Page 8

24 0 0
                                    

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
                 👑👑
                    🦋
               🦅🕊🦆
             🐍🎠🐄🏹
                       

  _*NA*_


UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

*FREE PAGE 08*

_DAN ALLAH INA CIGIYAR WATA BAIWAR ALLAH MAI SUNA HAMIDA HUSSAINI, ƊAYA DAGA CIKIN  MUTANEN DA SUKA BIYA KUƊIN SU WAƳAN DA AKE BAWA TA PC, PLS IDAN KINGA WANNAN PAGE ƊIN KIMUN MAGANA NA SAKE SEVER NMBR KI, NA RASA WACCEN NE TA SANADIN EMAIL ƊINA DA YASAMU MATSALA, KUMA AKANSA NAYI SAVING ƊIN TA._

"So nake abi masa ta hanyar da bai taɓa zato ba Dad, ma'ana kawai ka samu iyayen sa kayi musu magana akan auren mu, nasan idan akayi hakan dole ya dena mun hulaƙacin da yake yi mun, kamar yacce nasan babu tayarce za'ai mahaifin sa yaƙi yin komai kace yayi." Ta faɗa tana mai kallin baban nata, yayin da shi kuma yayi shiru ba tare da yace komai ba, sai kansa da ya ɗaga sama yana mai kallon haɗaɗɗen rufun dake cikin ɗakin, tukun daga bisani ya sauke kan nasa ƙasa yana mai watsa ƙwayar idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Tabbas na gamsu da zancen ki ɗari bisa ɗari my Daughter, Dan haka ayau yau ɗin nan zan turawa mahafin nasa da saƙon zuwa na gare sa, domin kuwa agobe-goben nan nake son ayi duk mai yuhuwa, sannan kuma aƙarshe in faɗawa mahaifin sa aja masa kunne, sabo da ya kiyaye kar bayan anyi aure ya cigaba da abun da yake yi yanzu." Ya faɗa still idanuwan sa akan fuskar ƴar tasa.
Yayin da ita kuma tayi wata irin miƙewa tana mai matawa kusa da shi, tukun tayi hugging ɗin sa daga zaunen da yake da matuƙar ƙarfi tana mai faɗin. "Yess my Dad, that's why akullum nake ƙara son ka, sabo da kaima kana son abun da nake so." Ta ƙarasa maganar da sakar masa kiss akan goshin sa, tukun ta juya aguje tana mai kama hanyar stair's cikin tsantsar farin ciki.
Yayin da shi kuma mahaifin nata ya bita da idanuwa fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi shima.

*WASHEGARI*

ƘASAR MALIN, JAHAR KARFUZ CIKIN BAƘAR MASARAUTA.

Tun daga bakin tafkeken ruwan da yayiwa jahar karfuz ƙawanya mutum zai fahimci yau ɗin ana wani gagarumin taro ne acikin sa basai an faɗa masa ba, sabo da yarce jama'a na garuruwa daban- daban suke ta shigowa suna wucewa, wasu akan dokuna, yayin da wasu kuma suke akan ƙafafuwan su, ga kuma yarce akabi aka zagye gefen ruwan da yake abakin garin, wanda dole sai mutum ya tsallake sa kafin ya shiga jahar karfuz da wuta acikin kaskwaye tanaci bal-bal-bal!

Acan cikin Baƙar  Masarauta kuwa ban da sautin kiɗa babu abun da akeji yana tashi, domin kuwa tun cikin dare aka gama shirya filin biki tas, sannan kuma aka zageye sa da kayan kiɗa masu matuƙar sauti, tare da kaskwayen Huta waƴan da suke ɗauke da iccina suna ci acikin su.
Yayin da daga can gefen filin kuma wani tamfatsetsen farin ruwa mai wucewa yake.

Sosai aka ƙawata wurin da ado kala-kala, yayin da tambarin masarautar tasu kuma ya kasance manne akowane wuri, acan ƙarshen filin kuwa daga jikin bango wata irin haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujerar ƙarfe ce aka jere awurin, yayin da gefe da gefen ta kuma aka aje wasu ƙananan kujerun masu azababben kyau suma na ƙarfe masu dauke da tambarin baƙar masarauta ajikin su, yayin da tsakiyar filin kuwa aka ƙawata sa fiye da yarce aka ƙawata ko wane wuri.

Wani tafkeken daɓe (floor) ne akayi awuri mai matuƙar tudu da tsairs ajikin sa, gaba ɗayan sa zage yake da randinan da suke ɗauke da Huta acikin su suna matuƙar ci sosai, yayin da saman daɓen kuma aka ajiye wani danƙareran gunkin da akayi sa da taɓo da basa da kyan gani ko kaɗan, yayin da gefe da gefen sa kuma ya kasance ɗauke da fulawoyi zube aƙasa zageye da shi masu matuƙar yawa da wal-wali, sai kuma tambarin baƙar masarauta da aka bi aka manna sa aduka ƙasan daɓen.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now