu daya,nazli wadda suke cewa (baby)
Itama intisar tasamu 'yarta mace"Aisha humairah.

Suna nan zaune lafiya,babu fada a tsakaninsu.
Alhamdulillah arwa yanzu ta kambala karatunta lafiya,tana zaune gida har ta samu aiki ta fara zuwa,takanzo nan gidan su imtihal idan tasamu time.

Watarana suna zaune imtihal din omair,takawo shawarar yakamata ya auri arwa,domin iyayenta sun cika 'yan halak,shima ya nuna musu shi din Dan halak ne,da farko shi lamarin nata tsoratashi ma yayi,but sai ta bashi goyon baya dari bisa dari,tace wllhy babu komai aishi mijin mace hudu ne,Kuma ma irin hallacin da su mammi suka mishi ai bai kamata ya tsaya wani tunani,shine ya kamata ace ya tunano wannan ba ita ba,saboda haka itadai ta amince har cikin ranta,babu damuwa Allah ya Basu zaman lafiya,Kuma Allah ya bashi ikon riqesu bisa gaskiya da amana.

A farko da ya jewa Abba da maganar saida ya Dan yi Tunani,but alokacin da mammi taji,ji tayi kamar zata taka rawa akan farin ciki,tayi murna sosai,nan magana taje wa su ummie,Inna batulu dakuma iyayen imtihal,suma suka bada goyon baya tareda sawa auren albarka,akayi auren arwa da omair.
Nan sukaci gaba da zamansu lafiya,tare da girmama juna, qauna dakuma soyayya.
Daman shi Anwar a gidan omair yake zaune tun bayan da imtihal ta haifi Aslam,Amma fa duk da ya girma ya zama big guy haryanzu Anwar Yana nan da gulmar da ya saba lolz.

Lafiya suke zaune,idan suka time suna ziyartar juna akai akai.

*ALHAMDULILLAH*
A nan nakawo qarshen littafina na KIBIYAR SO,Ina fata zakuyi hakuri Dani,ku Kuma karbi uzuri na,nagode sosai,darasin da ke ciki, Allah yasa muyi amfani dashi,mu gyara , kuskurenda nayi,Ina addu'ah Allah ya yafemuna baki daya.

Littafinnan bai cancanci qarewa a haka ba,but dole ce tasakani,kuyi haquri.

*Nagode wa kowa da kowa dukkan masoyana akan bibiyar wannan littafin na KIBIYAR SO,saduwar alkairi*


Taku har kullum
🏹💘🏹 *OUM AMEER* 🏹💘🏹
Nike cewa saduwar alkairi.......!






You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 13, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

   KIBIYAR SO (Complete)Where stories live. Discover now