Chapter seven

3 0 0
                                    

Wannan labarin ba karamin dagamin hankali yayiba, na gane matar da ta gayawa maman Fatima kawar Batul saboda dama asali sanda tazo karbar dinki kallon da naga tana yiwa Muslim din sai da naji banji dadinsaba amma sai wata zuciyar tace kishine nake saboda ta kalli abinda yake nawa, a lokacin suna simintin bandakine ya fito kuma wallahi ba gajeran wandone a jikinsaba three quarter ne Wanda yake aiki dashi da kuma farar t-shirt, tunda suka fara aikin kullum dasu yakeyi har Ina tsokanarsa Ina cewa babu yadda za'ayi rigar ta fita shi Kuma yace za ta fita.

Tunda suka fara aikin idan rana ta daga su Muazzam da al'ameen na cire riga amma shi bai taba cirewaba duk gumin da zaiyi amma duk da haka sai da akayi mana sharri Kuma ma sharri mummuna irin wannan.

Shi Muslim dinma naga kwata kwata bai damuba kawai shrugging yayi yace wai matsalarsuce sai dayaga na tashi nawa hankalin sannan ya zauna yace "Kinga pretty tsaya kiji shifa al'amari na rayuwar yanzu abubuwa uku zaki damu dasu na farko ubangijinki ki tababtar baki tsallake sharadinsa ba, na biyu makusantanki me suke tunani? Sun yadda dake ko kuwa? Makusantanki Ina nufin su Muazzam ba makotaba sai na karshe me zuciyarki takeso? Shin da gaske kinason abinda kikeyi ko bakyaso kinayine a dole dan wasu naso? Ki tababtar kinayin abinda kikeso that's it! Indai kin bi wannan maganar tawa abinda mutane ke cewa a kanki bazai taba bata miki raiba indai kin kare hakkokinnan uku karki wani damu da me Yan unguwa sukace kinjiko?" Nace "Amma Yaya Muslim ko a musulunci ana amfani da shedar mutane idan bawa ya mutu" Muslim yayi dariya yace "haba pretty da iliminki fa, an gaya mana shaidar mutane nada muhimmancine saboda anaso mu zama masu kyakykyawar mu'amala da mutanen amma badan wai shedar tasu zata iya tasiri akan hukuncin ubangijinki ba" shiru kawai nayi nasan duk abinda ya fada gaskiyane amma still idan bamu damuba bamuyi kyakykyawar mu'amalar da akeso muyiba kenan.

Tun daga ranar sai na koma duk sanda Muslim ya shigo gidan sai na kasa sakewa nayi ta kallon kofa Ina ganin kamar ana lekenmune, idan na fita sai in dinga ganin kamar mutane kallona sukeyi, kusan gaba daya yan uwana basu damu da abinba kamar Muslim amma ni abin ya dameni da gaske.

Dama zaman kanmu mukeyi a yanzu samun miji zaiyiwa kannena wahala ni kaina da nake da Muslim dinma a kila wa kala nake, dangin mahaifinmu sun watsar damu yanzu idanma aurenmune ya tashi na tabbata ba lallaine su shigaba sannan Kuma azo ayi mana wannan bakin fentin? Ai abin da matsala.


Muslim

Tun sanda nasan kaina na san pretty kuma tun a lokacin nake kaunarta, banajin zan taba iyayin rayuwa ba ita idanma nayi rayuwar to mai cike da kunci zanyi shiyasa a duk lokacin da aka bata mata rai tace na rabu da ita inajin kamar tana zaremin numfashinane.

Tun sanda na nuna da gaske nakeson pretty kuma aurenta nakesonyi na sanar da momyna saboda nasanta da son duk abinda nakeso, tana kaunata sosai sama da duk sauran 'yan uwana burirrikanta kullum a kaina suke a lokacin ma danace agric zan karanta sai da tayi iya kokarinta Wai na koma medicine ko engineering saboda a ganinta shine zan zama wani abu Ni Kuma na kafe nace agric nakeso, ganin inaso dole ta hakura shiyasa wannan karon ma na saka ran zata goyamin baya amma sai naga tayi fir tace wai batasonta.

Abinda na saka a raina shine idan taga ina kaunar pretty itama zata so ta Amma shiru. kullum kokarina shine ta sota kamar yadda nakesonta amma sai ma naga kamar kara mata kiyayyar ta nakeyi.

Lokacin da su Inna suka rasu hankalina ya tashi matuka saboda kallon iyayenake musu Dan a hannunsu na tashi su na fara sani a matsayin iyaye, na biyu kuma nasan za'a iya rabani da pretty babban tashin hankalina ma shine a tafi da ita Kano, addu'a nayi tayi Allah yasa abarta anan garin ni Kuma zan dauki nauyinta ita da kannenta gaba daya Koda kuwa zanyi dakone, Allah maji rokon bawa sai Kuwa ya amsamin sai ma aka barta a unguwar bama a garinba dan haka na zage damtse nake cika alkawarin da nayiwa Allah.

Tun farkon rasuwar su Inna momy ta kirani tace "Muslim kasan dai dama tun asali bason yarinyarnan nakeba ko? Balle yanzu da ta zama marainiya yanzu duk wani abu da ka samu a kanta zai kare alhalin ni nasha wahalarka, Dan haka banasonta na gaya maka ina kuma son ka rabu da ita" na Dan marairaice fuska dan indai momyce har shagwaba yi mata nake nace "haba momy ki duba irin wahalar da Inna tayi miki akan yayanki menene dan muma mun kular mata da nata yayan?" Momy ta harareni tace "sanda tayimin wahalar a kyauta tayi? Biyanta nakeyi da bana biyantama da bazatayiba" nace "shikenan naji biyanta kikayi to yanzu muma idan muka taimaka musu sai Allah ya biyamu ko?" Tace "to jikan sheikh jafar Adam tashi ka bani waje" sumi sumi na tashi na fice daga gidanma gaba daya tun kafin mu haura.

ZulaihatuWhere stories live. Discover now