Page 16

25 0 0
                                    

*BAƘAR MASARAUTA*

            *NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 16*

Wani irin ihu su Sarki Barbaru suka saki cikin tsantsar farinciki suna masu ɗaga hannuwansu sama, tare da faɗin.
"Gargabilu! Gargabilu!! Gargabilu!!!"
Sabo da yadda suka ga gaba ɗaya kaskon nan ya dare gida biyu, kana wutar cikinsa ta mace tas, kamar yadda boka ya faɗa, yayin da su kuma mutanen dake cikin jirgin nan suka sake fashewa da kuka mai sosa rai, shi ko Ishaƙ banda faman girgiza Aishatu yana kiran sunan ta, bayan ya watsa mata ruwa a fuska babu abun da yake iya yi.
Wani irin kuka yake jikinsa na tsantsar rawa tamkar ƙaramin yaro.

Sarki Barbaru da kansa ya durƙusa a ƙasa, yana mai ɗaukar jaririn dake ta aikin tsala kuka har yanzu a hannun sa, tukun ya buɗe baki cikin muryar sa mai futar da amon sauti, yana mai kallon dakarun sa tare da faɗin. "Ai'ki kuma ya ƙare daga yau, domin ko Ubangiji Gargabilu ya yaye mana wahala, ya aiko mana da mafutar mu, yanzu rayuwar mu zata dawo kyakkyawa ba tare da fargabar komai ba, tamkar yadda muka kasance ada, dan haka ku koremun waƴan nan mutanen, tare da jirgin su gaba ɗaya daga cikin ƙasa ta."
Sarki Barbaru ya faɗa yana mai nuna Jirgin su Aishatu.
Tukun ya juya ɗauke da Ɗan a hannun sa.

Da wata irin gigitattar ƙara Aishatu ta farka da ita tana mai faɗin. "Ɗana! Ɗana!! Ɗana!!! Kuyi haƙuri! Kuyi haƙuri karku kashemun shi, kuyi haƙuri kubani shi ko ɗaukar sa ne nayi, kumun afuwa kubarni inji ɗumin sa yaji ɗumin jiki na shima, kumun gafara ku barni nayi rayuwa da jinjiri na!" Ta faɗa a wani irin haukace tana mai funcike jikin ta daga riƙon da Ishaƙ yayi mata ta sake yin bakin Jirgin aguje tana shirin fucewa, sabo da yadda ta hango Sarki Barbaru ya juya yana tafiya riƙe da jinjirin nata, ga kuma yadda kukan jaririn ke dukan dodon kunnuwan ta.

Da sauri wani Badakare da yake abakin hanyar yasan ya hannun sa yana mai hankaɗata baya ta faɗi ƙasa.
Tukun suka ƙara zare mahaukatan makaman su suna masu saitawa direbobin jirgin hanya, tare da basu umarnin suyi gaggawar yin gaba tun kafin su canza shawara duka suka kashe su suma.
Jin hakan da matuƙan Jirgin nan sukayi kuwa ba ƙaramun sake hatsina musu ƙwaƙwalwa yayi ba, domin kuwa sun tabbatar da babu abun da mutanen nan zasu ce zasuyi sa suka sa yin sa, hakan yasa cikin gaggawa ko wanne ya koma wurin sa, tukun suka sake yin gaba suna masu ɗaukar hanyar su, yayin da suma mutanen Baƙar Masaruta suka ƙara shigewa cikin jirgin su suna masu binsu abaya domin suyi musu rakiya.

Tunda wannan Badakaran ya sake hankaɗa Aishatu ta faɗi a ƙasa, sai Ishaƙ ya sake zuwa ya riƙe ta gam, irin riƙon da bazata taɓa iya ƙwatar kanta ba, domin kuwa ya sani muddin zata cigaba da haka to Ba ƙaramun aikin su bane su kashe ta duka itama.
Sosai take kuka na tashin hankali mai tsanin ban tausayi daga kwancen da take acikin jirgi, banda raɗaɗi da suya babu abun da take jin zuciyar na nayi mata, tayi nadamar zuwan ta Jahar Ruman gaisuwar mahaifin ta tafi sau dubu, taji inama ace tabi maganar mijin nata tayi haƙuri tabar zuwan, tabbas da tasan babu wani abu wanda zai rabata da Ɗan ta a lokacin da ta haife sa.

Sosai take hango kamannin yaron a cikin idanuwan ta, sabo da yarce suka zauna mata a cikin idanuwan nata das, wato kamannin ta kenan sak kamar yacce ta gani akan fuskar jinjirin.

Sai da har suka rakasu ƙofar futa daga cikin Ɓakar Masarauta duka, tukun suka juyo da kan nasu Jirgin hankulan su akwance babu damuwar komai tattare da su, yayin da su kuma mutanen cikin Jirgin su Aishatu suka sake fashewa da wani irin azababben kuka, musamman  ma waƴan da aka ƙwacewa Ƴaƴa, suna masu kallon hanyar garin, hanyar da suka raɗa mata suna Bakar Hanya, kamar yacce suka raɗawa wannan rana ta Alhamis suna Baƙar Rana, mai tsantsar muni da ƙuna a cikin rayuwar su.

Acan ɓangaren su Sarki Barbaru kuwa kai tsaye suka doshi ɓangaren bayi.
Tafe suke suna masu furta sunan Gargabilu da matuƙar ƙarfi, yayin da jinjirin nan kuma yake ta cigaba da sakin kuka, har lokacin kuma Sarki Barbaru bai ajiye sa ba.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now