Zulaihatu

39 0 0
                                    

Tallah! Tallah!! Tallah!!!

Ina tsugunne a gaban murhu Ina ta faman kokarin wuta ta hadu na samu na dafa mana wannan kanzon dana samo dan Saudatu da al'ameen basuci komaiba suka fita nasan Kuma da yunwa zasu dawo kuma sun kusa dan exams sukeyi, ina ta faman hankoron firfita wutar naji kamar an shigo da gudu, da sauri na daga kai Muazzam ne yayi dakinsu da gudu.

Na mike tsaye ina salati Ina tambaya lafiya? Amma ina tuni ya kule a cikin daki, kafin na gaba nutsuwa na zakuloshi a dakin naji jiniyar yan sanda ta shigo layin sai kuma motar tayi parking a kofar gidanmu ba neman izini ba komai Yan sanda suka cika tsakar gidan.

Hankalina ya mugun tashi na nufi wanda yake shigowa yanzu da alama shine oga ina cewa "yallabai lafiya me ya kawoku wa kuke nema?" Ya karemin kallo sama da kasa yace "Muazzam muke nema ina yake?" Na kalli kofar dakin da ya shiga na kalli Dan sandan nace "me yayi muku kuke nemansa? Bayanan" Dan sandan ya danyi murmushi yace "nasan yana nan na Kuma san inda yake kawai so nake ki fada da kanki Dan karmu shiga hakkinki amma idan kinki zan fito dashi da kaina" na fara girgiza kai Ina cewa "na gaya muku bayanan me zakuyi masa? Dan Allah koma menene kuyi hakuri zanyi masa fada wallahi ba zai sakeba zan tabbatar da hakan" Dan sandan yace "Ina iyayenku? Kaninkine ko wankine?" Nace cikin kuka "iyayenmu sun rasu bamu da kowa ka tausayawa maraicinmu yallabai dan Allah ka kyaleshi" nayi tunanin maraicin da na ambata zaisa ya tausaya mana amma sai kawai yayi dariya ya nuna kofar dakin su Muazzam yacewa wasu yan sanda "ku shiga ku fitomin dashi" Ai kuwa ba bata lokaci sukayi cikin dakin Ni kuma na bisu ina faman rokonsu akan suyi hakuri amma kamar ina bawa kare dusa.

Suna shiga kuwa suka dankoshi tunda daman dakin babu wani wajen buya ko guduwa Dan ko gado babu balle ya shiga karkashinsa, haka ina kallo sukayi waje dashi ina binsu ina kuka har mukaje kofar gidan inda na tarar mutane sun taru kamar a filin idi wasu na jinjina kan tausayi wasu na murmushin Allah ya kara sannan ogansu ya juyo ya sake kallona sama da kasa yace "idan kina bukatar dan uwanki zaki iya biyomu office headquarter amma ki sani ba wai zakizone kawai mu bakishiba saboda mun kamashine da harkar drugs so get ready" har ya juya sai kuma ya juyo ya sake kallona yayi wani murmushi yace "ki kuma share wannan hawayen idan zakizo" sannan ya juya ya shige motarsu sukayi gaba suka barni cikin mutane a tsaye.

Zamewa kawai nayi na zauna a dandaryar kasa Ina maida numfashi dan ko energy din kukan bani dashi, sama sama nakejin maganganun mutane "Allah sarki baiwar Allah kullum yana cikin jawo mata magana" "shege Dan iska ai gara da aka kamashi fatana ma su kulleshi can ko ma huta" "gaskiya anyi asarar haihuwa mal Sabo nacan yana tsinewa wadannan 'yayan nasa" "ni na rasa dalilin da baza'a kori yarannan daga unguwar nan ba wannan ai bad influence ne ga 'yayanmu" dama wasu maganganun da bazan ma iya jinsuba, a hankali wani hawaye mai zafi ya tsiyayo daga idanuna zuwa kan kuncina.

Ta baya naji an rungume ni ana cewa "Yaya Zulaihatu lafiya? Menene ya faru? Me kikeyi anan cikin mutane ana ta kallonki?" Na waigo da fuskata jabe jabe na kalli Saudatu kanwata kwaya daya da take iya fahimtar abinda nakeji bayan auta nace "Saudatu an tafi da Muazzam" ta dan yamutsa fuska tace "an tafi dashi ina? Shi da suwa?" Na goge hawayen fuskata duk da ina gogewa wani ya maye gurbinsa nace "Yan sandane suka tafi dashi yanzu sukazo har gida suka tafi dashi" ta warwaro ido waje tace "Yan sanda kuma? Laifin me yayi? Wai yaya Muazzam bazai taba daina abinda yakeyi ba yanzu abin har yakai da Yan sanda?" Nace "Saudatu drugs suka kamashi dasu nasha gaya masa dama irin wannan ranar nakeji nasha gaya masa yanzu bansan yadda zanyiba bansan Yaya zanyi na karboshiba"

Ta daga kai ta karewa mutanen da sukayi saura a wajen da kuma masu kallonmu idan sunzo wucewa tunda gidanmu kusa da titi yake sannan ta mike tana kama hannuna tace "tashi mu koma cikin gida mu koma ciki sai musan koma menene zamuyi Allah nanan shi daya ajiyemu a haka yasan da zamanmu ba Kuma zai juya mana bayaba" da kyar na mike muka koma ciki na zauna a tsakar gida na jingina da dakinmu, kaina gaba daya ya gama daurewa bansan ma yadda zanyiba na tabbata idan naje office dinnan ko zan samu su banishi ba yauba hakan na nufin sai ya kwana kenan cikin wannan wahalar da ake fada da cikin cell, sannan sai sun bukaci wasu kudi ni kuma bani dasu bani da mai banisu.

ZulaihatuWhere stories live. Discover now