Page 01

342 4 0
                                    

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎

                 👑👑
                    🦋
               🦅🕊🦆
             🐍🎠🐄🏹
                       

  _*NA*_


UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


*INA KUKE MASOYAN LITTATAFAI NA, YAU DAI ALLAH YAYI ZAN FARA KAWO MUKU LITTAFIN DA KUKA DAƊE KUNA JIRA TARE DA TSAMMANIN GANIN SA TSAWON SHEkARA ƊAYA HAR DA WATA HUƊU YANZU, FATAN ZAKU BANI HAƊIN KAI, SANNAN KUMA ZAKU NUNA MUN ZALLAR SOYAYYAR DA KUKE IƘIRARIN KUNA YIWA LABARAINA TA HANYAR SIYAN WANNAN ƘAYATACCEN LABARIN.*

*BAƘAR MASAURATA YASHA BAMBAN DA SAURAN LABARAN, LABARI NE IRIN WANDA BAKU TAƁA CIKIN KARO DA KALAR SABA.*

*DUK ABUN DA ZAKU GANI ACIKIN LABARIN NAN ƘIR-ƘIRARRA NE, KAMA DAGA SUNAYEN GARURUWA HAR IZUWA NA MASARAUTU, KAMAR YACCE DUKA LABARIN YA KASAN CE ƘIR-ƘIRARRE.*

*BAN YARDA WANI KO WATA BA SU JUYAMUN LABARI TA KOWACE SIGA BA TARE DA IZININA BA.*

*FREE PAGE 01*

_SHIMFIƊA_

*ƘASAR HAUSA*

Ƙasa ce mai tsantsar girma da faɗi, ƙasace wacce Allah ya azurta ta da mayawaitan al'umma, maban-ban ta ƙabilu da mazaunai daban daban, ƙasa ce mai ɗauke da jahohi 30 cif acikin ta, yayin da jahohin suka kasan ce ayanku na daban daban, ƙasa ce wacce ta kasan ce ƙasar hausawa, duk da dai basu kaɗai bane suka kasan ce acikin ta, sai dai kuma mafi yawan jahohin da suke acikin ƙasar yawan cin su duka na hausawa da fulani ne, wato dai sune masu ƙasar.

*MASARAUTAR WASAI*

Ɗaya daga cikin manyan masarautun da suke aƙarƙashin ƙasar hausa kenan.

JAHAR WASAI
Jahace mai matuƙar girma da faɗi, jahace wacce take ɗaya daga cikin manya-manyan jahohin da suke a ƙar-ƙashin ƙasar hausa, jaha ce ta musulunci da musulmai, jaha ce wacce take da manyan ƴan kasuwa tare da manyan kasuwani acikin ta, domin ko itace ta kasan ce cibiyar kasuwan ci ta ƙasar hausa. Yayin da ita kuma masauratar wasai ta kasan ce ɗaya daga cikin manya manyan masarautun da suke acikin ƙasar hausa, sannan kuma ta kasan ce masarauta ɗaya acikin jahar wasai, wato dai itace mamallakiyar jahar gaba ɗaya.

Masarautar wasai masarauta ce mai tsantsar girma da ƙarfin mulki, masarauta ce wacce ta kafa tarihi acikin ƙasar hausa, masaurata ce mai ƙarfin mulki wacce ake ji da ita aduk faɗin ƙasar hausa harma da ƙasashen da suke maƙota ka da ƙasar.

***
*JAHAR KAGUL*

Itama dai jahar kagul ta kasan ce dlɗaya daga cikin manyan jahohi ne da suke aƙasar hausa, sai dai ita kuma jahar kagul tana ayankin yammacin ƙasar hausa ne, saɓanin jarah wasai da take a arewacin ƙasar hausa.
Jahar kagul ta kasan ce jahar fulani ce ita, wato dai kusan duk mazaunan cikin ta sun kasan ce fulani makiyaya ne, sai dai ita kuma ta kasan ce ɗaya daga cikin jahohin da addinin musulunci baiyi zurfi acikin ta ba, domin kuwa mafiya yawan mazaunan cikin ƙasar ko karatun sallah basu iya ba bare aje ga sanin tauhidi da hadisai, kai ataƙaice ma dai sallahr duka bata dame su ba, domin ko hatta da gidan sarautar dake cikin ƙasar shima babu addinin acikin sa, dan kuwa babu abun da suka sanya agaba sai tsafi da harkar kula da dabbobin su, kasan cewar itace babbar jahar kiwo aƙasar hausa, domin kuwa kusan duk wasu shanu da ake kadawa acikin jahohi talatin da suke aƙasar hausa suna futowa ne daga jahar kagul.
Hakan yasa ɗaukacin mutanen dake cikin jahar suka maida hankulan su akan kiwo da asirce asricen da zasu bawa dabbobin su kariya fiye da komai agidan duniya, ciki kuwa har da addinin su, wato dai in taƙaice muku zance jahar kagul itace cibiyar kiwo ta ƙasar hausa.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now