6

128 10 1
                                    

🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾

     🌾 *(OUR PROVINCE)* 🌾

*Na Aysha Sada Machika*

*6*

Manaay ya zaro ido waje cike da firgici sannan yace "garin yaya kayi wannan wautar Saaya? Kasan ko cewa Maigirma Sarki bazai tab'a barinka ka zauna lafiya ba? Ze cigaba da farautarka ne har k'arshen rayuwarka kai hada mu kammu mahaifanka"

Murmushi kawai Saaya yayi, ita ko Fauwa sai nok'e-nok'e take ta rasa yadda zatayi gata zindir.

"Manaay abunda za'ayi ciro rigarka kaga ni" inji Saaya.

Manaay ya yamutse fuska wanda hakan ke nuni da "bangane na ciro riga ta ba?"

Saaya yad'an karya kai gami da kashe ido d'aya, take Manaay ya gane cewa so yake aba Fauwa wani abu tad'an Saaya tsiraicin ta, babu gardama Manaay ya cire riga ya bata, ta saka amma fa ko d'uwawunta bata ida rufewa ba motsi kad'an zata yi ta d'age, Saaya ya rufe gabansa da ganye sannan ya sab'i Fauwa yace ma Manaay su tafi.

Abun gwanin bandariya, Manaay babu riga, Saaya babu kaya, Fauwa ko wannan zamu iya cewa da kad'an ta d'ara babu, kuma tafiyarsu suke hankali kwance.

Suna ta tafiya, Saaya da manaay nata fira sai ga wata mata tasha gabansu ga itace ta d'auko a kafad'a, da sauri suka dakata suka tsaya.

"Manaay ashe rai kanga rai?" Cewar wannan mata tana mai murmushi gami da bada cikakkiyar fuskar sani.

Fauwa ta kalli Saaya, Saaya ya kalli Manaay.

Manaay ya yamutse fuska yace "Aikuwa amma saidai ban sheda ki ba yake wannan mata"

Ta sauke itacen ta karkad'e hannaye sannan ta zaro wani zare me d'auke da laya ajiki ta nuna masa tace "nasan ba zaka shedani ba amma bana zaton zaka manta wannan" ta k'arasa maganar tana mai bud'e tafin hannunta inda zaren yake.

"Tabbas bazan tab'a mantawa da wannan laya ba to amma......."

Tayi sauri ta dakatar dashi "kar kaji komai Manaay ba wani abu bane, lokaci fa yayi, lallai lokaci yayi"

Tana gama fad'in haka ta jawo hannun Fauwa ta bata wannan zaren me laya tace "naki ne yarinya, kisa a wuyanki ko a hannunki kokuma duk inda yayi miki nakine dai" ta kalli Saaya tayi murmushi sannan ta d'auka itacen ta ta wuce.

Tana wucewa Saaya yaji an karce sa a hannu, da sauri ya juya amma sai be cimma ganin wannan matar ba harta k'ule ko ince ta b'ace.

Fauwa ta k'ura ma Saaya ido zuciyarta cike da tambayoyi masu yawa.

Shiko Saaya gaza yin shiru yayi saida yace "Manaay wacece waccan matar?" Duk da yasanta amma saida ya tambaya, don ta saba bayyana masa kanta saidai bada irin wannan suffar ba, yanaso yaji gaminta da Manaay wato mahaifin sa.

Manaay yace "labarin nada tsawo Saaya, nasanta saidai inada tabbacin ba mutun bace ita aljana ce"

"Inaso naji labarin komin tsawonsa Manaay, ka fara bani yanzu ka k'arasa wani lokacin, kokuma ka bani labarin atakaice, inaso naji" cewar Saaya.

Manaay ya k'ura masa ido, Saaya yace "eh ina sauraron ka"

"A shekarun baya da suka wuce, lokacin muna cikin shekara ta hud'u da aure nida mahaifiyarka Annu, a wannan lokacin kaf garin Dulme da kewaye ba'ayi masoya irinmu ba, komi tare muke, haka duk inda zamuje tare muke zuwa, wata rana sai muka d'auko tulu domin zuwa d'ebo ruwa rafin gabas, muna tafiya muna firarmu gwanin ban sha'awa har muka isa rafi, muna isa sai naji fitsari ya kama ni, nace da Annu ta taro ruwan bari na d'an zaga fitsari ya matse ni, tace dani to......"

NAHIYAR MU...{Our Province}Where stories live. Discover now