🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾
🌾 *OUR PROVINCE* 🌾*Na Aysha Sada Machika*
*Page 17*
Acikin wani k'ayataccen d'aki su Saaya da masoyiyar tasa Fauwa suka shiga, wanda yasha ado da kayan masarufi iya kallon mai rai, Fauwa zata zauna Saaya yayi sauri ya rik'ota, ya rik'e kwankwasonta da hannu d'aya sannan yasa d'ayan hannun ya tallabo hab'ar bakinta, ta bud'e kyawawan idanuwanta sosai ta kallesa, wasu hawayen dad'i suka fara gangaro mata, yayi sauri ya goge mata gami da dora d'anyatsansa guda d'aya akan leb'enta yana mai cewa "shshhhhh banason ganin hawayenki kema kinsani, karki manta na miki rantsuwa da iyayena Annu da manaay abaya, ayanzu ina miki rantsuwa da tsohuwar Aljana tawassuga, duk duniya babu wanda ya isa ya rabani dake, sannan na miki alkawari babu wata mace anan garin Dulme idan kika cire Annu da zata samu farinciki da gatan da zan baki, ina sonki Fauwa"
Ya janyota jikinsa ya rungume, wani murmushi ta saki mai had'e da kuka.************
"Zuru ashe tsafin naka na k'arya ne?" Zuru yayi caraf yace "a'a sarkina ni kad'ai ba'a kira tsafi na na karya ba kam domin bacin shi da bakayi dad'ewar haka akan kujerar mulki ba" wani irin mugun kallo mai cike da mamaki Sarki Diyara yama Zuru bayan da ya kirasa da *sarki na ni kad'ai*.
"Sarkinka kai kad'ai? Kanaso ka tabbatar min da cewa kenan babu abunda zaka iyayi akai? Kanaso kacemin yanzu ni ba sarkin kowa bane?""Tabbas kai ba sarkin kowa bane kuma kai ba kowa bane, nima dalilin da yasa kake sarkina don nasan kozan gudu bazan tsira ba, tafiyarmu d'aya kuma a halin yanzu makomar mu d'aya, kaga babu amfanin yi maka butulci, gara na mutu a k'ark'ashin jagorancin tsohon sarki kona samu sassauci yayin had'uwata da abun bauta zuba"
"Ban fahimce ka ba?" Cewar Sarki Diyara.
"Ai dukkan laifuka da mutanen daka mulka suka aikata yayin mulkinka yana rataye a wuyanka ne, haka hukuncin abun bautarmu yake, ni yanzu tas nake a wurin abun bauta yadda kasan nayi wanka da sabon ruwan rafin dul, kuma ga dukkan alamu komawarmu ga abun abauta tana kusa ne, domin yaron nan naka baida ragowa" yana kaiwa nan ya sunkuya alamar girmamawa gami da cewa "zuba ya taimaimake ka yakai sarkina ni kad'ai"
A kulle suke kowa da kejinsa amma kejin suna kusa da juna, Sarki Diyara ya karema kurkukun nan kallo tsaf sannan yace "zama nan ai daidai yake da hukuncin had'uwa da abun bauta, ni banma tab'a sanin haka wurin nan yake ba"
Murmushi kawai zuru yayi, wanda yake nuni da "ai yau ka gani"
Tafiyar gardawa da dogarawa suka ji, wani irin dad'i Sarki Diyara yaji, ya kasa b'oye farincikinsa har saida yace da Zuru "kaji ba, ai a irin mulkin da nayima mutanen nan nasan bazasu barni anan ba, ai haryanzu suna shakka ta"
"Wane irin mulki ka masu? Zuba ya taimake ka" Zuru ya tambaya.
Kafin Sarki Diyara yace komai sai gasu sun karaso, Sarki Diyara sai murmushi yake masu, bulalu suka zaro suka bud'e kurkukun suka shiga suka maida suka rufe sannan suka hau dukansu, saida suka masu lilis sannan suka fito suka kullesu suka wuce, cikin k'arfin hali da muryar tsananin azaba Zuru yace "lallai sarkina ka mulkesu dakyau"
Shiko Sarki Diyara maganar ma baze iya ba.*****************
Koda dogarawa suka iso dasu Manaay basu diresu ko ina ba sai cikin fadar sarki, daga gani basai anfad'a masu ba sunsan cewa lallai akwai abunda ya faru a fadar sarkinnan saidai basusan ko menene ba.
Mamaki ya kama su ganin yadda aketa haba haba dasu, ga kayan marmari anzo an dire masu a gabansu, sai girma ake basu.Annu da Manaay saidai su juya su kalli juna cike da mamaki, basu iya tab'a komai ba a wurin domin su kam bayan mamaki ma a tsorace suke.
Wasu k'ayatattun kujeru guda biyu akazo aka ajiye, sannan aka d'aukesu cas aka d'ora kan kujerun, sukam iya tsorata sun gama tsorata.
Ga mamakinsu sai suka ga Ale ya fito cikin girmamawa yace "ga sarkin nan fitowa" rufe bakinsa keda wuya saiga Saaya ya fito, ba shiri Annu da manaay suka mik'e tsaye, Saaya ya karaso wurinsu, suka rika kallonsa suna tattaba sa kamar sunga wani abu da basu taba gani ba, Annu ta fashe da kuka tace "nagode abun bauta daka kubutarmin da Saaya, na zata an kashe ka"
"Ta yaya za'a kashe sabon sarkin Dulme? Saaya jikan Saaya, d'an sarki jikan sarki, d'a wurin Annu da Manaay, na aljana tawassuga angon Fauwa" inji Saaya.
Manaay yad'an janye jikinsa yace "ban fahimce ka ba.
Ale yayi sauri yace " ai labarin da d'an yawa manaay, amma a tak'aice zamu iya kiranka da mahaifin sabon sarki domin ko Saaya dake nan a gabanku shine sabon sarkin garin nan, sarkin matsafa Zuruqum da sarki Diyara ko suna kulle a kurkuku, zaayi bikin fed'e sabon sarki da munafikin matsafinsa gami da auren fauwa da sarkin sarakuna wato Saaya.
Annu taja da baya ita da manaay cikin tashin hankali atare suka ce " ta yaya duk haka ta faru, badai kuna shirin kashe Zuru bane?"
"Kwarai kuwa, meye laifin hakan?" Ale ya tambaya.
"Lallai zaku gamu da fushin abun bauta domin ko baa tab'a y'an aikensa, karku manta Zuru shi kad'ai ne yake iso mana da sak'on abun bauta, shine zab'abbe tun shekaru aru-aru, dalilinsa muke sanin komai dakuma lokacin komai, so kuke mu zauna babu bauta?"
Saaya yace "au daman ita bautar harsai wani yace maku ga yadda zakuyi? Nasha fad'a maku babu wani abun bauta daya wuce mu kanmu, sai ga Usman ya shigo, Saaya ya cigaba da cewa "ni inaji araina hukuncin duk wani azzalumi shine a kashe shi" ya karasa yana kallon Usman yace "koba haka ba bawa Usman?"
"Hakane amma a hukuncin kwakwalwar d'an Adam, ni a addini na kowane laifi da kalar hukuncin sa kuma a rubuce yake a littafina mai tsarki"
"Meye hukuncin Zuru a addininka?" Inji Ale
"Da farko kafin duk hukunci kasancewar Zuru kafiri daze karb'i addini na da duk laifukansa ubangijina ze yafe masa, da babu wani hukunci daze hau kansa....... Kafin ya k'arasa Ale yaja wani mugun tsaki yace wannan wane irin raggon addini ne, lallai abun bautarka be iya hukunci ba.
"Abun bautana shine mafi iya hukunci, addini na addini ne mai saukin gaske, ubangijina mai yafiya ne bama kamar laifin da bawa ya aikata akan rashin sani" Cewar bawa Usman.
Saaya yace "to da sauk'i tunda ba addininka muke ba, domin babu abunda ya isa ya hanani hukunta Zuru, dole yabar duniya komin sonshi da ita"
"Na rok'e ka indai har mun isa dakai karka kashe mana jagora, karka mayar damu arna marasa addini, wannan shine addinin da muka sani tun kaka da kakanni" inji Annu.
Shiko bawa Usman aduk sanda suka kira wasu arna saboda basa addinsu na bautar ruwa sai su rika bashi dariya matuk'a domin a wurinsa duk d'aya yake kallonsu.
Saaya ya kara matsawa daf dasu ya kalli Annu yace "haba Annu kicemin da wasa kike?"
"Da gaske nake, indai na isa dakai to ka janye qudirinka"...............
YOU ARE READING
NAHIYAR MU...{Our Province}
Historical FictionRayuwar maguzanci awancan shuɗaɗɗen yanayin...