Page 17

28 1 1
                                    

*BAƘAR MASARAUTA*

            *NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 17*

Sanye suke da ƴan guntayen baƙaƙen wandina na yadi iyakar guiwoyin su babu ko riguna a jikin su dukan su.
Riƙe Bir yake da kwari da gwafa a hannun sa yana mai gyara danƙon jikin ta, kasancewar tana ɗaya daga cikin abubuwan da yake matuƙar so a rayuwar sa.
Tun da ya taso yaga mayaƙan Baƙar Masarauta na amfani da ita, sai shima abar take matuƙar birge sa, hakan yasa ko da yasuhe da ya futo daga ɗakin su muddin suna nan yake hucewa wurin su yaje ya tsaya yay ta kallon su, wani lokacin ma har ya ɗauki abar ya fara shirin gwada harbawa shima, hakan da ɗaya daga cikin maharban nasu ya gani ne yasan ya sa haɗawa Bir wata ƴar ƙarama dai-dai da shi ya basa, a ranar kuwa ba ƙaramar murna da farin ciki yayi ba, sannan kuma wuni yay adaji yana harbin tsuntsaye, har sai da Iyar Bayi taje ta kamosa da kanta da taji shiru, domin ko ita ko kaɗan bata son harkar kwari da gwafar da Bir ɗin yake yi, sabo da tana tsoron kar wataran aga ya ƙware da harkar amayar da shi cikin Maharban Masarautar, sabo da idan hakan ta faru to rabin rayuwar sa zata ƙare ne a yawon dajika, sannan kuma koda wani faɗan ya taso to yana ɗaya daga cikin mutanen da za'a na turawa, hakan yasa take ƙin abar sosai, sai dai shi kuma Bir akullum ƙara ƙaunar kwari da gwafar sa yake.

Tun yana ɗan ƙaramin sa yake da wata irin halayya ta taurin kai da kafiya, domin kuwa muddin baiyi niyyar yin abuba to ko ance yayi bazai taɓa yin sa ba, ko da za'a dake sa ne kuwa, haka kuma dan an dake san a banza, sabo da baya kuka kwakwata, sai dai mutum yayi ya gama, wannan dalilin ne yasa Iyar Bayi take kiran sa da suna JARUMI, saboda yadda yake da tsantsar jarumtar a ɗan ƙaramin sa.

"Jarumi! Jarumi!!"

Muryar Iyar Bayi dake tawowa wurin da suke ta daki dodon kunnen Bir da yake shirin harba tsinken gwafar sa jikin bishiya.

Da sauri ya juya ɓarin da take yana mai kai dara-daran kyawawan idanuwan sa kan fuskar ta, tukun ya buɗe baki yana mai faɗin.
"Me ayi ne Iya yanju ma?"

"Wanka da cin abinci mana Jarumi, kaga su Mauzum tun ɗazu nayi musu wanka, gasu nan har sunzo kuna wasa tare, amma kai tun da kafuce tun safe kaƙi ka dawo kana nan kana shirme."
Iya Bayi ta faɗa tana mai ƙarasawa kusa da Bir ta riƙo hannun sa.
Yayin da shi kuma ya buɗe baki yana mai faɗin.
"To a ƙoshi Iya ta, idan a gama halbo cuncuna zanjo kimun wanka, she ki shoya mana shi mucinye ko."
Ya ƙarasa maganar yana mai sakar mata dariya, tayarce har sai da kyawawan jerarrun fararen haƙwaran da suke a bakin sa suka bayyana.

"A'a Bir bani gwafar nan haka, in yaso bayan na maka wankan kaci abinci sai kadawo ka cigaba da harbo sun, domin kuwa idan ba haka ba nasanka sai ka kai har dare a wurin nan ba tare da ka gama ba."
Iyar Bayi ta faɗa tana mai ƙwace kwari da gwafar da suke riƙe a hannun sa, sabo da sanin da tayi muddin ba amsar sun tayi ba to bazai taɓa binta ba.

Diddira ƙafafuwan sa ya farayi a wurin yana shirin sakin kuka, sabo da ƙwace masa da tayi.
Hakan da Iya ta gani ne yasan ya ta buɗe baki tana mai faɗin.
"Haba dai Jarumi da kuka, ka taimaka kar kabani kunya mana, kasa yau mutane suyi mana dariya."
Ta ƙarasa maganar tana mai jan hannun sa sukayi gaba.

Ba dan Bir yaso tafiya ba yabi Iyar Bayi suka tafi, yayin da suma abokansa su Mauzum suka biyo su a baya.

*ƘASAR HAUSA, JAHAR WASAI CIKIN MASARAUTAR WASAI.*

A yanzu haka shekarun Babban Yaya goma shahuɗu a duniya, sosai ya ƙara girma tare da nutsuwa da kuma hankali, wanda hakan kuma ba ƙaramun ƙona zuciyar magautan su yake ba, domin kuwa babu kalar asirin da basuyi masa ba amma duk a banza har yau yaƙi cin sa, sai dai kuma suma ɗin har kawo yau basu haƙura sun dena ba, kamar yacce har yau Fulani bata sare ba wurin yiwa Ƴaƴan nata addu'a, sannan kuma suma ta koya musu sukeyi da kansu.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now