Muslim's POV
Kwana biyu da yiwa momy alkawarin rabuwa da pretty dady yazo sai dai kafin ma na shigar da magamar ya fara batun komawarmu Abuja, saboda aikinsa a yaunzu yafi karfi acan zuwan nasa yana bashi wahala sai kawai ya yanke shawarar daukarmu gaba daya mu koma Abujan da zama tunda wajen aikinsa sun bashi wajen zama.
Yana maganar na fito na gaya masa ni bazan komaba anan zan zauna ya nemi ba'asi na fito a mutum na gaya masa saboda su pretty idan na tafi babu Mai kula dasu na kara da cewa "Kuma ma dady ni da nake jiran posting na service ai kaga ba sai nayi wahalar parking na koma Abuja sannan gaba daya bazan wuce Yan kwanakiba na sake dawowa gara kawai nayi zamana, sannan inason na fara survey akan gidan gonar dana gaya maka inason budewa anan Kuma nakesonshi" dady ya jingina maganar sannan yace "ba komai ku Kai da Abdul sai kuyi zamanku mariya da farida dama admission nake nema musu kaga ya kamata ace tun waccen shekarar farida ta tafi dandai bata samu bane yanzu zan iya nema musu anan tamu, ita kuma Salma sai a barta a wajen antynku ta karasa karatunta tukunna" nace "aa dady dama transfer kawai akayi mata itama ta koma can ina ganin bada rukon nata ai bashi da amfani" dady yayi murmushi yace "yaran yanzu baku da zumunci ko kadan gidan yar uwar tawane gidan ruko? Kanwata uwa daya uba daya menene Dan ta rikemin 'ya?" Nima Ina murmushin nace "nifa dady ba cewa nayi ba zata rike maka 'ya ba ba Kuma cewa nayi anyi laifi idan aka bada ita ba amma ina ganin ita Salman ai bazataji dadiba ace an rabata da Yan uwanta ita an barta ita kadai anan su Kuma an tafi dasu" dady ya jinjina kai yace "hakane kaima kayi magana ba matsala zanga yadda za'ayi"
Daganan aka fara Shiri gadan gadan na komawar 'yan gidanmu Abuja, momy batasan babuni za'a tafiba ta dai san babu Abdul saboda tasa makarantar sannan Salman ma momy ta tubure tace da ita za'a tafi Dan haka har munje mun nema mata transfer a makabartar su. Naji dadin komawarnan tasu Abuja a ganina idan momy bata ganina bata ganin pretty zata kyalemu muyi soyayyar mu cikin kwanciyar hankali sannan zata manta da batun rabuwarmu da ta nace akai sai dai da nasan abinda cewa bazanbisu Abuja ba ya janyo tabbas dana bisu na tafi.
Ina kwance a gida kamar Wanda aka tsikareni ko da yake kaddarace ta kirani kawai na mike na fito momy na falo na wuceta har nakai kofa tace "Ina zakaje?" Na waigo nace "zan fita bakin shagon bukarne" tace "a dawo lafiya" nace "ameen" sannan na juya na fice, kullum Ina feeling guilty idan nayiwa momy karya ko nakiyin abinda takeso amma babu yadda zanyine shiyasa.
Ina fita nayi gidansu pretty na danji nayi kamar wani magnet na jana zuwa gareta, Ina zuwa nayi sallama naji ba'a amsaba sai na tura kofar na shiga a daidai lokacin da take fitowa daga toilet da daurin kirji a jikinta kanta babu dankwali daga alama daga wanka take, da sauri na juya mata baya ina cewa "oh my God I'm so sorry" da alama rikicewa tayi itama ta rasa ma Ina zatayi.
Kafin mu gama registering abinda ke faruwa momy ta budo kofar gidan ta shigo, tsayawa kawai nayi ina kallonta ina tunanin me ya kawota? Momy ta kalleni sannan ta kalli bayana da alama har yanzu pretty na wajen kamar amsa ga tunanina sai cewa tayi "munafika hijab din me kike sakawa? Ai Allah ya tona asirinki shegiya yar iska" na kama hannun momy nace "momy please zo muje gida" tana daga hannu ta kwadamin mari, na firgita sosai da marin da tayimin laifin me nayi na mari? Maimakon ta juya mu tafi gidan kamar yadda na roketa sai ta karasa shiga cikin gidan ni ma na bita da sauri ina rike mayafinta tare da rokonta mu tafi gida, zuwa yanzu pretty ta saka hijab kan daurin kirgin jikinta, momy na zuwa ta kare mata kallo tace "Zulaihatu Allah ya isa tsakanina da ke bazan taba yafe mikiba muguwa algunguma yarinya sai kace parasite? Ke babu abinda za'a karu dashi tare da ke sai dai shanye jinin duk abinda kika kama? to wallahi ba zan yadda dana ya zama victim dinkiba, wato jikinki kikeson using Dan kija hankalinsa kanki ko? Parasite kawai Kin nacewa yaro sai zukar jininsa kike to wallahi bazan bariba muguwa" ta waigo ta kalleni tana nunani da yatsa "Kai Kuma saboda banzane baka da hankali duk maganar da akeyi maka baka fahimta bakasan mai sonkaba shine zakace ba zaka bimu ba saboda wannan abar ko? Ina alkawarin da kayimin? Bakayimin alkawarin zaka rabu da itaba? Shine wato mu zaka iya rabuwa damu saboda ita to bari kaji na gaya maka magana ta karshe wallahi wallahi idan baka rabu da itaba na rantse maka da ubangiji sai na tsine maka" fadin kalar tsoratar da nayi ma bata lokacine gaba daya na fito da idanu waje hankali a tashe Ina kallonta daga gefen idona Ina hango pretty ta dora hannu aka.