Chapter Eight

4 0 0
                                    

Wani tunani na zauna inayi anya kuwa abinda mukayi mun kyauta? Idan iyayenmu sun gujemu mu ya kamata mu gujesu? sune iyayenmu Kuma gaba suke damu beside sanda zasu tafinnan ma mu mukayi musu rashin kunya a ganina kamata yayi mu bisu har gidajensu mu Kai musu ziyara mu gaishesu sannan mu basu hakurin waccan rashin kunyar da mukayi musu wai bahaushe yace hannunka baya taba rubewa ka yankeshi ka yar.

Dama an kusa albashi Dan haka nayi cancelling duk hidindimun dake kan salary din nawa duk da dama ba yawane dashiba amma nasan zai ishemu muyi kudin mota, muna zaune muna hirar dare kamar yadda muka saba nace "Ni kuwa kunsan abinda nake tunani?" Duk sukace sai kin fada na cigaba "ya kamata mu kaiwa su baba lawan ziyara" Batul ta yamutsa fuska tace "waye ma baba lawan? Kamar na tabajin sunan" sauran suka saka dariya, amma Ni abinda tayin bai bani dariyaba bai kuma sagarmin da jiki naji cewar na fasaba.

Na hade rai nace "zamaki sanshine ubankine dolenki" tace "Kinga Yaya Dan Allah karki nemi ki jawo mana abinda zaazo ana zaginmu haka kurum, kina ganin irin sallamar da sukayi mana kwana uku da rasuwar iyayenmu sannan tun daga lokacin basu sake ziyartarmuba watanni hudu kenan to me zamuyi musu mu Kuma?" Na gyara zama yadda zan fi ganin fuskokinsu gaba daya nace "da farko akwai hadisin manzon Allah SAW da yake cewa (Wanda zaije azo masa bashine mai zumunci ba wanda aka yanke zumunta dashi amma shi yaje shine mai sadar da zumunci) kinga hakan yana nufin idan mukace sai sunzo mana sannan zamuje musu ko sai sun tuna damu sa'annan zamu tuna dasu ashe bamu da zumuncin da manzon Rahma ya fada kenan amma yanzu da suka yanke zumunci damu mu Kuma sai mu sadashi a garesu sai mu sami ladan hakan a wajen Allah.

Na biyu mu uku matane wata rana aure zamuyi duk kiyayyar da muke musu ko suke mana ba zamu taba iya aurar da kanmuba dole dai su zasu aurar damu dan haka yanzu idan mukace babumu babusu idan misali kika sami Wanda kikeso fa? wajen Muazzam zaki kawoshi?…" Ga mamakina sai cewa tayi "eh Mana Muazzam da Yaya Muslim sun isa su dauramin aure" na girgiza kai kamar zanyi kuka ganin duk ashe bama fahimtar bayanin nawa takeba nace "it doesn't work like that, Babu uban da zai yadda dansa ya aureki indai baki da dangin uba Muazzam da Muslim ba dangin uba bane" ta dan mirgina kai tana kunkuni ni kuma na cigaba "a unguwarnan ansan uwarmu ansan ubanmu amma daga rasuwarsu aka fara kiranmu da masu zaman kansu ana gudunmu anayi mana sharri kala kala ina ga mun tabbata masu zaman kan namu? Amma at least idan muka zawosu jikinmu idan suna Dan zuwa za'a fi respecting dinmu, na uku asali lokacin da zasu tafi mu mukayi musu rashin  kunya kunga kuwa ba zasuso sake dawowaba tunda zasuga idan sun dawoma rashin kunyar zamu sakeyi musu shiyasa sukaja girmansu.

Mu kanmu zamuji dadi ace yau mun tafi ziyarar danginmu kun tuna baba har ya rasu gashi dai shine marar karfi a ciki shine marar lafiya amma still kullum yana hanyar Kai musu ziyara saboda yasan su dolensane Dan haka muma dolenmune su Kuma na tabbata da baba zai dawo ya tarar mun watsar da Yan uwansa ba karamin bakin ciki zaiyiba idan kuwa yazo ya tarar muna zumunci dasu Koda su sun wulakantamu zaiyi farin ciki ba dan kadanba kun gane?" Jikinsu a sanyaye suka daga kai nayi murmushi sosai Dan naji dadi da suka fahimceni nace "yauwa Allah yayi muku albarka" suka amsa da ameen suna dariya Ni Kuma na cigaba da cewa "kunga dama gobe nake sakaran za'a bani salary na sai mu sami kudin motar zuwa har Kano zamuje" Al'ameen ya fara murna Saudatu tace "Yaya har da Muazzam?" Nace "indai zashi harshi zamu tafi"

Muna haka Muslim yayi sallama muka amsa sannan ya shigo ya samu waje ya zauna ka kallemu sai yayi murmushi yace "ya dai naga kamar Kuna dariya wace wainar kuke toyawane?" Al'ameen da murnarsa yace "Kano zamuje" Muslim yace "Kano Kuma? Wajen wa?" Nace "goggo hafsa Amma dai yanzu zamu fara zuwa gida dubune wajen baba lawan" da mamaki yace "me zakuyi musu? Me kuke bukata? Dan Allah karkuje zasu wulakantaku" jin zai ciremin liki nayi sauri nace "noo ba abinda muke bukata ziyara kawai zamu kai musu dan mu sami lada kuma na tabbata ba zasu wulakantamu ba tunda ba nema mukaje ba" yace "amma…" nayi saurin tarar numfashinsa nace "Babu abinda zai faru inshallahu" yace "ai shikenan yaushe zakuje?" Nace "sai an bani salary tukunna zamuje gidan baba lawan mu kwana biyu sannan muje kanoma mu kwana biyu" gaba dayansu sukace "au harda kwana?" Na kallesu daya bayan daya nace "eh mana kunsan dai baba lawan bazai dawo da wuriba dole mu kwana idan munason ganinsa ba Kuma zamu iya zuwa Kano mu dawo a ranar ba" Yaya Muslim yace "sau nawa ake zuwa kanon a dawo a ranar nan dai da Kano?" Nace "kudai kawai ku barshi zamu kwana bibbiyu"

Muazzam bai dawo gida da wuriba har muka gama hirarmu muka kwanta bacci Dan haka washe gari sai da ya gama baccinsa na safe ya fito sannan nake gaya masa, direct yace "bazaniba Kuma da zan iya hanaku da nace bazakujeba" nace "haba Muazzam…" ya dagamin hannu "bafa zaniba kuma wallahi duk abinda akayi muku karkuzo kunayimin kuka kunji na gaya muku Allah ya kiyaye hanya" Dole naja bakina nayi shiru.

A satin kuwa aka bani salaryn ranar da akayi hutu Dan haka washe gari asabar muka hada kaya tun da wuri sai gida dubu gidan baba lawan, muna zuwa da kyar muka gane gidan muka shiga da sallamarmu baki har kunne, matan baba lawan biyu da 'yaya kusan gomasha dan ni bama zan iya tantance 'yayan nasaba na dai san manyan, matannasa duk su biyun suna tsakar gida daya na wanki daya najan ruwa a rijiya da alama girki takeyi, suka amsa mana sai karamar wadda ke jan ruwan ta saki fuska tana cewa "ahh lale maraba da mutanen takur Koda yake kamata yayi na hade rai sai yau?" Mudai mukayi dariya amma dayar wato uwar gidan ko kala batace manaba ta wani hadw rai.

Goggo karama ta kira yaronta dake wasa a gefe tace "Bello maza je daki ka dauko musu tabarma su zauna sannunku da zuwa" mukace "yauwa sannu goggo" yaron yaje ya dauko mana katuwar tabarma a dakinta ya kawo mana na karba na shimfida a gindin bishiyar tsakar gidan muka zazzauna, ita Kuma ta fito daga kitchen tazo da kujerarta yar tsugunno ta zauna tana cewa "lalenku barka da zuwa" duk muka hada baki wajen gaisheta ta amsa fuska a sake tana kama sunayenmu tare da tambayarmu yadda muke muka amsa mata sannan na juya wajen goggo babba nace "goggo Ina wuni?" Bata ko kalleniba sai da goggo karama tace "Yaya ana gaisheki" sannan ta juyo "au ashe sunsan Ina wajen na zata basa iya ganina ai lafiya" Saudatu ma tace "goggo Ina wuni?" Itama ta bata amsa da lafiya Batul matso tace "gogg…"sai ta katseta "Kai da  Allah ni banason gaisuwa sai kace wasu maroka ko almajirai duka lafiya na yafe" Batul ta shaka ni kaina har tsorata nayi da tayi tsawar.

Mukayi shri gaba dayanmu can sai goggo karama tace "Ina Muazzam shi ba'a taho dashiba?" Nace "wallahi kuwa kinsan shi yayi girma da yawa" tace "Allah sarki gashi kuma baban naku yana kasuwa amma ai kunanan anan zaku kwana ko?" Nace "eh munanan" tace "yauwa bari na karasa girki" daganan ta koma kan girkinta sai dai lokaci zuwa lokaci idan ta fito ta danyi mana magana wani lokacin tambaya akan karatunmu ko yadda muke coping da dai sauransu amma goggo babba dake wajen kala bata Kuma ce damuba.

Sanda ta gama girki ta zubo mana mukaci anan da akayi sallah ma mukayi alwala mukayi sallah a wajen muka cigaba da zama haka dai har bayan magriba. Anayin sallar magriba tace mu dawo daki waje da sauro haka muka koma ciki can bayan isha sai ga baba lawan ya dawo tun daga waje yake masifa anyi wannan baayi wancan ba.

Yana shigowa ya dago labulen dakin Yan cewa "takalma su waye wannan?" Sai kuma ya tsaya yana kare mana kallo daya bayan daya, duk muka gaisheshi ya amsa ba yabo ba fallasa yace "lafiya dai ko?" Na amsa "lagiya kalau baba dama zuwa mukayi mu gaisheku tunda anyi hutu" yace "to sannunku ai da har na zata wani aikin kuka daukomin nima ina fama da kaina" duk mukayi shiru har ya juya zai fita sai kuma ya waigo "Ina fatan dai ba anan zaku kwanaba ko? Dan naga dare yayi Amma baku da niyar tafiya" muka kalli juna ni da kannena sannan nace "eh dama baba anan zamu kwana biyu…" ya katseni "kwana biyu? Aa na gode madallah maza ku kama hanya ku gaida gida" goggo karama tace "ayya baban bello da ka barsu ko zuwa da safene tunda yanzu dare yayi gasu duk mata" yace "idan na barsu ke zaki basu abinda zasuci da safe? Dan ban shirya ciyar dasuba" tace "naji zan basu amma ai bai kamata a darennan su tafiba gashi da yar tazara" yace "ke Kuma kikasan wannan indai zaki ciyar dasu kuje kuyi tayi" ya kada takalmansa yayi waje.

Kaina a kasa wani hawaye mai zafi ya zubo sai nayi na goge kafin ya uwana su gani nace "goggo dama kin bari mun tafi yanzun ai dare bai gamayiba " tace "nace sai gobe zaku tafi kuyi hakuri Allah ya kaimu da safen sai ku tafi" nace "Allah ya kaimu" ta amsa da "ameen".

*************
Hi guys
Kuyi hakuri da wannan anjima zan posting wani inshAllahu.

Zulaihatu littafin siyarwane wadda take bukatarsa zata iya biyan kudinsa N200 kacal ta banki
Acc name: Aisha Usman Tafida
Acc no: 0007887305 jaiz Bank
Ko katin MTN zuwa wannan number 0906 122 3180 sai a turo shaidar biya ta number din sama via WhatsApp.

Saura page 2 mu gama free dan haka maiso sai yayi kokarin biya dan gudun katsewar labarin, Ina mai tabbatar muku ba'a fara komaiba.

Thank you

ZulaihatuWhere stories live. Discover now