Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F5ppyca606H1wzCJoowSXv
*BUSHRA*
_By_
*REAL ESHAA**Elegant Online Writers*
*JAN HANKALI*
_Dan girman Allah 'yar uwa idan kinsan zaki karanta ta littafi na dan ki kirani awaya ki zageni ko kuma ki tura min sa'kon zagi ta Inbox kar ma ki soma karanta min book da bazan juri irin zagin cin mutunci da kuka min acikin KISHIYA KO BAIWA ba dan banga abinda na rubuta Wanda be dace ba dana cancanci zagi kun kirani da sunayen daku kaga dama kunce min jahila kunce ina rubutu akan cin zarafin mata kamar ni ba mace bace ko kuma bansan darajar mace ba na ha'da ku da girman Allah kada wacce ta kirani ko kuma ta tura min sa'kon dabe daceba domin KISHIYA KO BAIWA labarin gaskiya na hasalima na rage wasu abubuwan dake ciki anma Duk da haka ban tsira ba._
*PAGE 1&2* 🖊
__________📖Litinin ce mai zafi a gurin Alhaji Aliyu da Matar sa Hajiya Asma'u, kallo ɗaya zakai masu a lokacin da suka 'kura ma bango idanu suna tunani, a take zuciyar ka zata tabbatar da suna cikin rububi da sanin mece ce makomar su takarshe a rayuwar duniya...
A 'kalla wannan ita ce asibiti ta goma da suka je domin tabbatar masu da sakamakon gwajin da ake masu na lafiyar su, amma duk sakamakon ɗaya yake zuwa,a yanzu da suke zaune a a sibitin Dr Usman dake Garin Kaduna.Babban likitan da yakware wajen bada maganin haihuwa, babu abinda suke fata, sai samun saɓani akan abinda sauran likitocin garin su suke faɗa masu.Shigowa Dr yayi 'dauke da file guda biyu a hannunsa zama yayi a kujeran zaman sa ya zuba musu idanu Wanda yana Iya hango tsantsar tashin hankalin dake akan fuskarsu,gyaran murya yayi sannan yafara da yimusu nasiya,Kamar haka.
Ha'ki'ka bawa baya kaucewa kaddararsa,Allah shiyake tsarawa bawan sa abinda yafi zama alkhairi agaresa,kusani yadda da 'kaddara me kyau ko mara kyau yazama wajibi ga duk kan mumini,domin idan Allah yajarabce ka kagode masa seya musanya maka da mafificin alkhairi wanda bakayi zato ba.Nasani rashin haihuwa Abune me ciwon gaske ga duk wanda Allah ya jarabce sa,saboda 'ya'ya rahma ne ga iyayen su,anma ku haka taku 'kaddaran yakasance,saka mokon gwajin yanuna lafiyar ku 'kalau babu wanda ke da matsala sede lokaci ne da Allah be kawo ba kuyi,ha'kuri Ku kuma jure se Allah ya Baku ladan hakurin da juriya.
Domin ba'a yanke 'kauna da rahmar Ubangiji dan shine metsara yanda yaso akan bayin sa,kuma seya baku haihuwar asanda yaga dama.Sosai Dr Usman yayi musu nasiyya me ratsa jiki har yaga alamar tqsirin sa.Numfasa wa Alhaji Aliyu yayi yace"Ha'ki'ka bamu daja akan lamarin Ubangiji mu domin shike tsara mana abinda yafi zama alkhairi agaremu tabbas duk abinda ya jarabce mu dashi ya zama dole mu amshe sa hannu bibbiyu.Nagode da tunanar damu abinda muka manta Dr.Hannu Alhaji Aliyu yasake mi'kawa Dr suka sake Musabaha kafin yami'ke ri'ke da hannun Hajiya Asma'u da tunda aka fara magana bata ce komai ba.Sallama suka yiwa Dr kafin sufice su tafi,da kallo Dr Usman yabisu cike da tausayin su ha'ki'ka da yanada wani temako daze Iya yi musu da yatemake su sede kash!!,shima bashida halin temaka musu a wannan 'bangaren saboda lamari ne na Ubangiji....
Direct mota suka shiga yai mata key tafiya suke babu mecewa da 'dan uwansa komai saboda tsantsar damuwar dake damun zuciyoyin su.Ahankali ya lumshe idanunsa ha'ki'ka yayi imani da Allah da mala'ikun sa da littafin sa da kuma manzan ninsa toh hakan yazar masa dole ya yadda da kaddaran sa aduk yanda yazo masa.Sunyi nisa da tafiya sosai motar ta tsaya,Key yayi anma ta'ki tashi kallon sa ya mayar kan Hajiya Asma'u da niyyar yi mata magana seya ga, da alama bata Masan sun tsaya ba ganin yanda ta 'kurawa waje 'daya Idanu...Cike da tausayin ta ya zuba mata ido yana jin tausayin ta na ratsa dukkan ilahirin jikinsa Ahankali ya furta ya Allah kada ka jarabce mu da abinda baza mu iyaba...Ahankali ta juya jin shirun yayi yawa kallon sa tayi taga sun tsaya, juyawa tayi taga ajeji suke da sauri ta sake kallon sa cikin sanyin murya tace"Lafiya me muka tsaya yi anan??, tayi tambayar tana me kafesa da idanunta...
Cikin raunin murya yace"kiyi ha'kuri Asma'u nasan...da sauri ta 'daura hannun ta a bakin sa tana girgiza kai tace"Dan Allah bansan wata magana kabari!!,tana ida maganan tayi saurin bu'de marfin motan ta fita batare data jira jin abinda ze ce ba.Tana kallon motar tace"barin duba mana dan naga da alama matsala tasamu".Da kallo ya bita yana jin 'kaunar ta na sake ratsa sa kasancewar ta mace me ha'kuri shi kam yagode wa Allah daya basa Asma'u amatsayin matar Auren sa....
Fitowa yayi yasa meta tsaye agaban motar ta bu'de tana duba wa, Murmushi ya mata sannan yafara duba wa,dafe kai yayi tare da fa'din" ya salam. meyafa ru??,ta tambaye sa,"Kinga mun manta bamu 'dauki ruwa ba gashi lagrato na bu'katar tar ruwa"ya fa'da cike da damuwa.Itama shiru tayi tana tunanin ina zasu samu ruwa a jeji babu gida ko shago a kusa." kallon ta yayu yace" kijira ni barin samo mana ruwa.Da sauri tace"Zan bika"Ok ya amsa sannan suka sau'ka daga titin suka gangara cikin jejin.Sunyi nisa da tafiyar suka hango wani 'dan rami daya tara ruwa anma bashi da haske,da sauri suka karasa wajen.
Goran Swan ya hango,'karasawa yayi ya 'dauka,Ya 'debo ruwan kenan yaji kaman kuka daga 'kar'kashin wata bishiyar mangoro dake da duhu,A nutse ya juya dan tabbatar wa da kunnun wan sa aikuwa kukan ne kuma akusa dasu suke jiyo wa.A tsorace Hajiya Asma'u ta 'karaso kusa dashi hannun sa ri'ke da 'karfi acikin nata,Dan Allah mubar wajen nan ka jifa kuka nake jiyowa,kuma kukan se sake tsananta yakeyi...Al ajabine yacika Alhaji Aliyu,cikin dakiya ya nufi wajen da yaji kukan yafi 'karfi.Tir jewa Hajiya Asma'u tayi tana girgiza kai tace"ni bazan je ba.Kizo mugani ya fa'da ahankali,Ba dan ranta ya soba tabi bayan sa,Cak suka tsaya batare da sun 'karasaba suna ganin ikon Allah....
Karfin halin 'karasawa yayi da addu'a 'dauke a bakin sa ya tsugunna yana kallon abinda ke gaban sa,ita kam tsoro da far gabane suka shiga cikin zuciyar ta, se addu'o'i take jerowa sannu ahankali taji duk wani tsoro da fargaba sun fara fita akanta sema wani tausayi da imani dake ratsa mata zuciya.Ahankali Alhaji Aliyu ya 'dago jaririn daya gani acikin wani jememen tsimman,Ido ya'kura mai sannan yasa 'dayan hannu sa ya 'daga tsimman yaga Ashe macece Allahu Akbar ya furta"yana Mi'kewa da sauri Hajiya Asma'u ta 'karaso wajen tasa hannu takar be'ta batare da 'kyan'kyami ba ido ta kura mata tana jin wani tausayin ta na ratsa duk kan ilahirin jikinta..
Dafa ka fa'darta yayi yace" kinga ikon Allah ko? kinga Allah me kyau ta da hana wa??kinga ribar ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara ko??.Murmushi tayi tana jin wani irin nutsuwa da kuma farin ciki yana ratsa duk kan ilahirin jikinta,Alhamdulillah Allah nagode ma ta'fada tsananin farin ciki.Hannu ta ya ri'ke suka koma wajen motar,'dan kwalin kanta ta cire ta nanna'de jaririyar aciki sannan ta jefa je mamman tsimman acikin,shiga Motar tayi shima yashiga."Se murmushi suke jifan junan su da shi suna jin farin ciki;baza ka ta'ba cewa sune suke cikin tashin hankali da kuma damuwa ba na tsawon lokaci....
Tafiya suke cike da farin ciki, sai hira suke yanda zasu fara tsara sabon rayuwarsu da kuma ta 'yarsu ,ahaka har suka 'karaso gida hong yayi a'kofan wani katafaren gida,gate me gadi ya bu'de masa yashiga direct part din Hajiyar sa suka nufa cike da farin chiki mara misaltuwa,da sallama abakin su suka shiga zaune suka same su sun hakimce akan kujeru suna fira da alama suna jin da'din firar tasu ,juyowa sukayi tare da zuba musu ido da sauri suka mike suna ji fansu da kallon mamaki da kuma tuhuma.
Jikin su ne yayi sanyi ganin irin kallon da mahaifiyar sa da kuma kanin sa ke jifansa dashi"Aliko me wannan ahannun Ma'u cewar Hajiya ta'fada tana tsaresu da ido kana tana bin su da mugun kallo....'''Ga masu bu'katar complete documents din KI YADDA DANI 400 hundred ne se sututo da katin mtn ta wannan number 09068403802 ko kuma ta account 'dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548....'''
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah ka gafar ta masa zunuban sa ya Allah ka kai haske kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya....*
*ESHAA CE ~*🤙🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/285047293-288-k146083.jpg)