2

168 10 0
                                    

🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾

     🌾 *(OUR PROVINCE)* 🌾

*Na Aysha Sada Machika*

*2*

Tafiya Saaya keyi hankalinsa kwance cikin dajin nan, zeje ya had'o ma Annu itace na girki.

Kamar daga sama yaji muryar tsohuwar data saba bayyana ga dubansa lokaci zuwa lokaci tace "Arkisaaya" cikin wata iriyar murya mai firgitarwa.

kasancewar yau bashine karo na farko da hakan ya tab'a faruwa dashi ba, sai be wani firgita ba, saidai juye-juye da ya tsaya yana yi na k'ok'arin gano ta inda muryar ke fitowa.

Jikin wata bishiya dake nesa dashi kad'an ya hango wannan yank'wananniyar tsohuwar, suna had'a ido ta dashare bakinnan nata da babu hak'ori ko guda d'aya aciki, ga wasu irin kwala-kwalan idanuwa da zurkud'ed'en hanci wanda ya kusa tab'o bakinta.
Saaya yaja tunga gami da nuna ta da d'an yatsa yace "wai ke me kike nema daga gareni ne eh? Na rantse miki da girman iyayena idan baki dena bibiyata ba ni zan zama ajalinki"

Tsohuwar nan ta sake mannewa jikin bishiya har lokacin murmushi take masa, sannan ta fara magana kamar haka;
"Ya kai Arkisaaya Sarkin garin Dulme da kewaye! Nakan ji matuk'ar sanyi araina duk lokacin da na ganka a raye cikin k'oshin lfy, akwai b'oyayyen al'amari a tare dakai na fad'a maka, lokaci yayi! lokaci yayi! lokaci yayi, kaje iyayenka su fad'a maka abunda baka sani ba, ya kai farincikin ruhina Arkisaaya"

"Meyasa kike son kirana da Sarkin Dulme? bayan munsan babu wanda ya tab'a sarautar garin face d'a ga sarkin dake kan kujerar mulkin, sannan sanin kowa ne sarki Diyara baya da wani d'a a doron duniya, idan ko har akwaisa to tabbas da Zuru ya bankad'o labarinsa"

Tsohuwar nan ta fashe da wata matsananciyar dariya tace "Arkisaaya d'a ga Annu da Manay mazauna anguwar turha dake cikin garin Dulme kaine sarkin Dulme na 24 kuma magajin sarki Diyara, kaje mahaifanka su baka labari"

Tana kaiwa nan ta b'ace ya nemeta ya rasa kamar dai yadda ta saba, sai wani zafi daya ji a hannunsa, koda be duba ba yasan cewa yankarsa tayi, domin duk sanda ta bayyana garesa takan masa y'ar yanka kad'an me kama da tsunkuli, ko meye hikimar yin hakan?, shikam be damu ba yayi wucewarsa gami da dafe hannun da d'ayan, amma da sak'e-sak'e cikin ransa masu tarin yawa.

Bayan Saaya ya gama yo iccen nan, be zame ko ina ba sai gida.

"Gafara" irin tasu sallamar kenan, ya shiga gida fuskarsa d'aure, cikin damuwa Annu ta taso daga inda take zaune tazo ta samesa.

"Saaya lafiya naga ka shigo min da fuskar da bada ita ka fita ba?"

Kallonta ya tsaya yana yi na wani guntun lokaci sannan ya k'ak'alo murmushi yace "Annu babu komai, kinsan baya wuce tsakani na da dak'ik'an mutanen garin nan"

Annu ta sauke ajiyar zuciya tace "Haba Saaya kayi kunnen shegu dasu mana, mutanen nan ba dena tononka zasuyi ba, don ma kana kai amma da ace wani ne aida tuni an kashe sa an manta da labarin sa a garin Dulme, kasan fa kana matsayin marar addini ne a garin nan"

"Annu akwai abunda ya kamata na sani ne game dani? Saboda yanzu naji kince don ma ina ni, inaso nasan abunda ban sani ba Annu, wanene ni? "

"Saaya bansan me kake magana akai ba, duk lokacin da kayiman irin wannan tambayar ni kaina nakan shiga tinani, banyi maka wani sani daya wuce kai d'ana bane, ni yakamata ka amsa ma tambayar da nake mayar maka kullun, shin Saaya meye yasa kake yawan tambaya ta ko kai waye bayan kuma kafi kowa sanin kanka?"

Kafin yayi magana saiga abokinsa *Ale* ya shigo.

"Gafara, Zuba ya taimake ku" inji Ale.

"Ah, kaiiii mugu ina ka b'oye ne? Duk jiya banganka ba ko jaffa ce ta b'oye ka?" Saaya ya tambaya fuskarsa shinfid'e da murmushi.

NAHIYAR MU...{Our Province}Where stories live. Discover now