10

124 7 0
                                    

🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾

   🌾 *OUR PROVINCE* 🌾

*Na Aysha Sada Machika*

*10*

Zata luma a cikinta, ga mamakinta sai ganin wuk'ar tayi ta kufce daga hannunta, tayi gefe ita bata fad'i ba ita bata yi sama ba, shigowa akayi d'akin da sauri ta juya don ganin waye.

"Nine karki ji tsoro gimbiyata" cewar sarki Diyara.

Ya k'ara da cewa "meyasa kikeso ki datse rayuwarki bayan kinsan inada buk'atarki a doron duniya, gobe iyanzu kin zama matata, Fauwa ki dena fushi banason b'acin ranki"

Fauwa nada maganganu da dama da zataso amayar wa azzalumi sarki a cewarta, saidai tana b'akincikin yaji sautin muryarta, hakan yasa tayita had'iyar kalmomi tana korawa da yawu, ko had'a ido dashi ta kasa, kanta k'asa yake duk wannan zantukan, Fauwa ganinsa take tsoho tukuf wanda ze iyayin sa'a da kakanta.

K'arar zubewar wuk'arnan k'asa yasa Fauwa dawowa cikin hayyacinta, ta kalli gefen wuk'ar, shiko sarki yace "ki kwantar da hankalinki domin koya kikaso cutar da kanki cikin gidan nan bazaki iya ba, kisa aranki kin zama mallaki na" ya sakar mata murmushi sannan ya fita.

Fauwa ta fad'a kan shinfid'a sannan ta fashe da wani matsanancin kuka.

*********************

Su Saaya kusan lokaci guda suka isa gida dasu Ale, saboda su Ale na zama su Saaya suka shigo, be zame ko ina ba sai gefen mahaifiyarsa Annu da tayi butu-butu da k'asa, ya rik'a jijjigata amma sam bata lumfashi, Usman yace ko za'a gwada sa mata ruwa ta yiyu doguwar suma tayi amma bari mu gani, Usman ya matso ze tab'a ta Ale yace "dakata karka sake ka tab'a mana Annu domin ga dukkan alamu kai matsafi ne me shan jini, munsan Annu ta mutu Kuma yanzu haka muna saran tanacan gaban abun bautarmu Zuba, yayi mata tarba da musamman"

Shikam Usman wasu lokutan maganganun mutanen garin nan sukan tashi daga bashi mamaki su koma bashi dariya, hakanan dai yake dakewa don gudun sab'ani kar ya kira ajalinsa da kansa.

"A'a barshi yayi abunda zeyi mu gani" inji Saaya.

Ale ya kafe Saaya da ido na wani tak'aitaccen lokaci sannan yace "kasani Saaya tun muna yara muka taso tare, dukda cewa baka yadda da addininmu ba kowa na kyamarka hakan besa na guje ka ba, ni kad'ai ne  abokinka nake tare dakai amma yau ga lokaci yazo da kake nuna ma wani so fiye dani, kana gasgata duk abunda ya fad'a, haka ka zab'i ka mutu dashi kan ka rayu dani, na barka dashi"

Ale ya mik'e a fusace ze fita, Saaya Shima ya tashi da sauri ya rik'o Ale ya tare hanya, yad'an daki  damtsensa cikin wasa yace "haba Ale, ba haka bane kaima kasan ina sonka, ta yaya zanfi son bawa na fiye dakai, kawai dai ni bansan menene ba, amma akwai wani abu da nake ji a tare dashi, tabbas ya shiga raina bankuma san dalili ba amma karka had'a kanka dashi don kowa da wurin sa"

Ale bece komai ba ya ture Saaya gefe ya wuce, tsaya yad'an Jima a tsaye domin tunda yake da Ale basu tab'a samun sab'ani ba sai yau, yasan cewa Ale na amanarsa ne, yanason sa matuk'a kuma kome Saaya zeyi ko zece shi a wurinsa dai-dai ne koda ace ba dai-dai d'in bane, saida Tura ya kira sunansa sannan ya juyo ya dawo gefen Annu, ya kalli Usman, Usman shima beji dad'i ba.

Saaya ya bashi damar matsowa yayi abunda zeyi, Usman ya tab'a wuyanta da jijiyar gab'ar hannunta, cikin farinciki ya sanar dasu Saaya cewa tanada rai a kawo ruwa, Saaya ya tashi da sauri ya d'ebo ruwa, suka yayyafa mata karo na farko bata motsa ba, suka sake sa mata ruwa shiru, hankalin Saaya ya k'ara tashi, yaje ya d'ebo ruwa cike da k'ok'o ya kwara mata har saida su Usman da Tura dake gefe suka jik'e Suma, habaaaa saiga Annu ta saki lumfashi, Saaya besan sanda ya rungumeta ba sai hawaye sharrrrr, abunda basu tab'a gani ba nima haka.

Annu tad'anyi k'ara kad'an alamun zafi take ji , sannan ne Saaya ya sassauta ya saketa, sawun bugu gasunan ajikin Annu Kamar an samu jaka.

Manaay ya shigo, ga mamakinsa sai ya gansu, yaji dad'i marar misaltuwa, yaje ya rungume Saaya Yana fad'in "abun bauta ya kula dakai Saaya, abun bauta ya taimake ka, yayi maka abunda kayimana yakuma baka sa'a"

Sannan ya shafa kan Annu dake matuk'ar jin jiki, shiko Saaya namijin duniya har yama manta da bugun daya sha.

Manaay ya d'auki Annu ya shigar da ita ciki sannan ya fito yana had'a wuta ze had'a mata ruwan zafi.

Tura ya k'ura ma Usman ido, Usman hardai ya gaji yace "lafiya?"

Tura ya girgiza Kai yana murmushi, sannan yace "bani labarin addininka"

"Addini na?" Ya tambaya.

Tura yace "eh".

"Addini na bana tantama da cewar shine addinin gaskiya, labarinsa nada tsawo Kuma kashi-kashi ne, kama daga kan ni'imomi na ubangijinmu Allah, isarsa, ikonsa, rahamomin sa da sauransu, zuwa kan mala'iku, annabawa, sahabbai, malamanmu, shuwagabanni, mutane aljanu, dabbobi da ababan more rayuwa, addini na shine addinin da bebar komai ba, duk tambayar da kayi yanada amsarta, zaman yanzu baze isa na gama fad'a maka addini na ba, atak'aice shi addinina iliminsa nada zurfin gaske ma'ana yanada fad'i, har mu mutu bamu tab'a sanin komai da komai, saidai me, idan akwai abunda ya shige maka duhu zaka iya tambayata idan na sani na baka amsa idan ma har bansani ba nasan malamai na basu rasa sani saidai ganinsu ne da wuya, koda yake ubangijinmu ya umarce mu da mu fita mu nemo ilimi komin nisan wuri"

"Meye malamai?" Tura ya tambaya.

"Malamai sune mutanen da ubangijinmu mu ya zab'a gami da basu baiwar saninsa dakuma addininsa, sune wanda muke jewa d'aukar karatu wurinsu, wanda muke nemo haske daga garesu yayinda muka shiga duhu, sune mutanen da keda amsoshin mafi yawancin tambayoyi kan addinin mu na musulunci"

Tura yace "a addinin mu matsafanmu sukan ce mana akwai tambayoyin da basu da amsa, kai kuma naji kace kunada amsar kowace tambaya"

"K'warai kuwa" Usman ya amsa a tak'aice.

"Zan rik'a yi maka tambayoyi akan wasu abubuwa da suka shigemin nima, dafatan bazan takura maka ba?" Cewar Tura.

Usman yaii dad'i sosai, a ransa yace "Allah ka bani ikon amsa masa duk tambayar dazeyi min" a fili ko sai yace "babu damuwa"

Saaya dai na gefe yanai masu kallon tara saura kwata.

**********

Ba'a jima ba saiga Nayzu mahaifiyar Fauwa ta shigo a rud'e tana kuka, ba shiri Saaya ya mik'e ya tareda yace "lafiya"

"Babu" ta amsa atak'aice.

Sannan ta cigaba da cewa "Fauwa ce, Fauwa na gidan sarki ta kai kanta domin ceto ka, yanzu haka sarki nacan ya bada damar sanarwar aurensa da za'ayi da ita gobe, abokin Kuyal dake aiki gidan sarkin ya kawomin labarin yanzunnan"

Saaya ya juyo rai b'ace yace ma Usman "kace dani abun bautarka ne ya kub'utar damu ashe Fauwa ce ta sadaukar da kanta saboda mu, to ina rantsuwa da girman iyayena idan har wani abu ya faru da Fauwa sai nayi bikin fed'eka da ranka sai muga abunda abun bautar naka ze sake yi............

NAHIYAR MU...{Our Province}Where stories live. Discover now