Watan su Inna guda da rasuwa amma idan ka kallemu zakayi tsammanin sunfi shekara, gaba daya mun lalace kaf cikin babu wanda baiyi wata muguwar ramaba har Muslim, gashi dai abinci dai dai gwargwado kamar yadda yayi alkawari kullum zai kawo mana abinda zamuci safe rana da dare sannan nima an Dan fara kawomin dinki ina Dan samu ina ragewa Muazzam ma yana dan samowa daga garejin da yake zuwa dan yanzu ya fara koyon aikin yanayi da kansa Dan haka bawai yunwace ta saka muke a hakaba ba rashiba ni kaina bansan dalilin lalacewar tamuba.
Kullum zan share gidan nan tas kamar yadda na saba amma sai in ganshi kamar akan bola yake kwata kwata bayayimin kyau ko kadan.
Zamuyi wanka mu saka kaya amma sai inganmu dukun dukun, kullum muka kwanta da daddare sai inyi ta ganin kamar wani zai hauro mana gidan koma nace zai shigo tunda kofar dama karata kawai akeyi ba rufuwa takeba.
Kullum sai Muslim yayi tayimin fada Wai nice naki fawwalawa Allah na dau kaddara shiyasa suma kannena suka kasa daukanta, a ganinsa ina sane na kasa hakura baisan kuma babu irin kokarin da banayi ba Dan kawai kannena suga na saki jiki suma su saki amma na kasa.
Rannan ina shara a tsakar gida da safe bayan yaran duk sun tafi makaranta sai ga farida kanwar Muslim da muke saanni da ita, Inna tace tare ta rainemu da ita lokacin ana kawota wajen Innan, ta shigo ko sallama babu tana wani yatsina fuska tana kallon tsakar gidan na dago kai na kalleta sai na saki fuska duk da batayimin sallama ba amma nayi mata uziri.
Fuskata a washe nace "ahh farida sannu da zuwa" sai ta dagamin hannu tana cigaba da yatsina fuska tace "ke dallah malama dakata ba zuwa nayi ki yashemin baki kiyimin sannu da zuwaba, bakiga ko sallama banyi mikiba? To saboda babu aminci a zuwan nawa shiyasa bazan nema miki Shiba" abin ya bani mamaki ni bansan laifin da nayi mataba da yakai girman da har zatace Wai bata nemamin amincin Allah.
Duk da haka na daure nace "to Allah ya baki hakuri duk da bansan laifin da nayiba" tace "kina sane mana muna fika saboda iyayenku sun mutu kina tunanin nauyinku ya dawo kan Yaya Muslim ne ko menene? Shikenan kun maidashi saniyar tatsa kullum shine cinku sitirarku da maganinku? Aikin me yakeyi kuma waye shi a wajenku? To wallahi bari kiji nice daidai ke shiyasa na fara zuwa nayi miki warning idan bakijiba Babu abinda zai hana muzo gaba dayanmu mu nakasaki wallahi banzaye masu San zuciya haka jiya kawai saboda kunyi pressuring dinsa ya daga filinsa ya siyar babu wanda ya sani sai dazu aka zo aka gayawa momy kuma munsan a kanku zai karar dashi kwadayayyu kawai" tana gama fada ta juya ta fice ta barni da sakakken baki.
Har ga Allah ni bansan Muslim ya siyar da filiba a nasan dai yana da filin kullum yana maganar irin ginin da zaiyi mana a kansa, idan da nasan zai siyar a dalilinmu wallahi ko ita momyn nasa ba zata kaini jajircewa wajen hanashiba amma ni din ni a akazo akewa rashin mutunci a dalilinsa.
Gaba daya ji nayi jikina ya saki bani ma da karfin da zan karasa sharar Dan haka naja kafata da kyar na koma dakinmu na zauna kawai nayi shiru, bansan kuka nakeba ban kumaji shigowar al'ameen ba sai ji nayi yana jijjigani yana cewa "Yaya Zulaihatu menene kike kuka?" Da sauri na share hawayen na kakalo murmushi nace masa "ba kuka nakeyiba autan Inna" yace "gashinan kuwa ina kallo da idona kina kuka" nace "sharafa nake abu ya fadamin ido shine na dawo daki leka ka gani ma sharar da nake" ya daga mataccen labulen kofar ya leka tsakar gida sai kuma ya dawo ya fara gogemin idon yana cewa "ayya sannu watakil tsakuwace kiyi zamanki bari na karasa miki sharar" na rike hannunsa nace "ka dawo daga makaranta a gajiye zakayi shara? Bari na karasa" na mike sai Kuma na kalleshi nace "wai ya akayi ma ka dawo yanzu? Badai har an tashiba ko girki ban doraba" ya sunkuyar da kai yace "aa ba'a tashiba" nace "to meya dawo dakai gida?" Yayi shiru sai dana sake maimaita masa tambayar sannan yace "kudin makaranta akace nazo na karba".
Nima shiru nayi Ina tunanin yanzu da Yaya za'a samu? Can nayi ajiyar zuciya nace "Allah zai hore" sannan na juya na fita amma kaina cushe yake da tunaninnika na yadda za'ayi a samu kudin Kuma ba wani ma yawane dasuba amma fa ga maisu kenan.
