5

78 8 2
                                    

🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾

     🌾 *(OUR PROVINCE)* 🌾

*Na Aysha Sada Machika*

*5*

Idanu duk suka dawo kan Saaya, ga Fauwa ya rik'o a hannu kamar ya d'auko jariri, suka ci Sa'a Sarki Diyara na zaune gaban fada, yaci ado yana jiran a kawo masa sabuwar amaryarsa ayi shagalin aure.

Saaya yazo gaban sarki ya tsaya batare daya sauketa ba, kuma bece da kowa k'ala ba, Zuru yace "meke tafe dakai d'an samari?"

"Nazo ne na gayyaci sarkinku da mutanensa zuwa d'aurin aurena da masoyiyata Fauwa, ina fatan zaku samu halarta domin da kaina nazo ba sak'o nayo ba"

Zuru cike da mamaki ya juya ya kalli Sarki Diyara, shi kuma Sarkin yanai ma Saaya kallon gawa, domin ko yaga gadara da rashin kunya tsantsa acikin kalamansa.

Saaya ya k'ara da cewa "muna nan zamu jira zuwanku a bakin rafin Dul, domin samun albarkarka yakai wannan tsohon sarki namu"

Sarki Diyara ya turnik'e fuska jin ya kirasa da suna tsoho, Zuru ya fahimci b'acin rai matuk'a bayan kallo d'aya tak daya sake yima sarkin, hakan yasa yace "hattara dai d'an samari, Zuba ya gafarce ka, baka da matsayin da zaka zo ka gayyaci sarkin sarakuna a wannan yanayin na gadara, bayan sani dakai cewa wannan yarinya itace matar da sarki ze aura yau d'innan"

"Haba? Tooo ai bansani ba, ta yaya masoyiyata wadda muka taso da son juna tun yarinta zata zama matar Sarki" yayi murmushi ya cigaba da cewa "wannan ai yafi k'arfin uba saidai yayi jika da ita, nasan wasa kuke domin a al'adarmu daman duk wani tsoho yakan yi wasa da matasa a matsin jikokinsa"

"Hattara dai k'aton Arne" cewar wani dogari.

"Na barku lafiya" Saaya ya fad'a gami da juyawa ya nufi hanyar fita, zuru ya yunk'ura ze dakatar dashi Sarki Diyara ya hana, Saaya ya fice hankalinsa kwance.

Bayan daya fita Sarki Diyara ya shiga cikin gida Zuru ya bishi a baya.

Matan gidan sarki sai y'an maganganu suke, suna yaba abunda Saaya yayi, bayin gidan ko suma sai jin dad'i suke suna dariya a b'oye.

"Ka shirya mutane muje bakin rafin Dul" cewar sarki.

Zuru ya zaro ido yace "Zuba ya taimake ka, amma dagaske zuwa auren zakayi?"

"Ko kuma zuwa d'aukar ransa ba, ku shirya muje, inaso ayi masa kisan wulak'anci a gaban mutanen garin Dulme, kai a had'a harda mahaifansa ma duk, bana da buk'atar ganinsu a doron duniya"

"An gama yakai sarkin sarakuna" cewar sarkin matsafa Zuru, sannan ya fita domin kiran jama'arsu.

**********

A b'angaren su Saaya ko, be ajeta ko ina ba sai bakin rafi, kafin kuce me har mutane sun fara taruwa, wasu ko don gulma ma zasu so zuzo domin ganin yadda zata kasance tsakanin sarki da Saaya.

Caan aka hango k'ura na tashi, wazasu hango? Sarki Diyara ne da muk'arrabansa.

Saaya ya saki wani d'an iskan murmushi yadda kasan ya taki wani abu nanko be taki komai ba sai k'asa.

Yana hango su yajawo hannun Fauwa suka shiga cikin ruwannan, bayan da suka shiga sai suka cire kayansu kamar yadda addininsu da al'adarsu ya gindaya masu, suka nitse cikin ruwannan, daidai lokacin da su sarki suka iso su kuma adaidai nan suka d'ago kawunansu.

"Ku shaida ni Arkisaaya d'a ga Annu da Manay na auri Fauwa yau, ta zama mallakina ni kad'ai" Saaya ya fad'i haka fuskarsa d'aure.

Ran sarki Diyara ya b'aci, ya juya ya kalli Zuru, kallo irin na takaici yace "ku kashe shi ku fiddomin ita nan"

Mayak'an sarki kowa ya fara raba ido, ga makamai duk sun fiddo amma sun kasa yin komai sai dube-dube suke, Sarki ya daka masu tsawa yace "me kuke jira? Na rantse da abun bautarmu Zuba idan kukayi wasa zan had'aku tare dashi nayi maku kisan wulak'anci"

"Ranka shi dad'e maigirma sarkin sarakuna ai mu bamu ganin kowa" cewar d'aya daga cikin mutanen nasa.

Zuru yace "gaskiya ne mu kad'ai ke ganinsu, muma d'in idan mukayi yunk'urin kai masu hari to lallai bazamu gansu ba" ya k'arasa maganar yana mai k'ura ma cikin rafin ido.

"Wace maganar banza ce wannan kake yi Zuru? To su idan sun kasa kai kayi mana, kaine sarkin matsafan garin Dulme" inji Sarki Diyara.

Zuru ya bud'e baki kenan zeyi magana sai yaji wata dakusassar kod'ad'd'iyar murya tace "Shekaru masu dama yakai Zuruqum, dafatan kana cikin k'oshin lafiya?" Ya juya gefen da muryar ke fitowa, sai ya hango k'yamusassar tsohuwa ta k'walalo masa ido.

"Tawasugga" Zuru ya fad'a a fili gami da zaro idanu.

Sarki ya sake daka tsawa a karo na biyu, wanda yasa Zuru dawowa cikin hayyacinsa.

"Meye Tawasugga?, ina cewa ka kashe sa kana wata maganar ta daban" inji Sarki.

Sai a lokacin Zuru ya gane cewa shi kad'ai ke ji kuma yake ganinta kaf fad'in wurin, kafin ya juyo daga kallon nan da yayi ma Sarki Diyara har ta b'ace, suma su Saaya da Fauwa mutane suka dena ganinsu sun b'ace b'at.

Cikin kurari da d'aga murya Sarki Diyara yace "suna ina, ina suka shige? Ku nemo su"

Kowa yayi cokar-cokar domin abun ya girmi saninsu, Sarkin matsafa kansa be motsa ba su ina suka ga ta motsi, Zuru yace "Zuba ya taimake ka, inaga kazo muje gida ne kawai, akwai rud'ani cikin lamarin nan, zamu nemo su duk inda suka shiga"

Sarki Diyara ya gama tsayuwar gami da huci sannan yaja jiki fuuuuu suka wuce, mutanen garin Dulme abun nema ya samu, aisai surutu ya kacame, kowa da abunda yake tofawa.

Kan hanya Zuru ya fad'a tinani "meye ya jawo baiyanar Aljana Tawasugga, ina kyautata zaton ita ke kare bak'in arnen yaron nan Saaya, shin waye Saaya? Meye gaminsa da Aljana Tawasugga? Akwai abunda ya kamata na sani" maganar da yayita yi kenan a zuciyarsa har suka isa fada.

Niko marubuciyar sai na fara yima kaina tambaya kamar haka "shi Zuruqum a ina yasan wannan tsohuwar Aljanar? Sunada wata ajiyayya ne a tsakaninsu? Wai meye gamin tsohuwar nan da labarin Saaya ne?

*********

Annu tana can tana ta zarya band'aki, tsabar tsurewa yasa data fito sai cikinta ya k'ara katsawa ta koma, ta kasa zuwa wurin wannan kasada da Saaya yayi, domin a cewarta bazata iya gani akashe d'anta d'aya tilo a gabanta ba, jira kawai take a kawo mata gawarsa ko kuma a kawo mata sak'on mutuwarsa, duk abunnan dake faruwa manay baya gida yana daji samo nama.

********

" Saaya! Saaya! Kai Saaya"

A firgice Saaya ya bud'e ido ya zabura ya tashi zaune, itama Fauwa haka.

Manay ne yaci karo dasu shame-shame cikin daji a k'asa an rufesu da ganye, kunya duk ta kama Fauwa saidai tayi ta faman jan manyan ganyayyaki tana rufe k'irjinta domin ko zindir suke babu kaya.

"Me ya kawo mu nan?" Saaya ya tambaya.

Manaay yace "nidai zan tambaye ku abunda kuka zo yi cikin wannan dajin.

"Arkis wai meke faruwa ne? Nidai nasan da muna cikin rafin Dul ne.

Manay ya zaro ido yace " me kuka je yi rafin Dul?"

"Aure mukayi" Saaya ya amsa a tak'aice................

NAHIYAR MU...{Our Province}Where stories live. Discover now