🏹💘🏹 *KIBIYAR SO* 🏹💘🏹
*ADABI WRITER'S ASSO.*
(Home of exquisite writers)*BY*
*AMEENA IBRAHEEM*
*OUM AMEER*
*WATTPAD@ UMMU AMEER*👉🏹💘🏹 *PAGE 6*
Washe gari da asussuba ta diro daga Kan gadon da suke kwance ita da intisar da gudu tayo waje taje tana buga qofar dakin mama da qarfi tana Kiran sunanta,mamar daman zaune take akan sallaya tana azkar tafito da sauri,daga nan itama mommy nafi tayo waje da sauri suna rige-rigen tambayarta ko lafiya???
Cikin damuwa tace"wllhy mama inaji ajikina omair bashida lafiya,acikin mafarki na yanata kirana,wllhy mama Ina tunanin wani abu Yana faruwa da omair!
Tsawa mama ta daka mata tace"Dan Allah rufemin baki,shashashar yarinya kawai,shiyasa kikaga wani lokacin kece kikesa inajin haushin omair din ba wani ba,kinji ajikinki bashi da lafiya saboda kece uwarshi,ki wuce kije kiyi sallah ko in babbalaki a wurin.
Mommy nafi tace"haba anty saurara,ba haka za'ayi ba,yanzu ke imtihal kije kiyi sallah kafinnan su daddynku sundawo daga masallaci sai yayanki yaje ya dubashi,shikenan ai wannan abun Mai sauqi ne.
Sai yanzu ta Dan ji natsuwar rai,tace"toh mommy bari inje.
Bayan taje ta tayarda intisar sunyi sallah sannan saiga su baba sundawo,tanajin sallamarsu tafito suka gaisa tace"Dan Allah ya Imran muje mu duba omair wllhy bashida lafiya.
Kallon kallo suka shiga yiwa juna,baba yace mata"wanene yace Miki bashida lafiya??
Zatayi magana mommy nafi tafito tace"Kai Imran kaje ka dubashi yanzunnan qanwarshi tazo,shine mukace adakata tukun har ku dawo.Mama kam sakin baki tayi tana kallon mommy nafi da sanyin safiyar nan tana ruga qarya,Don kawai ta faranta wa imtihal rai.
Baba qaseem yace"subhanallah! Toh Imran kaje ka duba miya sameshi.
Yace,"toh daddy.
Ya juyo zai fita itama tabiyoshi a baya.
Baba yace"ke imtihal Ina zaki???Wiqi wiqi tayi da ido tace"baba zanje tare dashi ne!
"Mtsw! Dan Allah zoki samu wuri ki zauna,da wannan asubar saboda bakida hankali.Baba qaseem ya kalleta yaga harta fara hawaye yace"aa malam,ka barta taje,aiga Imran nan,jeki.
Suna fita baba yace"ikon Allah kenan!wato qaseemu lamarin wannan yarinyar sai addu'ah.
Baba qaseem yace"wannan duk harakar qurciya ce watarana zai zama tarihi.
****
Suna isa qofar dakin suka ganta a balle, qirjinta na dukan uku uku suka fada a dakin,da yake haryanxu akwai sauran duhu basa iya ganin inda yake saida ya ciro wayarshi ya haska.
Cikin gigicewa ta buga wata irin muguwar qara duk Wanda yake kusa da wurin saida yaji ihunta.
Zumbur Inna batulu ta miqe tare da janyo mayafinta tafito,idan kunnuwanta ba gizo suke mata ba,toh tabbas waccan muryar imtihal ce,tambayarda ta fara yiwa kanta itace"toh miya kawo imtihal dakin omair da asubar nan??,kodai a nan ta kwana???miyayiwa yarinyar mutane??
Tana fitowa itama Inna rahane nafitowa daman sa'idu bayanan tunjiya,saboda qauyuka yake zuwa cin kasuwa yakanyi kwana biyu kwana uku kafin ya dawo.Batulu Ina zakije da asubar nan.
Bata tanka taba tayo qofar gidan itama saita biyo bayanta.Cikin rudewa imtihal tace"kagani ko ya imran?? Wllhy daman jikina yabani wani mugun abun Yana faruwa da omair.
Saikuma ta fada jikinshi ta cacumeshi tace"omair waye ya maka wannan?? Wane tsinannen ne ya maka wannan ta'asar??? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!
Ganin babu alamar motsi a tare dashi tace"nashiga uku na ya Imran! Duba ka gani bayama numfashi.
