🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾
🌾 *(OUR PROVINCE)* 🌾
*Na Aysha Sada Machika*
*9*
Ale ne da Tura, bawa Usman yaji dad'in ganin su duk da cewa yasan basa sonsa tun ganin farko.
Saaya ya saki murmushi kamar kullun sannan yace "mazajen duniya tanan kuka b'ullo? Sai kace mutanen b'oye"
Suma murmushin suka mayar masa.
Suka k'araso wurinsu suna k'ok'arin bud'esa ya dakatar dasu yace su duba masa mahaifiyarsa ko rai yayi halinsa.
Abun bantausayi shiko bawa Usman ko kallon inda yake basuyi ba,
Suka je suka yita k'ok'arin bud'e Annu, dakyar suka bud'e, sudai a mace suka ganta don kuwa bata lumfashi ko kad'an, Ale ya sab'eta suka fiddo ta sarari, Tura ya matsa kusa da Saaya nan ma yahau k'ok'arin bud'e sa, Saaya babu k'arfi a jikinsa ko kad'an, yana nan dai sai abunda hali yayi, shiko bawa Usman na daga gefe cikin kejin sa yana kallonsu cike da damuwa.
Motsi da surutai suka fara ji kamar an tunkaro wannan kurkuku, habaaa nanfa Ale ya k'araso suka k'ara k'aimi bisa k'ok'arin da suke hardai suka bud'e Saaya, Tura ya kamo Saaya, Ale yayi sauri ya kinkimi Annu zasu bi ta wannan rami da suka shigo ta k'asa, Saaya yace aishi inaaaa babu inda zeje batare da bawansa ba.
"Haba Saaya kanajin fa tafiyar mutane kuma ga dukkan alamu nan suka nufo, bawan me? Ka barsa nan ajalinsa ne yazo" inji Ale.
Usman dake cikin keji yace "ku tafi kawai kar ayi biyu babu, kar saboda ni wani abu ya same ku"
Ale ya sake cewa "ai ko baka ce ba tafiya zamuyi, munafikin bawa mai bak'in addini Kai daga ganinka azzalumi ne"
"Bazanje ko ina ba tare da Usman ba" Saaya ya k'arasa maganar yana mai kallon cikin idon Ale.
Ran Ale yayi mummunan b'aci, ganin irin hatsari da sadaukar da rayuwar da sukayi domin ceto sa amma saboda wani sakaran bawa a cewarsa, Wanda dika yaushe ya sansa ze juya masu baya, alamu sunaso su nuna cewa Saaya yafi son Usman kansu, cewar zuciyar Ale.
Ale na janyo Saaya, shiko yana fizgewa, Tura yace da Ale "kazo mu tafi Ale, mu samu mu fitar da gawar Annu domin inada tabbacin ta mutu babu sauran rai a jikinta.
A fusace Saaya ya kallesu batare da yace komai ba, suka sab'i Annu, suka turata ta wannan rami Tura ya fara shiga shine me jan k'afarta, shi kuma Ale yana daga saitin kanta, hararar Saaya kawai yake har suka ida shigewa ramin.
"Daka sani ka bisu, bani kad'ai bane Allah yana tare dani, kuma duk abunda ya faru dani ikonsa ne haka ya tsara" cewar Usman.
Saaya yayi masa wani irin kallo na rainin wayo sannan yace "idan dai har dagaske Allahn ka yana tare dakai dabe barka cikin wuya ba, ina ganin wautar masu bautar zuba amma nafi ganin wautar ka domin gara su suna ganin abunda suke bauta mawa, kaiko baka ganin komai, kanata shirme, kaga Usman kake kome? Idan zaka natsu ka natsu, kayi nazari da tinani babu wani abun bauta daya wuce kai kanka, mutun shine ubangijin kansa da kansa, muna cikin nan wurin Allahn ka be cecemu ba, Zuba be cece mu ba, Amma mutane sune sukazo ceton mu, idan zaka rik'a tashi kana taimakon kanka ka rik'a tashi don babu wani Allah, duk abunda ba'a gani to Aljani ne"
"A'uzubillahi minash shaid'anirrajim" cewar Usman, sannan ya k'ara da cewa "Ni addini na matakin farkon shigarsa shine IMANI, idan har kayi imani dashi to yadda da kuma saninsa zezo maka a sauk'ak'e, amma matuk'ar bakayi imani da shiba, babu wani haskensa da zaka gani, Allah gaskiya ne, kuma shi Allah........
Sai ji sukayi an shigo, mamaki ya kama dogarawa ganin Saaya a tsaye gaban kejin Usman suna magana, sukayi cokar-cokar suna tinanin yadda akai ya fito daga nasa kejin, ga kejin Annu shima a bud'e wayam babu kowa.
"Basai kunsha wahalar tinani ba, nina b'alle na fitar da mahaifiyata ta wancan ramin, yanzun ma ina niyar fitar da bawana ne kuka shigo" inji Saaya.
Usman acikin ransa yace "Saaya yayi nisa amma inai masa kwad'ayin musulunci domin irinsu addinin musulunci ke buk'ata, jarumai masu dakakkar zuciya, marasa tsoro ko fargaba"
Gani sukayi dogarawa na darewa, suka zuba ido domin ganin abunda ze faru, sarki Diyara ne da kansa ya shigo, koda ya dudduba yaga aika-aikan da akayi a kurkukun bece komai ba saidai kawai ya saki munafikin murmushi yace "a tsaftace masu hanya gami da tabbatar da sun fita lafiya, idan akwai abunda suke buk'ata ku basu"
Saaya da Usman suka kalli juna, su kansu dogarawan sunyi mamakin hakan.
"Alhmdlh" inji Usman yana mai d'aga hannu sama.
Saaya dai ya kallesa ya buntsure baki,
Dogarawa suka tasasu gaba, gabaki d'aya fada tayi tsit sai kallo ake, saida dogarawa suka fitar dasu daga gidan sarki gabad'aya sannan suka koma.
Saaya yayi tsaye yanata kallon Usman, Usman yace "ka gani ko? Wannan ikon Allah ne, ni nasan Allah yana tare dani"
"Uhm" Saaya ya fad'a atak'aice, sannan suka cigaba da tafiya.
Fauwa na ganin fitowar farincikin nata, taci kukanta a b'oye sannan ta goge hawayenta ta fito daga b'oyewar da tayi ta tunkaro gidan sarki, tana kawowa k'ofar gidan sarkin aka dakatar da ita gami da tambayar inda zataje.
"Nazo ganin sarki ne, sunana Fauwa" ta fad'a cikin d'acin rai.
Basu barta ta shiga ba har saida suka fad'ama sarki ya basu izini.
Koda Fauwa ta isa gaban sarki wani irin bak'inciki ya mamaye zuciyarta, wanda har saida ta kasa daurewa hawaye suka sauko daga idanuwanta.
Sarki ko abun nema ya samu wai akace matar d'an sanda ta haifi b'arawo, farinciki fal ransa, a b'oye da bayyane dominko bakinsa ma yak'i rufuwa.
Take aka yima Fauwa wurin Zama bisa kujerar mulki wadda tasha ado, sannan sarki ya bada damar shiga birnin Dulme da kewaye domin sanarwar shagalin bikinsa da za'ayi gobe-goben nan.
Da Fauwa tayi motsi sai sarki yace menene?
************
Dak'in da aka sauke Fauwa kansa wata duniyar ce guda, ga bayi da aka tara mata ko wanka sai taso tayi, Fauwa ta b'uk'aci a barta ita d'aya a d'akin, babu musu kowa ya fita, ta dudduba ko ina, daga gefe guda taga kayan marmari acikin wani kwando ga wuk'a aciki, da sauri ta d'auki wuk'ar nan ta gama jujjuyata sannan ta rumtse idanuwa ta dage ta d'aga ta...........
*Plz ku yita hak'uri Dani masoyana, bazan ja littafin da tsawo ba sakamakon hidimomi da sukayiman yawa, Allah yabar zumunci.*
YOU ARE READING
NAHIYAR MU...{Our Province}
Historical FictionRayuwar maguzanci awancan shuɗaɗɗen yanayin...