Page 13

21 0 0
                                    

*BAƘAR MASARAUTA*

            *NA*
UMAR FARUQ*D*

*PAGE 13*

Boka mai wutar kasko ya futo daga cikin ɗakin sa amatuƙar ruɗe, yana mai kallon sama, ga kuma yarce garin ke sake rikiɗewa yana yin duhu.

Da matuƙar sauri ya dire daga kan dokin, yana mai yin wurin da ya hangi Boka mai hutar kasko.

"Shin meke shirin faruwa damu n ya kai Boka?" Sarki Barbaru ya watsowa Boka mai hutar kasko tambaya cikin kakkausar muryar sa, hankalin sa atsantsar tashe.
Yayin da Boka Barbaru kuma ya cigaba da juyi yana kallon sama, ba tare da ya kalli ko inda Sarki Barbaru yake ba, ballan tana ya tanka masa.

"Na roƙeƙa da abun bauta Gargabilu ka tsaya kai mun bayanin ta inda mafuta take." Sarki Barbaru ya sake faɗa adai dai lokacin da ya ƙaraso gaban Boka mai hutar kasko.

"Ni kai na bansan ta inda zan fara ba, domin kuwa lamarin yazo mun alokacin da ban tsammace sa ba, sabo da ko kaɗan abun bauta Gargabilu bai sanar mun da faruwar hakan ba, gashi kuma afahimta ta ta yanzu naga kamar garin ake shirin rusawa tare da jama'a..." Dakata Boka!" Sarki Barbaru ya katse sa da faɗin haka cikin tsawa, hankalin sa na sake bala'in tashi, tukun daga bisani ya fara ɗaga ƙafafuwan sa yana mai ƙara matsawa kusa da Boka mai hutar kasko, sannan ya buɗe baki yana mai faɗin. "Mafuta nake son ka samar mana Boka, ba wai bayanin abun da yake shirin faruwa damu ba, domin ko tun lokacin da wannan labarin ya iso kunnuwa na na fahimce cewar mun aikata babban laifin ne ga Ubangiji Gargabilu, shiya sa har yake shirin hukun tamu ta wannan hanyar, dan haka duk yanzu ba lokacin dogon jawabi bane, kamata yayi ace ko da na ɓullo wurin nan in hangeka agaban Huta da Ƙasa kana ƙoƙarin nemar mana afuwa ba anan ba." Ya ƙarasa maganar da sakin huci.
Yayin da Boka mai Hutar kasko kuma ya buɗe baki cikin zafi shima yana mai faɗin. "Haƙiƙa al'amarin ya huce duk yarce kake.zato, domin kuwa cikin duka abubuwan daka lissafo ayanzu babu ɗaya da ya rage banyi sa ba, amma duk basuyi aiki ba, sabo da ita kanta Hutar kasko Bama ta koma, tana futar da jan hayaƙi, wanda hakan ke nuni da cewar kamar wasu al'ummar ne daga wani yankin suke shirin kawo mana farmaki, wannan dalilin shine ya sanya kazo ka sameni awurin nan, sabo da in duba ne dan na gano ta yadda zan ɓullowa al'amarin!" Boka mai hutar kasko ya ƙarasa maganar yana mai kallon cikin idanuwan Sarki Barbaru.
Yayin da shi kuma ya juya yana mai kaiwa iska naushi, tare da faxin. "Kai, kai, kai inaaa! Hakan ba zata taɓa faru dani ba wallahi." Ya faɗa da ƙarfi yana mai juyawa ya fara taku daga inda yake zuwa gaba cikin tsantsar sauri, tukun daga bisani kuma ya sake juyowa ahaukace yana mai dawowa gaban Boka Gargabilu, kana daga bisani ya buɗe baki yana mai faɗin. "To yanzu meye mafuta kenan Boka?"

"Zan koma ciki a yanzu domin nayi ƙoƙarin ganin mun sadu da ubangiji Gargabilu ayanzu-yanzu, duk da yau ɗin bata kasance ranar saduwar mu ba, amma sai dai kuma babu yarce zamuyi dole zanje nabi wata hanya, domin ganin na sadu da shi, sabo da ya samar mana da mafuta."

"To muje mana kawai kafara Boka, domin kuwa na sani ubangiji Gargabilu bazai taɓa barin mu mutaɓe ba, sabo da mun kasance masu ƙoƙarin yin duk wani abu da ya sanya mu muyi." Sarki Barbaru ya faɗa yana mai bin bayan Boka mai hutar kasko da yayi gaba.

Ɗakin iccina ne mai ɗan girma dai dai misali, zagaye yake da bakin ƙyalle wanda aka buga tambarim Baƙar Masarauta tako ina na jikin sa da farin fenti, ga kuma kaskwayen wuta da suke ajiye a kowace kusurwa ta cikin ɗakin suna ci da huta, sai kuma wasu uban kayan kari-kitai kala kala marasa kyan gani da suke ako wane wuri dake cikin ɗakin.
Yayin da daga can jikin bango kuma akayi wani ƙaton daɓe mai matuƙar tudu, domin kuwa harda matattakalar hawa manne ajikin sa.
Daga saman daɓen kuma Sassaƙen gunkin nan wanda suke kira da abun bautar su ne kafe awuri ɗaya, ɗauke yake da kayan ado kala kala manne ajikin sa, sai daga can gefen sa kuma aka ajiye wata shimfiɗar fata tafkekiya, yayin da kowacce kusurwa dake kan shimfiɗar kuma ta kasance ɗauke da kaskwayen Huta waƴan da suke matuƙar ci da huta, sai dai kuma kamar yacce Boka ya faɗa gaba ɗaya hutar suna futar da jan hayaƙi ne, yayin da kalar hutar kuma ta kasance baƙa!
Acan kuwa tsakiyar shimfiɗar mazaunin Boka mai hutar kasko ne awurin.
Gaba ɗaya layayoyi ne da ƙulluka kala-kala zagaye da mazaunin nasa, yayin da daga gaban sa kuma aka ajiye wata randa da take faman ci da huta itama, sai akusa da ita kuma aka ajiye wani ƙaton faranti da yake ɗauke da farin yashi acikin sa mai matuƙar yawa.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now