Chapter one

28 0 0
                                    

Safiyar wata asabar sararin samaniyar garin Dutsen jihar jigawa a lullube da hadari iska na Dan kadawa daga gabas zuwa yamma Mai dadi da kashe jiki, nima nawa jikin a sanyaye na sauko daga motar hayis din da tayi parking a kofar layinmu a unguwar takur aduwa, yaron motar ya bude baya ya fitomin da kayana bagco ce wadda gaba daya ta gama mutuwa sai akwatin karfe irin na Yan boarding sai Kuma yar matacciyar katifata da bokiti shima da Dan tarkace a ciki.
Bayan ya gama sauke min kayan nayi masa godiya suka ja motarsu sukayi gaba suka barni da tulin kaya a gaba, Ni dai nasan indai ba sababbin hannayene zasu tsuro a jikina ba bazan iya daukan kayannan Ni kadaiba dole na Nemo yaron da zai tayani ban Kuma ga kowa Wanda na saniba wadanda ban saniba din kuwa nasan idan na Dora musu to fa tabbas sai na biyasu bani Kuma da ko karfanfana.

A hankali na sauke ajiyar zuciya bayan yanke shawarar in dauki wasu na kai gida sannan na dawo na dau wani tunda gidan namu babu nisa da titin, na sunkuya na dauki katifar na dora aka sannan na dauki bokiti na juya da niyyar zuwa gida sai dai daga bayana naji an rike katifar kaina sannan naji muryar da ko a filin yaki na jita sai nutsuwa ta ziyarci zuciyata tana cewa "haba pretty Ina raye? A Kuma unguwarnan ki dauki kaya a ka? Allah ya sauwake Oya sauke" da murmushi na waigo na kalli fuskarsa kafin nayi magana ya sauke katifar daga kaina ya dora a nasa kan sannan ya sunkuya ya dauki bagco din ya Kuma Miko hannu yace "kawo bokitin" nace "haba dai Ni Kuma ai na rike bokitin ko?" Yace "badai idan Ina rayeba bani duk zan iya" nace "Dan Allah Yaya Muslim ka barni na dauki ko dayane" ya hade rai yace "kinsan kuwa tun 7:00am nake wajennan ko karyawa banyiba kawai dan kina zuwa na riga kowa ganinki sannan kuma na daukar miki kaya amma zakice wai na barki ki dauka?" Haka babu yadda na iya dole na mika masa bokitin ya hada hannunsa Dana bagco din ya rike da hannu daya dayan hannun kuma ya dafe katifar kansa sannan yace "yauwa yanzu naji batu muje to".

Fuskata kamar gonar auduga haka muka jera Ni dashi muna tafiya, jina nakeyi kamar akan gajimare yau nayi candy na dawo gida Ina zuwa na hadu da masoyina zan karasa gida inga Inna baba da Yan uwana, Zan zauna tare dasu Babu batun komawa makaranta hutu ya kare.

Mun fara tafiya nace "uhmm kana nan kana ta daukan kaya ko gaisawa bamuyiba Ina kwana?" Yace "tab Ni nama manta da wata gaisuwa Dan farin cikin da nakeji, ya makarantar shikenan an gama ko?" Nace "inshallah" yace "to alhamdulillah congratulations ubangiji ya bada saa saura University" nace "ameen ya Allah Amma University kam ai ba yanzuba daga dawowata banyi bacciba? Tab" ya fara dariya yace "tab baccin me zakiyi? Pretty yanzu fa duniyar sauri takeyi Dan haka komai da sauri akeyinsa" nace "aa ni kam sai na huta tukunna, kaifa? ya taka makarantar?" Muslim yace "alhamdulillah wlh Ina da lecture 2pm ma yanzu zanje na shirya na tafi kinsan mun kusa fara exams" nace "final kenan ko?" Yayi wani murmushi yace "inshallah" a lokacin da mukazo daidai kofar gidanmu nace "Allah ya bada saa" yace "ameen kinga na kusa makara bazan shiga cikiba karbi kayan ki karasa dashi" bucket da bagco din hannunsa na fara karba nace "bara na mika wannan sai na dawo na karbi wannan din" kai kawai ya kada yana kokarin sauke katifar Ni Kuma na daga labulen buhun da yayiwa tsakar gidanmu sutura na shiga bakina dauke da sallama fuskata dauke da murmushi.

Ina shiga batul da saudatu Yan biyun Inna suka daneni suna ihun murna nima Ina jin wani farin ciki kamar Zan bude kirjina na zirasu a ciki, Inna dake tsugunne gaban murhu itama sai murmushi take harda dariya tana cewa "kuyi hankali yar boarding ce karku ballamin ita" saudatu da sakeni ta waiga tace "Inna karmu balla Miki itafa kikace? Ai ba taki bace ke kadai" batul tana karbar kayan hannuna tace "barta saudatu Wai wariyar launin fata zaa nuna mana tunda ta dawo" da sauri na karasa jikin Innata na rungumeta Ina cewa "nayi missing innata itama tayi missing dina karku saka mana ido" da yake Inna bata kunyata duk da kasancewata yar fari itama sai ta rungumeni tana dariya tace "sosai ma kuwa zulaiha duk munyi kewarki" sai da dumin uwata ya shigeni sannan kamar tuni naji muryar Muslim yana sallama a bakin kofa da sauri na waigo na ganshi ya shigo da katifar a hannunsa ya jingineta jikin dakinmu inna na cewa "au dama kana waje?" Ya tsugunna yace "wallahi kuwa inna ta shigo ta makalkale miki tama manta dani" nace "laa wallahi ba haka bane yanzu fa Zan tura a karbo" duk sukayimin dariya sannan ya gaishe da Inna ta amsa masa cikin sakin fuska kamar d'an da yake a wajenta sannan ya fice yana cewa makaranta zai tafi inna tayi masa addua kamar yadda ta saba.

ZulaihatuTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon