14

15 4 6
                                    

🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾

     🌾 *OUR PROVINCE* 🌾

*Na Aysha Sada Machika*

*Page 14*

Diyara ya saki baki cike da mamaki, daga bisani ya saki wata iriyar dariya ya juya ya kalli mutanen dake kewaye dasu ya sake fashewa da dariya sannan yace "yayi Namijin duniya, lallai Kai jarumi ne a soyayya amma zaka k'asara jaruntarka a kurkuku yayin dani kuma zan angwance da farincikina zinariyar mata wato Fauwa"
Sannan ya juya ya kalli dogarawa yace "ku kama su, ku masu jahilin bugu sannan ku d'aureman su a tsakar gari kuyita doka masu ganga"

Batare da b'ata lokaci ba dogarawa suka kama Saaya da Tura, suna k'okarin jansu Saaya cikin hargagi da d'aga murya yace "Ni Saaya haifaffen d'ane ga azzalumin sarkinnan naku Diyara, ku bani dama na kawo maku k'arshen zaluncin sa"

Diyara ya sake fashewa da wata iriyar dariyar rainin wayo a karo na biyu,
Mutanen wurin kuma sai maganganu sukeyi k'asa-k'asa, yayinda wasu Kuma da suketa harkar gabansu suka tsaya cak sakamakon furucin da Saaya yayi.
Ya cigaba da cewa "na rantse maku da iyayena Annu da Manaay ni keda wannan kujerar mulkin, kunyarda cewa yayin da d'an mai mulki ya tasa za'ayi bikin kisan mai mulki a mayar da d'ansa kan kujerar mulkin, to ni d'a ne a wurin wannan tsohon banzan"

Wani cikin dogarawa har ze Kai masa hannu sai sarkin matsafa Zuru ya k'araso yace "kaiii yaro Anya kana cikin hankalinka kuwa? Babu wani jinin sarkin sarakuna Diyara dake lumfashi a doron duniya domin da akwai shi da mun gano shi, ku sani cewa ninenan sarkin matsafan garin Dulme da kewaye babu wani abu daya isa ya shigemin duhu da yardar abun baitarmu zuba"

Zuru ya maida dubansa ga Saaya ya kara da cewa "kace kai d'a kuma jinin sarki Diyara ne meyasa kake rantsuwa da mutanen daba iyayenka ba? Ka rantse da wadda ta haifeka mana ka rantse da sarkin sarakuna Kuma ka rantse da abun bauta, sannan ma meye hujjarka? Kuma waye shedarka?"

Ba zato ba tsammani sai sukaji murya mai ban tsoro mai cike da tsananin b'acin rai kamar daga sama tace "nice shedarsa"

Aljana tawassuga ce ta bayyana a wani irin yanayi mai ban tsoro jikinta kamar yanaci da wuta jajjawur daga gani tana cikin azaba.

"Sarkin matsafa zuruqum, shin ina tsafin naka yaje ne daka kasa gane ko waye wannan d'an saurayin?" Inji Tawassugga.

Ta wani bud'e hannayenta a fusace ga mamakin mu sai dogarawan da suka rik'e Saaya suka zube kasa suna murd'e- murd'e, rigar dake jikin Saaya ta rabe biyu, jikinsa duk tabo na yankarsa da take aduk lokacin data bayyana, tayi siddabarun ta sannan ta yarfa ma Saaya hannunta a goshi, take tabban dake jikin nasa suka b'ace, ganin haka yasa Zuruqum dafe kirji gami da zaro ido yaja da baya cikin d'imaucewa, Sarki Diyara na ganin yanayin da sarkin matsafansa ya shiga shima jikinsa yayi taushi.

Sarki yayi k'arfin halin cewa "ke kuma wacece ke aljanar banza"

Tawassugga ta fashe da wata firgitacciyar dariya tace "haba Diyara har kayi saurin mantawa dani? Nice aljana Tawassugga masaniyar duk wani sirri dake masarautar nan, kayi tinanin tsafinka ze hana irinmu bayyana ne? dadai ban bayyana ba saboda gudun mutuwa, a yanzu ko da masoyina arkisaaya ya shirya karb'ar kujerarsa to na shirya mutuwa, inada masaniyar mutuwa ta tazo amma daman nad'auka alwashi kozan riga ka mutuwa to da yardar abun bauta bazan jima ba zaka biyoni sai mutafi can mu had'e"

Ta cigaba da cewa "nasan gane wacece uwar masoyina Arkisaaya ze maka wuya kasancewar irinta da ka kashe Kai kanka bakasan iyaka ba amma abunda ka manta shine (kaza mai kwai a rijiya babu rabon shaho bare kare)"

"Zuruqum yaya akayi ne kayi shiru?" Ta karasa tambayar tana dariya.

Kafin ace me fadar Sarki ta cika mak'il mutane nata baro gidajensu suna zuwa kallon abun alajabi, bawa Usman da Annu dake fama da jiki da Manaay dai suna gida.

Zuru babu baka sai kunne domin ko yaga mutuwar Diyara a idanuwan Saaya, shakka babu Saaya d'an sarki Diyara ne.

Tawassugga ta silale kasa Saaya ya rik'ota suka Kai k'asa tare tana lumfashi dakyar, wani murmushi ta sakar ma Saaya, a karo na farko daya tab'a mayar mata da murmushi,
"Masoyina Arkisaaya, Kai jarumi ne, nasan mahaifiyarka tanacan tana alfahari da wannan jarumtar daka nuna yau, zan tafi sai mun sake haduwa a wata rayuwar bayan wannan masoyina"

Dariya Saaya yayi sannan yace "meyasa bazaki bari ki d'ora masoyin naki kan kujerar mulki ba tukunna? Kuma zanso ki fad'amin ma'anar sunana kafin ki wuce"

Ta bud'e baki zatayi magana kenan sai sukaji muryar mace ance "bata sani ba, ni kad'ai nasan ma'anar sunan, daman na dad'e Ina jiran rana irin wannan"

Wata dattijuwar mata ce acikin mutanen dake tsaye a wurin, ta matso gaba cikin shigar kaya irin na ma'aikatan fada, tace "sunana zaina ni kuyangar sarki ce".........

NAHIYAR MU...{Our Province}Where stories live. Discover now