Sanda naje iya kacinmu student ne kawai a harabar wajen sai malamai ana ta shirya wajen, na matsa kusa da yan uwana student na zauna kusa da wata khulsum wadda da itane kawai muke dan magana lokacin training din itama ba wani sabawa mukayiba da yake Ina da wuyar sabo, bayan mun gaisa muna dan hira sama sama can mukaga malaman duk sun hargitse ana ta canja yanayin arrangements na kujerun aka kawo three seater cussians aka saka a tsakiya harda table dogo aka lillibeshi da farin yadi mudai muna zaune sai idan an kiramu ace muyi kaza da mun gama mu dawo wajenmu mu zauna.
Karfe goma mutane suka fara hallarar wajen muma aka bamu wajen zama muka zauna kowa yazo sai ya samu waje ya zauna ana ta saka wakokin siyasa a manyan sifikun wajen, can sai ga yan gidan radio da TV sunzo suna ta kafa kayan aikinsu khulsum tace "zulaiha wai meke farawane? Naga harda yan gidan tv da radio" nace "nima dai haka na gansu dama tun dazu ai naga shirin nasu ya canja maybe wanine zaizo" tace "watakil" daganan bamu kuma bi ta kan abinba muka cigaba da harkokinmu, sai sha daya aka fara shirin bayan wanda suke jira ya iso, kamar yadda mukayi zarki kuwa wani babban dan siyasa ne hon. Musa Babandi dan takarar gwamna shine da kansa yazo ashe shiyasa ake ta faman shiri dan suma basu zata zaizo da kansaba, abinda muka fahimta shine yayi using wannan opportunity dinne zaiyi campaign dashi bawai dan Allah ba.
Bayan jawabe jawabensu aka kiramu shi da kansa ya bamu certificate muka koma muka zauna sai can kuma ya tashi ya sake yin jawabi yace zai bawa kowacce daliba da aka yaye abinyi, wadanda suka koyi dinki da saka za'a bamu kekuna masu kayan su turare man shafawa ko zannuwan gado su kuma zaa basu jari akayi ta ihu ana sai yayi ni kam kaina na kasa ko ta kansu banbiba.
Muna nan sai ga mota katuwa da kwalaye tazo nan fa aka fara kiran sunayenmu ana raba mana su kuma yan jarida suna ta aikin da aka daukosu suyi, nima ankirani aka bani keken dinki da yake kuma ina cikin wadanda suka koyi abubuwa biyu nayi dinki da zanin gado dan haka aka hadamin da kudi ba laifi masu dan kauri.
Munyi murna sosai da wannan kyautar duk da dai daga gani badan Allah yayiba amma wannan matsalarsace ba tamuba su Batul ana ta rawar kai Allah ya taimakeni Muazzam yazo yana dai ta zumbura baki ya daukarmin keken shi da Muslim muka tafi gida baki har kunne.
Bayan mun koma muka baje a tsakar gida ana ta hira can saiga baba ya dawo shima ya zauna na dauko kayan na nuna masa ya dan shashshafa yana ta saka musu albarka har kudin ma na bashi ya jujjuyasu yace "to yanzu sai ki siyo kayan aikin tunda dama jari sukace sun baki" Muslim yace "nima dama baba abinda nake tunani kenan muje ta siyo yadiddika da duk abinda take bukata na zanin gadon da kayan dinki akwai abokaina a kasuwa suna siyarda kayan labulale haka dasu zanin gado sai ta dinga basu suna sara suna bata kudinta" baba yace "tabbas Dan inna haka zaayi shikenan kaga ta samu sana'a kafin Allah yasa ta samu makarantar" haka sukayi ta hirarsu inajinsu daga gefe.
Ai kuwa kamar jira Muslim yace washe gari sai gashi wai na shirya idan ya dawo daga makaranta zaizo muje kasuwa, naso nokewa amma dai na hakura na shirya sai ma gashi bai dawo da wuriba yace mu bari sai gobe tunda dare yayi gobe Kuma bashi da lecture sai 4pm. Washe gari da wuri na shirya su Batul suka tafi makaranta sai gashi yace na fito naje wajen Inna nace "Inna zamu tafi kudin" tace "to" sannan ta yunkura ta daga dan gadonsu inda ta saba ajiyar dan kudinta sai dai tana zarosu taga babu an kwashe abinda yayi saura ko rabi baiyiba.
Ta fara kokarin sake daga katifar wai ko zubewa sukayi fadi take "ke Zulaihatu zo ki tayani duba kudinnan naga saura kadan" nan da nan gabana ya fadi na fara adduar Allah yasa ba Muazzam ne yayimin halin nasaba ai kuwa dai babu kalar neman da bamuyiba baby kudi ba alamarsu, jiki a sanyaye na fito Ina gayawa Muslim shima yayi mamaki sosai dole muka hakura da zuwa kasuwar Dan sauran kudin ba wani abin kirki zai siyoba nace kawai a hakura ko dan kayan abincine a siyo dashi sai ayi addua Allah ya kawo wasu Batul ma kuwa na dawowa daga makaranta sukazo da batun kudin jarabawa aka danka musu shi shikenan ta faru ta kare.
