🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾
🌾 *(OUR PROVINCE)*🌾
*Na Aysha Sada Machika*
*11*
Tura a firgice ya tashi tsaye, Saaya yace "nizan juya Usman ka kulamin da Annu da Manaay"
"Ina tare dakai bazan zauna bayan Fauwa na hannun azzalumin can ba, zan bika koda hakan na nufin ajali na"
Gyad'a kai kawai Saaya yayi.
"A'a ba yanzu ba, kuyi hak'uri ku bari sai gobe, shiga fadar sarki a wannan karon ze maku wuya, kar mu rasa ku ku dika, kudai zauna ku sake nazari da tinani" inji Nayzu.
"Nazari? Nazarin me zamuyi? Kuna jifa aurenta zeyi kuma na tabbata baze jinkirta ba don yasan zanzo mata" Saaya ya k'arasa maganar cikin d'acin rai.
"Yakai masoyina Arkisaaya, kar ka biyewa zuciyarka, fushi ba naka bane domin zuciya ba jiki bace, bazata iya yi maka yak'in daya kamata gangar jiki tayi ba, bazaka iya shanye bugun mayak'a da dogarawan sarki ba, gidan sarki a zagaye yake da tsafi yanzu haka bazamu iya kawo maka d'auki ba" muryar AljanaTawassuga ce suka ji mai cike da ban tsoro.
Gogan naku ko d'ar baiji ba, sai ma tambayar ta da yayi yace "me kike nufi da haka?"
Tsohuwar aljanar tace "ina nufin ka hak'ura da Fauwa, daman ba matarka bace, bakazo duniya don kayi aure ka haihu ba, kazo duniya don kayi mulki ne"
"Baki fad'a da kyau ba aljanar banza" cewar Saaya.
Ya shiga d'aki ya sake d'auko wata takobi zandamemiya, yace da Tura "muje"
"Hahahaha kuje ina? Babu inda zakaje, bazamu rasa ka ba Saaya, sai na tabbata anyi bikin sarki kana zaune gida" inji Tawassuga.
Saaya yayi tsaki ze wuce, sai yaji kamar an tad'iyesa yayi mummunar fad'uwa k'asa, tunda ya zube babu inda nasa ke motsi sai kansa kad'ai.
Kaf mutanen wurin nan sun tsorata matuk'a, Manaay dake bakin murhu ya matso kusa yana jijjiga Saaya.
"Kaja kunnen d'anka Manaay domin yanada taurin kai kuma baze kaisa ko ina ba, ka fad'a masa waye shi, ka kuma sanar masa dalilin dayasa muka zab'esa" cewar Tawassuga
Bayan ta gama fad'ar haka sai wurin yayi tsit, ga dukkan alamu ta tafi.
Manaay ya fashe da kuka yarik'a cewa "abun bauta me ni da matata da Saaya muka yi maka? Me nayi maka? Abun bauta nine Manaay na Annu, na kasance bawan ka na k'warai me kyautatawa wurin bauta maka, ka dubeni Abun bauta, abun bauta ka dubeni" ya cigaba da rusa kuka.
Tura dake tsaye k'ik'am Yama rasa me zeyi, tafiya zeyi ko tsayuwa.
Usman ya tallabo Saaya yana fad'in "sannu"
Saaya yayi murmushin takaici yace "sannu ai ba ciwo nake ba, banajin ciwon komai kawai dai naji jikina ya shanye ne bana iya motsi"
"Ciwon kenan ai" Usman ya fadi haka cikin rashin jin dadi.
Annu dake daga ciki tana jinsu kuka kawai take, Nayzu sai taji dama bata fad'a masu cewa Fauwa ta tafi gidan sarki ba.
******************
Fauwa da idanuwanta ke a rufe sai ji tayi ana shafata, da sauri ta bud'e ido, wa zata gani? Saaya.
Ta k'ara bud'e ido sosai tace "Arkis kaine? Ta yaya ka shigo nan?"
Ya wani wangale baki yace "saboda matuk'ar sonki da sha'awarki da nake, Fauwa ki amince dani" ya sake shafota ta janye jiki.
Fauwa bata yarda dashi ba domin kamanni ne kawai yake da Saaya amma maganganunsa da yanayin yadda yake sam ba haka Saaya yake ba.
Ya k'ara matso ta, aiko Fauwa ta mik'e cikin tsiwo tace "karyane Kai ba Arkis d'ina bane, Saaya baya abunda kake yanzu, Saaya jarumin namiji ne me kamewa ba sakarai ba, Saaya be tab'a furta makamanciyar kalma koda d'aya a cikin wanda kayi yanzu ba, Saaya baya dariya saidai murmushi, kai ba Saaya bane" Fauwa ta rarumo tasa, tayi-tayi ta buga masa amma tak'i.
Yayi tsaki ya fita a d'akin, yana fita ya juya kamanninsa, Zuruqum ya biyosa yana cewa "zuba ya taimake ka ya baka yawan rai, ya kuka k'are ta gane ka kuwa?"
"Bata gane ni ba, tadai gane cewa niba Saaya bane, matsalar bana iya b'oye maita ta" cewar Sarki Diyara.
Zuru yace "lallai ya kamata ayi aiki akan hakan.
***********A gefen Fauwa kuwa, tinani ta hau yi tana cewa a zuciyarta "meyasa na koresa? To ko da gaske Arkis ne? Amma kuma Arkis ai baya irin wannan halailayin dana gani yanzu"
Nan kuma ta dasa wani sabon kukan na kewar matsoyinta, farincikin ta.
*********************
"Ba don karkace nayi maka shishshigi ba, bakuma don na b'ata maka rai ba, da nayi maka tayin addini na musulunci, ka karb'i addini na domin bebar komai ba, ubangiji na yana warkar da har irin wannan ciwon da kake yi yanzu" inji Usman.
Saaya yayi murmushin rainin wayon daya saba yace "addininka k'aryane, abun bautarka ma karyane, wannan addinin kai kad'ai ne mabiyanshi, idan na fahimce ka, so kake ka samu mabiya bayanka wanda zasu rik'a bauta maka a matsayinka na shugabansu mafi kusanci da abun bautar su"
"Ko kad'an ba haka bane, ni ban isa a bautamin ba domin niba Allah bane ni mutun ne da Allah ya halitta ni bawan Allah ne, kuma shi ubangiji na ba'a masa kishiya wurin bauta, wanda duk ya had'asa da wani to lallai mushiriki ne kuma ya kafirta, tabbas ina neman mabiya domin mu tsira tare, addini na addinin rahma ne dakuma sauk'i, sannan kuma ina kira zuwa ga addinina ne badon komai ba saidon cika umarni"
Usman ya cigaba da cewa "an tambayi annabi Muhammad SAW, nasan baka sanshi ba, yana daga cikin annabawan Allah abun bauta ta, shine fiyayyen halitta kuma annabin karshe wanda Allah ya aiko mana da Alqur'ani maigirma (littafi), wanda muke bin aikinsa da koyarwarsa"
"Aka tambayesa, menene abubuwa guda hud'u da suka wajaba akan dukkan musulmi? Sai yace, "Sani ma'ana ilimi, aiki dashi ilimin, kira zuwa ga ilimin sannan hak'uri dashi, shiyasa nake kira zuwa ga addinina domin shine addinin gaskiya"
"Kai bawa Usman, kai bawa na ne ba bawan wani, wata ko wani abu ba, rayuwarka a hannuna take, ni kad'ai keda iko dakai"
"Na yadda ubangidana, amma gaka yanzu a kwance, idan ran kowane mutun a hannun d'anuwansa mutun yake meyasa ban kasheka ba yanzu? Ko ance ka kasheni bazaka iya kashe ni ba yanzu domin kaima ta lafiyarka da rayuwarka kake, ubangidana Saaya shin ka tab'a tinanin ta yaya ake mutuwa? Bayan kuma an mutu ina ake zuwa?"
Saaya yayi shiru nad'an wani lokaci sannan yace "naji, idan har ka rok'i abun bautarka ya warkar dani kafin gobe zan k'arb'i addininka"
"Banyi maka alk'awarin warkewa gobe ba domin k'arfin iko yana hannun Allah, kuma zanyi iya bakin k'okari na domin tabbatar maka da cewa addinina gaskiya ne" inji Usman.........
YOU ARE READING
NAHIYAR MU...{Our Province}
Historical FictionRayuwar maguzanci awancan shuɗaɗɗen yanayin...