🌾🌾 *NAHIYAR MU* 🌾🌾
🌾 *OUR PROVINCE* 🌾
*Na Aysha Sada Machika*
*Page 16*
Caraf Sarki Diyara yayi sauri yace "wai yama kake irin wannan furucin zuruqum? Wato kama yadda cewar wannan sakaran jinina ne kenan?"
Zuruqum yayi shiru gami da sadda kai k'asa.
"Kayi shiru, kace wani abu mana" sarki Diyara ya sake magana.
Tawassugga dukda tana cikin azaba na rad'adin mutuwa amma bai hanata fashewa da wata muguwar dariya ba, tace "Hahahahaha d'an jad durun uwar can ai ruwa ya k'are ma d'an kada, fad'a masa Zuru, fad'a masa ajalinsa, karka manta babu sauran rina a kaba" ta karasa maganar tana d'an tari.
"Lallai shakka babu ranar wanka ba'a boyon cibi, a iya abunda abun bauta ya bani ikon gani dakuma shedawa, tabbas Saaya jininka ne, Saaya d'an ka ne ya kai sarkin sarakuna" Zuruqum nakai aya yaji saukar mari, Sarki Diyara ne ya maresa cikin fushi dakuma kad'uwa.
Mutanen garin Dulme yaukam suke ganin abun alajabi, Saaya ya kwantar da Tawassugga sannan ya mik'e tsaye, yayinda Fauwa ta bishi suka mike tsaye tare domin bata ko son kallon aljanar tsoro zubinta da suffarta suke bata.
Saaya ya fara magana kamar haka "be zama dole na nemi amincewar ku wajen karb'ar kujerar mulkin garin Dulme ba, kasancewar na tara na kuma gabatar da duk shedun daya kamata su tabbatar maku ninenan sabon sarki, amma saidai ni zanzo na zama zab'in ku, ba so nake na mulke ku ta karfi ba"
"Karku yadda da abunda ze fad'a maku, sarki Diyara shine sarkin mu, idan ko har wani ze karb'i mulkin nan saidai bayan raina" Kuyal ne yayan Tura da Fauwa ke magana, ya k'arasa maganar yana me zare takobi"
Wani tsoho a cikin mutanen garin yace "kaiii yaro shin yadda kowa yasan kai arne ne ina muke da tabbacin zaka barmu mu cigaba da bautar ubangijin mu na kaka da kakanni?"
"Zan bama kowa damar bauta ma koma me mutun yakeso ya bauta mawa, zan kuma bama kowa damar aiwatar da bautarsa yadda yakeso ya aiwatar da ita, ba Kuma zan yanke al'adu da bukukuwan al'adu ba ko guda d'aya saidai zan canza salon wasu abubuwan da kuma tsarin mulki, ta hanyar y'anta duk wani bawa da sauransu"
Nan da nan aka hau ihu, alamu sun nuna cewar jamaar garin dulme sun amince da kasancewar Saaya sabon sarkin su.
Kuyal ya matso a guje da takobinsa ze cakama Saaya ta baya, ga mamakin mu sai wani daga cikin dogarawan sarki ya tare gami da fille kan Kuyal, hakan ba k'aramin tsorata Sarki da zuruqum yayi ba, domin Koda haka aka barsu sunsan cewa lallai garin Dulme yabar hannunsu, Tura dukda yana cikin alhinin rasa d'an uwan nasa amma bai bari fuskarsa ta nuna hakan ba domin shima jarumi ne na gaske, Fauwa kam kuka taketa yi, kamar daga sama sai ga Ale ya matso fili ya zare tasa takobin shima, kowa ya zata fad'a zeyi da abokin nasa Saaya sai suka ga ya caka takobin k'asa ya zube k'asa shima gaban Saaya alamu da ke nuni da cewa yayi mubaya'a dakuma girmamawa, take dogara suka zube k'asa gaban Saaya gami da saddar dakai suma, nandanan mutanen garin gabaki d'aya suka zube, Tura ya zube shima, Fauwa tazo zata d'uka'a Saaya yayi sauri ya tare ta, ya janyota jikinsa yana mai shafa bayanta gami da sumbatar kanta, domin kuka take sosai.
Zuruqum da Diyara ne kad'ai basu duk'a ba saima kallon junansu da suka tsaya suna yi, da ka gansu kasan a tsorace suke.
Wani siddabaru zuru ya fara yi da hannensa inada yaqinin na Shirin guduwa ne, banyi mamakin yadda a take kasusuwan sa na kafa da hannu suka fara lankwashewa ba ya zube k'asa babu shiri, cikin tsananin ihu na azaba, wannan ba aikin kowa bane face aljana Tawassugga, ganin haka ya masifar k'ara tsoratar da Diyara, domin ko zuruqum shine k'arfin sa.
Saaya ya umarci kowa daya mik'e, Ale yazo ya mangari kan Diyara yace "zube ka kwashi gaisuwa tsohon banza" Diyara kamar zeyi kamar bazeyi ba haka dai har yakai k'asa cikin takaici.
K'arshen tika tiki tik inji bahaushe, ihu aka hau yi ana kad'e-kade, Saaya ya umarci a kwashi Zuruqum akuma tasa k'eyar Diyara aje a kulle masa su, sannan a d'auki gawar Kuyal akai gidansu daganan a d'auko masa Annu Manaay da bawa Usman a kawo masa su fada.
Yace ya nad'a Ale sarkin fada, shi kuma Tura ya nad'a sa sarkin yak'i, sannan kuma kowa ya koma gidansa ya hau shirin gagarumin shagali da za'ayi gobe na aurensa da gimbiya Fauwa dakuma nad'i.
Tun a lokacin kafin kowa ya motsa Ale ya fara aikinsa, yace ma'ai katan fada suje su fidda duk wani tarkace daya shafi Diyara kama daga kan tufafinsa da komai nasa, a wanke fada gabaki d'ayanta da ruwan rafin dul.
Babu gaddama aka hau shiri, Tawassugga ta fara kakkarwa tana jijjiga, koban fad'a maku ba kunsan hakan na nuni da cewa aljannar bankwana take da gidan duniya, da sauri Saaya ya saki Fauwa yaje ya durkusa gaban Tawassugga, muryarta bata fita amma zamu iya gane me take cewa "kaine sarki na yakai masoyina Arkisaaya, kayi mulki bisa adalci, kayi tsawon rai kaine sarkin Dulme, Kai sarki ne d'an sarki jikan sarki, zanyi kewarka masoyina Arkisaaya" bakinta a bud'e ta mutu tana dariya.
Abun da matukar ban mamaki yadda hawaye suka rik'a zuba sharrr daga fuskar jarumin sabon sarkin wato Saaya.
Mutane ne suka bayyana masu tarin yawa, Kai daga gani kasan aljanu ne suka bayyana cikin suffar mutane, suka gewaye gawar Tawassugga, da kaga fuskokinsu kasan suna cikin alhini na rashi, gabaki d'ayansu suka zuro hannuwa suka daddafa kan Saaya batare da sunce ma kowa komai ba sai Kuma aka ga sun b'ace b'at tare da gawar ko sawun su babu, Saaya nanan durkushe a k'asa, Fauwa ce tayi k'arfin halin kamosa suka wuce cikin fada.
*****
Mahaifiyar su Fauwa taci kuka ganin gawar babban d'an nata, haka dogarawan suka wuce suka shiga gidan su Saaya suka barta nan da gawar Kuyal rabi da rabi.
Da shigarsu gidan, sunko ci sa'a duk su Manaay na cikin gidan, Manaay na ganinsu ranshi ya bashi ai ta faru ta k'are shikenan an kashe d'ansu suma kuma yanzu zaa kashesu.
"Sarki ya umarce mu damu d'auko ku kuma karmu dire ku ko ina sai fada" wani a cikin dogarawan ya fad'i haka.
Aisai Annu dake kurya tahau kuka, haka ko dogarawan nan suka sab'e su kaf suka nufi fada dasu.........
YOU ARE READING
NAHIYAR MU...{Our Province}
Historical FictionRayuwar maguzanci awancan shuɗaɗɗen yanayin...