🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒 🍒🍒🍒🍒🍒 🍒🍒🍒🍒 🍒🍒 🍒 *SAWUN BAYA* 🍒 🍒🍒 🍒🍒🍒 🍒🍒🍒🍒🍒 🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
*Na*
*_Fadeela Lamido_**Marubuciyar*_ZAKIGANE KURENKI__TSUNTSUN DAYA JA RUWA__TSUNTSU ME WAYO__MIJIN MARAINIYA__ASIRINSA YA TONU__TAMISHI ILLAH__DAUKAN FANSA__BUGUN ZUCIYA_ (heartbeat)_KOWANNE BAKIN WUTA__ME CETONA__ABUNDA ZUCIYA KE SO__BAYA BA ZANI__WATA FITSARA_ and now_SAWUN BAYA_ *GARGADI* _Ban yadda ayi amfani da wani bangare nalabarin batare da izinina ba, ko a sayar da labarin ba._ *SADAUKARWA* _Wannan littafin gabadayan shi sadaukarwa ne ga iyayena Allah ya jaddarahamarsa agare su👏🏻
_✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_
*✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ ______________________________________*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*_____________________________________--------PAGE-------https://www.facebook.com/110384724043172/--------GROUP--------https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/*Page 15 to 17*
Typing........🖊️ Idon Munirah nakan Sadiq takasa daukewa shikuwa duk da cewa ba gabansa yake kallo ba bata iya cewa motar tasu yake kallo" Tafiya sosai sukayi har yanzun hawaye bebar idonta ba, kuka kawai take yi tare da zuba masa Ido" Tafiyan kusan awa daya sukayi sannan ta fara hango gine ginen su daga can nesa, raba hankalinta tayi gida biyu tana kallon Rakumin Sadiq dake karta gudu tare da kallon gine ginen" Sosai hankalinta ya tashi ganin irin Saharan da suka keta, cikin ranta take fadin inda nasan haka garin yake banzuwa da kowa sai Annanin na" Suna isa suka samu cin cirondon mutane tun kafin motarsu ta tsaya Sadiq ya diro akan rakumin sa saidai wannan karon be ko kalli inda take ba, fuskarsa ya goge tare da kafar wandon sa sannan ya nufi inda mutanen suke yayin da yake mika musu hannun, wasu Kuma suna runguman junah" Kokarin sauka take amman takasa taka kafarta Saida taimakon wasu 'yan mata da sukaxo gurin su Uku ta samu ta fito, biyu ke rike da ita yayin da dayar ke rike da takalman Munirah" Wanni banban falo suka shiga inda ta hango Sadiq zaune dafda wani tsoho, nan ta tabbatarwa kanta kakansu ne tsoho duk da cewa hutun shi da take gani gidan su bekai haka tsofa ba Amman ta shaida tsoho ne" Zama tayi tana fadin wash Allah na" Zonan, yaki, karaso Muniratu" Bana iya tafiya tsoho, kafata ta karye ahanya" Subuhanallahi, juyawa yayi ya kalli Sadiq yace" Abubakar garin Yaya?? Kallon kakan nasu yayi sannan ya maida kallon sa ga munirah yana fadin, akasa kawai naganta" Subuhanallahi, lallai ya kamata aduba gurin, da alama yana ciwo sosai tunda har take tunanin karaya ce" Ibrahim daya tsinkayi mgnr ne yace, daga Kan Amale ta fado baba" Juyawa yayi ya sake kallon Sadiq sannan yace waye ganin daurata a Amalen? Ibrahim ne yasake cewa ita ta matsa saita hau" Ganin inda Sadiq ya dauke kansa yasa tsoho ya kalli Ibrahim yace ka leka nan waje ka Kira min Sule wanzami" Juyawa Ibrahim yayi cikin sauri, yayin da Sadiq ya sake gyara zaman shi ya daura kafa daya Kan daya sannan yaciro gilashinsa ya maida" Bajima ba Ibrahim ya dawo da Sule kamar yadda tsoho ya bukata, nan ya fada masa bukatarsa yayin da ya juya ya kalli Munirah yace Mugani" Hannunsa yasa ya rike kafar riko mekau tunda ya rika be sakiba yayin da Munirah ta shiga kwala ihu tare da Kiran mutanen gidan su Annanin da Abbanin Umma da Sagir, tsone ke Mata sannu yayin da Ibrahim ma ke Mata sannu" Saida ya gama daidaita kafar sannan ya saki lokacin Munirah ta hada zufah sosai" Wannan 'yan matan ne dai na dazon suka sake shigowa saidai wannan karon su biyu ne kama Munirah sukayi suka shiga da ita ciki" Nan taga Babban gida saidai yanayin duk yana canza mata, jinta take kamar awata duniya daban komai bayya Mata dadi" Wani daki sukashi yayin da matar dakin ta fara fara'a tana me zubawa Munirah Ido" Alhamdulillah Masha yau gani ga Muniratu" Munirah babu vakin mgn gurin kwanciya kawai take nima, kasa taso kwanciya Saida tsohuwar tai saurin tarewa cikin fadin" Yau naga raguwa menene haka? Mammmah nagaji kwanciya kawai nake so" Toh kidaure kiyi wanka mana" Badan ranta yasoba aka hada Mata ruwan wanka Sannan aka Mata jagora zuwa bayin" Wankan tayi yayin da tana dawowa dakin ta samu akwatin ta Kan gado, goggoge Jikinta tayi sannan tafito da mai ta shafa doguwar riga tasa kawai sannan tagabar sa Sallah ta kwanta" ******** Misalin Karfe biyu narana ta tashi zaune, gaba daya gabobin jikinta ciwo suke Mata, yayin da kewan gida ya fara damunta lallai gidan mu aljannar duniyace tafada cikin zuciyarta, tunani tashigayi tare dayin zurfi cikinsa, nayi nisa da gida sosai, babu wadda nasani wadda Sai Sadiq anan dagani sai shi, hawaye ta share sannan ta mike ta nufi tsakar gida" Mammah kawai tagani tare da yan matan nan guda biyu sai aikace aikace sukeyi acikin gidan sanna ta musu yayin da suke binta da kallo" Buta ta dauka tai al'awala sannan ta sake komawa dakin, Sallah kawai tayi ta sake komawa gadon ta kwanta tana mecifaba da zubar da kwallah" Tsowar ce ta shigo dauke da kwano abinci ta tashita tana fadin tashi kici abinci" Hawaye ta share tare da fadin" Nakoshi" A'a, menene haka Munirah, toh fada abun da kike so akawo miki" Kanta ta girgiza alamar babu komai" Wani iri tsohuwar tayi zuwa can takalawa wata Kira tare da fadin kawo min kwanon" Cikin sauri ta fita tadawo da kwano cike da naman zabi gaban Munirah tajashi ta ce to ci wannan idan Kuma Madara kikeso kema aje a anso miki? Kaita sake girgizawa tare da fadin nakoshi" Kallo tsohuwa ta sake tsareta dakyau sannan tace, ke nan ba gurin bakunta bane, nan da kika gani anan dakin ubanki ya girma, kinzo musan juna Kuma kamar kin shigo cikin bare? Dauke Kai Munirah tayi cikin turo baki, yayin da tsohuwar ta fice tabarta awajen" ****** Sadiq ne kwace awani wakeken gado, yayin daya yasar da wayarsa acan karshen gado" Dagashi sai gajeren wando yayin kafarsa take Kan daya, bacci yake sosai wadda daganin yanayin kwanciyarsa kasan yanajin dadin baccin sa" Wani irin duka yaji ankai masa agefen marar sa, runtse Ido yayi daya dafe gurin, wani dukan ya sakeji adayan gefen dan haka yaja tsaki batare daya bude idoba yace" Muhammad banson iskanci" Toh katashi tsoho na mgn" Tashi yayi zaune tare da tura hannunsa cikin gashin kansa yace" Ina tsohon?? Aikoni yayi, Wai Munirah takicin komai, yace kaxo kusa da ita komai aka Bata bataci, tunda tashigo gari batasa komai abakinta ba kuka kawai take" Kallo yabi mutumin dashi sannan ya sake shafa gashin kansa tare da fadin" Toh takicin abinci zan dannetane inbata? A'a Wai kaje kusa da ita dai inji tsohu fah bani ba" Kawar dakai yayi koma waye ya Aiko ka mezan Mata?? Tabe baki Muhammad yayi tare da mikewa shikuwa Sadiq komawa yayi ya kwanta rigingine tare da fadin" Kasan menene?? Batare da Muhammad ya juyoba yace saika fada" Awanni daki aka sauketa? Wacece? Tamudiriccin Munirah" Tana dakin Mammah" Jimmmm, Sadiq yayi, sannan yace, kace masu su ware mata daki, subarta ita daya, komai nadakin Kuma ya kasance fari ne tass👌 Cikin mamakin Muhammed yace bangane ba?? Nima bangane ba, amman haka naga kamar an mata agida, Aliya da Lubbunah suna kwanciya guri daya, Amman ita daya dakinta daban, komai farine adakin ta, farin kaya, farin zanin gado, ta kwanta tsakiyar gado, haka naga suna mata, kuje ku mata hakan wata kila taci abincin tunda kun matso saitaci" Ban gane mun matsu saitaci ba? Kun matso mana, ida rashin cin abincinta be dameku ba bazakazo nan gurin sabo da itaba kawai, wacece ita?, Ko taci abinci ko kartaci ni ba matsalata bace" Murmushi kawai Muhammad yayi ya fice dakin, shikuwa Sadiq wanka yayi sannan ya wuce masallaci sallar la'asar" *****Misalin hudu na yamman Munirah taji Kara wayarta wadda sai ayanzun ta tuna da ita, cikin sauri ta jefa hannunta cikin Jakarta ta fiddota, Kallon dakinta tayi tana fadin" Allah yasama waya na aiki awanan garin, Sagir ne cikin sauri ta dauka tana ajiyan zuciya tare da fadin Amukarnin" Na'am, Munee, Yaya akayi Kun isa shine ko ki kirani" Amukarnin mancewa nayi da waya, sannan bana tunanin waya zatayi aiki anan gurin😭 Murmushi yayi yana fadin, kardai kuka kike gaya min menene? Hannu tasa ta share hawayenta sannan tace Amukarnin garin ba Dadi Sam, jina nake kamar Ina bangon duniya, jikina ciwo yake min sanan Kuma rakumin tsoho ya kadani Saida aka min gyara muna sauka" Toh ke banda abinki daga zuwa saiki kama hawan rakumi, basai kibari ki huta ba" Toh ai su sukazo daukan mu tare da rakuma Kuma ai tun agida nace maka zan hau rakumi" Ikon Allah, yanzun kina nufin cikin garin Zaki shiga arakumi?? Labarin yadda akayi ta gaya masa tsaf jin ya kwashe da dariya yasa ta tsaya cak tana sauraron sa" Me isarsa yayi sannan yace" Muneee? Shiru tayi cikin Jin haushin shi" Kinajina Munirah mgn nake fah? Ai dariya kake min" Nabari, kinajina? Ummm" Toh Ina dau'uwana fah? Dan uwanka bansan inda yake ba, ai yasan bazan iya hawa Amalen ba yace yabarmin Ashe tsabar munafunci ne" Dariya Sagir ya sake yi sannan yace kinaji Munee, ba haka bane, taurin kanki yasa yabar miki, kinga nafarko beson aga yana jayayya dake vayan kina matsayin kanwarsa, abu na biyu kuma yana son ya gaya miki shi ba sa'anki bane, Kuma na tabbatar yanzun kin gane ba'anki bane" Ni daman can nasan ba sa'ana bane, daman waye zaiso yai sa'a dashi" Dariya Sagir ya sakeyi sannan yace to kinsan meye ne yanzun?, Sharawa zan baki, kitashi ki mike kici abinci, Ina me baki shawara idan har Sadiq yaga kin firgice haka hmmmm bazan gaya miki abun da zai faru ba, tayaya mutum zaije asalin sa ya firgice haka? Toh ni Amukarnin bansan kowa bafa anan saishi Kuma ya gudu yabarni tunda mukazo banganshi" Idan kin ganshi me zai miki?, Kinga shidai bazai rarrasheki ba, Kuma bazaije ko Ina dake ba, sannan bazai Bari kije koda kusa dashi ba bare Kuma ya kalleki" Kuma fah hakane wannnan sai Aliya" Ashe dai kin gane, yanxun Zaki saki jikin ki ga kowa ko kuwa? Zan sake, shiyasa naso ace dakai nsyi tafiya gashi ma duk gidan kaine kafara kirana, yauwa Amukarnin rannan Umma tace Wai nida Kai soyayya muke? Me kikace Mata to? Cewa nayi barin tambayo ka" Lumshe idonsa yayi da kinsani kince mata Eh, ko baki sona? Runtse Ido tayi kamar tana gaban sa, rasa abun cewa yasa tai sauri kashe wayar yayin databi wayar da kallo tana murmushi, ayanzun ta manta komai har tama manta inda take, ahankali nutsuwa ya dinga shiganta har ta fara dawowa cikin hankalinta saidai hankalin nata har yanzun yana gurin Sagir domin fuskarsa kawai take gani koda Bata gabasan tana iyasta yadda fuskansa yake ayanzun tasan yana nan cikin farin ciki, aunau sa tayi sanda ya sauke waya banyan sun gama wayar, sosai Sagir din ke burgeta fiye da tunani, Karan wayar data sakeji yasata kallon wayar Sagir din ne dai murmushi tayi sannan ta dauka" Munee munyi waya da Sadiq ya gayamin akwai bikin da za'ayi anjima, zan rokeki wani abu dan Allah ki taimake ni" Inajin ka" Munirah kada kiyi rawa dan Allah" Ai bazan ma iya rawaba Amukarnin kafata ciwo take har yanzun sannan jikina ciwo yake min, ni inaga bazan fita ba ma" Idan baki fitaba bazasuji Dadi ba kije Amman kada kiyi rawa, sannan Kuma banda hira da maza idan kin dawo zan gaya miki wata mgn" A'a nidai ka gaya yanzun kawai" Nafison sanda zan fada gani gaki, kina kallon idona Ina kallon naki" Cikin kukan shagwaba tace Amukarnin ni ko yanzun ji nake kamar Ina kallon ka, kasan tunda mukayi waya dazon?, har ka sake bugo wayar ban daina ganin fuskarka ba" Dan Allah fah Munirah? Wlh Amukarnin har wani murmushi nake gani Kan fuskar taka" Kara fadada murmushinsa yayi sannan yace kamar kin shiga zuciyata fah" Inajinka toh Gaya min" Kinaji Munirah, mgn ce me girma ba irin mgnr da mukasabayi bace, idan kin dawo zan gaya miki" Kukan shagwaba tasa mishi yayin daya shiga murmushi tare da fadin" Ya isah ya isah, kinaji ko, daman cewa zanyi gidan yamin fadi da bakyanan sann....... Kukan takarasa sakawa wlh bawannan mgnr bace" Dariya yayi sosai sannan yace to shikenan yi shiru naji zan fada miki, kin shirya? Eh Ki Kara shiryawa dai" Amukarnin ni ashirye nake" Toh rufe idon ki" Kaima ka rufe naka" Narufe to, kinajina nafara? Eh Zuciyata takamu da ciwon son ki, daren jiya banyi bacciba bayan tafiyan ku, gani cewa ban bayyanar miki da soyayyata ba, inajin tsoron kar wani yayi maki tayin tasa ki amsa, ajiyan zuciya yayi sannan yace Munirah Zaki yadda ki aureni?? Lumshe idonta tayi yayin da take karajin amon sautin sa yana Mata wannan dai tambayar kashewa tayi da sauri sannan ta bude idon ta kalli wayar cikin sauri ta daga filon ta tura kanta ciki Sagir ma kallon wayar yayi tare da murmushi kadan" ********Misalin Karfe 8:00pm kofar gidan Baba tsoho cike yake makil da jama'a" Banda kide kide da bushe bushen babu abun dake tashi" Wuri yayi guri, tuni baki ya kankama Sadiq na hanga kusa da tsoho tare da wasu Samari guda biyu sai Sai Mammah tare da wasu yan Mata biyu itama agefenta dagacan gefe kuwa Kannen Alhaji jafar ne Mata su Uku zaune da yaran su, iyalan Bava tsoho kenan sai Kuma baki dakecan gefe yayin da iyalan Baba tsohu suka fara taka rawa" Sadiq kallon rawan kawai yake tare dabin 'yan matan da kallo daya bayan daya yana kallon yadda suke tasu girgizan saidai nasu ba irin nata bane yafada cikin ransa, Amman duk da haka ya kasa dauke idonsa akan su" Sosai yan uwa da jam'ar arziki ke son ganin Munirah Amman Sam taki fitowa acewarta jikinta ciwo yake mata dan haka aka barta sadai duk wadda ya tambayeta saidai agaya masa inda aka sauketa" Ita kuwa Munirah kusan awa biyu kenan tanajin kida natashi, sosai Busan ke tsumata yawanci saidai ta kunna taji yau ga busa muraratan natashi wannan yasata zuwa yin wanka batare data shirya ba" Cikin sauri tayi wanka shiryawan ma cikin sauri sauri tayishi, sannan ta dauko kayan da aunty Khadija ta saya mata, wandon tasa sannan ta dauki doguwar rigar ta tabude daga kasa ta Sanya, ita dakanta ajikin ta take tabbatar da tayi kyau bana wasaba" Dan kunne da sarka tasa tare da awarwaraye sanna ta Kara gyara gashin kanta afili tace yau ba zan sa lafaya ba, dogon takalmin da aka bata tare da kayan ta sanya sannan ta fesa turare ako Ina najikinta" Gaban madubi ta tsaya tana me fadin masha Allah nayi kau saidai makiyi" Inda takejin kidan natashi take nufa yayin da take tafiya kidan na dada tsomota tare dajin dadin yanayin, kamshin garin da komaima ayanzun burgeta yake yi" Tana fitowa ta hangi matan dake rawa afili cikin sauri tsowar ta mike tana fadin, ko ke fa Muniratu ki shiga cikin yan uwan ki kowa yasanki yafi ai ko" Toh Mammah gashi ai na fito Amman ni kibar cemin Muniratu kar wani yaji yakama" Nikuma shina iya fada yaya zakiyi dani? Nidai gaskiya banso" Hannunta tsowar taja suka zauna kusa da yanmatan yayin da kallo yadawo gun Munirah sosai kyaunta ke daukan hankalin jama'ar gurin duk da cewa akwai kyawawa agurin Amman daganin Munirah da shigarta kasan bakuwa ce" kamar yadda shigan Sadiq ma ya nuna hakan' *********Tun fitowan Munirah Sadiq yamaida gilashin sa tare da daura kafarsa daya kan daya" Mawakin da take yawan kunna wakokinsa ne yafara tasa, yayin da kida ketashi kota Ina tare da bushe bushe, sosai Munirah ta tsomu fiye da tunanin me karatu yayin da har tafara rawa daga zaune ganin be gamsar da itaba ta mike tundaga inda take zaune ta fara rawa dan haka da rawa ta isa filin yayin da gurin ya dauki tafi da ihu hakan ya karawa rawar tata armashi" Bayan ta tsaya tsakiyar filin kuwa wani irin girgiza tafara yayin da tabbatarwa jama'ar Ingall iyalan tsohu basu yada al'ada ba" Mikewa Sadiq yayi daga inda yake zaune cikin kasaita yake takawa harya isa gaban Munirah ya tsaya" Ita ko Munirah wannan lokacin ta tsomu iya tsumuwa rawa take tare da gigiza kirjinta" Idonsa cikin gilashi yake kallonta cikin sauri ya zura hannunsa a alihun wadonsa nabaya, bandir din kudin can ya fito dashi yayin da ya fara yi Mata liki akirjinta, be tsayaba Saida ya karar dashi sannan ya maida hannunsa yasake dauko wani adayan aljihun dai dake bayan sa, likamata yake yayin da Munirah tai nisa busa yai mata dadi rawa kawai take" Ihu gurin ya dauka tare da tafi, abune wadda ba'a Saba gani ba Sadiq betaba shiga fili yayiwa wani likiba, itako Munirah tana kallon yadda kudi ke sauka akirjinta saidai batasan waye ke manna su ba" Ganin abun yaki karewa ta daga idonta sama dan ganin waye da wannan aikin........ Mmn Yazeed