Chapter Six

5 0 0
                                        

Washe gari tun asuba naji jikina a wani irin mace kamar wadda akayiwa duka, haka na koma na kwanta kamar marar lafiya har su Saudatu suka tashi suka gama shiryawa sai dai wannan ya shigo ya taba wuyana yace "Yaya Zulaihatu lafiya?" Idan ya fita wani ya shigo shima ya taba jikina yace "Yaya baki da lafiya?" Haka har suka tafi makaranta ban iya fitoba.

Kwanana uku a kwance ni ba jinyaba ba kuma lafiya kalauba, sai ranar na hudunne ma na Dan ware na fito shima gani nayi muna neman rasa abinda zamuci shiyasa na tashi na karasawa wata mata dinkinta na bayar aka kai mata shine fa muka dan samu abin kashewa.

Tunda muka rabu da Muslim a kofar gidanmu ko nace tun ranar da na koreshi bai sake dawowa gidanba ban kuma jin duriyarsaba sai yau, ina zaune naji ana sallama na amsa na dauko hijab dina na leka alh Bashir babansu Muslim na gani da shi Muslim din, har kasa na zube na gaisheshi yace "muje ciki Zulaihatu magana nakesonyi dake" da saurina na dauko tabarma na shimfida masa na dora sallaya akai sannan na koma gefe na zauna Ina sake gaisheshi.

Fuskarsa fal fara'a ya amsamin sannan ya tambayeni ya kannena suke da karatunsu duk nace suna nan kalau sannan yace "Zulaihatu naji duk abinda ya faru kwana biyu da yake bananan kwata kwata ban saniba sai yau Muslim yake sanar dani banji dadiba kwata kwata wallahi amma Ina mai bada hakuri a madadin iyalina kuyi hakuri" da sauri nace "lahh dady ba komai wallahi ai ya riga ya wuce Kuma ai shima muazzam din da laifinsa bai kamata ya dauki mataki a hannunsaba idan ma bazai hakuraba da sai ya bari ka dawo sai yaje ya gaya maka shima yayi laifi sosai" alh Bashir yace "aa Zulaihatu karki dorawa Muazzam laifi ai shi aka taba itama momyn tasu ta mantane Amma ni a gidana ko yanzu shi Muslim ban yadda ya saka hannu ya daki farida ba gashi dai kanwarsace uwa daya uba daya amma ban yaddaba dan daganan ne zakiga mazan sun saba da dukan mata sai suzo suna dukan matansu amma duk laifin da yarinya tayi sai ka bata punishment wani lokacin ma punishment din har yafi dukan ciwo, Amma ita saboda zuga na dibanta shine ta dauko Abdul Kuma suka shigo har cikin gida ya dakeki a gabanta kamar ba uwaba, Allah dai ya sauwake" duk muka amsa da "ameen" sannan ya cigaba "Kuma shima Muslim din ai yayi laifi me yasa zai dau kadararsa kawai saboda wata bukata ta taso masa ya saka a kasuwa ya siyar? Shikenan sai mutum yace idan yana da kadara da ya shiga matsala option dinsa kawai ya siyar da ita? Ai ba haka akeyiba sanda bashi da ita kumafa ya zaiyi? Idan matsalar kudi ta tasowa mutum nemansu yakeyi dan har gara ka bada ita kadarartaka jingina akan ka daga ka siyar Kuma ni me yasa bazakazo ka gayamin ga abinda ke faruwaba? Ni menene amfanina? Dan haka kaima kana da laifi kuma karka sake kaji na gaya maka?" Muslim ya sake sunkuyar da kai kasa yace "inshAllahu dady bazan sakeba" yace "yauwa yanzu dai komai ya wuce naso ma Muazzam din shima yana nan naja masa kunne duk abinda ya faru azo a gayamin ni zan bi maganar banason na sake jin wata magana makamanciyar haka, sannan" ya juyo kaina "naji wai kinyiwa Muslim iyaka da gidannan da Kuma rayuwarku me kike nufi? Shikenan zumuncin tsakaninku na shekara da shekaru ya tashi a banza kenan? To ban yaddaba gashinan na dawo dashi ya zama wakilina nine na ajiyeshi a cikin gidannan kinaji ko?" Na daga kai shi Kuma ya cigaba "banason sake jin wata magana kunji na gaya muku ku cigaba da zumuncin ku ku cigaba da taimakon juna manzon Allah (SAW) zaiyi alfahari daku kunjiko? Allah yayi muku albarka" ya mike tsaye yana cewa "Kai kuma kazo muje ka dauko wadancan kayan" na bishi Ina godiya har bakin kofa ya sake saka min albarka sannan ya fice.

Daga baya sai ga Muslim ya dawo da exactly kayan da su momy suka kwashe har da karin kudi masu nauyi Wai inji dady yace su Batul su biya kudin makaranta.

Haka nayi tayi masa godiya nace zanje nayiwa dadyn ma godiya Wai yabar garin da yake shi ba mazauni bane a Abuja yanzu yake aiki.

Ranar mukayi girkinmu mai dadi har da nama mukasa a ciki muka hada zobo, ranar dai kamar masu party da yake Friday ce babu islamiyya haka da yamma muka zauna a tsakar gida mukayi ta hira muna dariya, inajin tunda su inna suka rasu bamu taba sakin jiki munyi wasa da dariya irin na yau ba.

ZulaihatuWhere stories live. Discover now