Page 7

28 0 0
                                    

🐎 *BAƘAR MASARAUTA* 🐎
                 👑👑
                    🦋
               🦅🕊🦆
             🐍🎠🐄🏹
                       

  _*NA*_


UMAR FARUQ*D*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*


*FREE PAGE 07*

"Shin waya sanar da kai wannan tatsuniyar da har kake shelantawa duniya cewar ni ɗin takace?" Ta faɗa cikin kaushi tana mai kafesa da dara-daran idanuwan ta, tukun daga bisani ta ɗora da faɗin. "To idan ma mafarki kake ina son kayi gaggawar farkwa, domin kuwa ni ɗin nan daka gani an hallice ni ne domin mutum ɗaya, haka kuma na daɗe da zamtowa mallakin sa, dan haka ina mai shawartar ka akan kayi gaggawar komawa wurin waƴan da suka aiko ka zuwa gare ni kasanar musu da cewar banyi ba, domin ko bazan taɓa yi maka ba har abada, kamar yacce kaima bakai  mun ba, kuma baka da abubuwan da zanyi tinanin zakayi mun ko agaba!" Ta ƙarsahe maganar ƙasa-ƙasa tana mai jifan sa da wani irin matsayacin kallo, tukun daga bisani ta juya tana mai sauka daga kan shmfiɗar, sannan ta sanya takalmam ta, tukun ta fara ɗaga ƙafafuwan ta tana mai dosar hanyar da ta biyo ba tare da ta tsaya jin ta bakin sa ba.
Yayin da shi kuma Yariman Yamma lokaci ɗaya yana yin sa ya sauya, kana gaba ɗaya annurin dake kan fuskar sa ya ɓace ɓat, idanuwan sa kuma suka kaɗa sukai jajajir yana mai kallon ta, kafin daga bisani kuma ya buɗe baki cikin kaushi yana mai faɗin. "Shin waya baki izinin tafiya ne da har kika juya kika tafi?"

Cak Gimbiya Haddiyal ta tsaya daga inda take, sabo da furucin sa da taji ya daki dodon kunenn ta da ƙarfi, rumtse idanuwan ta tayi daga inda take ba tare da ta juyo ba, haka kuma bata cigaba da tafiya ba, sai zallar turiri kawai da take jin ranta na mata, tana mai tinanin kalar amsar da zata basa idan ta juyo.
Yayin da shi kuma ya miƙe daga kishingiɗen da yake yana mai zuwa ya sanya takalman sa, tukun ya fara ɗaga ƙafa cikin takun sa na isa yana mai dosar inda take.

Direct ya huce bayan ta yana mai zagayawa ya tsaya daga gaban ta gab da ita, tukun ya ranƙwafo da kansa yana mai rage tsayin sa ya zamto fuskar sa ta dawo saitin tata fuskar, tayarce har suke jin dirar numfashin junan su.

Kallon-kallo suka fara aikawa junan su da shi ba tare da wani daga cikin su yace tak ba, tukun daga bisani shi Yariman Yamma ya buɗe baki cikin kakkausar muryar sa yana mai faɗin. "Ke atinanin ki har akwai wani jarumin ne bayan ni aduk faɗin jahar nan da ƙetaren ta, ko ko azaton ki akwai wani mutum wanda zai iya jure raɗaɗin tsumagiya ta? Shin shi ɗin ɗan wace masarauta ne ma da farko?" Ya faɗa ƙasa-ƙasa tayarce ita kaɗai ce zata ji yana mai kafeta da idanuwan sa, kamar yacce itama ta kafesa da nata, tukun daga bisani ya saki wani shu'umin murmushin da yayi ai'nahin futo da kyawun sa, sannan ya ɗora da cewar. "Agaskiya nayi matuƙar jin daɗin sauraron wannan labarin daga bakin ki, domin ko ada ina tinanin bani da abokin karawa wanda zamu gwada ƙwanji tsakanin ni da shi wurin neman ki, amma sai gashi yau naji cewar akwai sa daga bakin ki, hakan kuwa ki sani ba ƙaramun farin ciki ya sanya ni ba, sai dai kuma ina son ki shaida masa cewar ni Yariman Yamma, tun farkon kafuwar ahalin mu ba'a taɓa yin wani wanda yay bugun shaɗi ba tare da yayi nasara ba, dan haka sai shima ya ƙara shiri akan wanda yake yi, domin kuwa ke ɗin tawace ni kaɗai, kuma an halkice kine domin n... "Dakata Malam!"
Ta faɗa da ƙarfi tana mai ɗaga masa hannu sama, tukun ta buɗe baki tana mai sakin wani irin wuci tare da faɗin. "Kar ka kuskura ka ƙara gigin furta kalmar cewar ni ɗin takace muddin baso kake na datse harshen ka ba kafun kabar wurin nan, domin kuwa wannan kalmar mutum ɗaya ne kawai ya halatta ya faɗe ta aduk faɗin duniya, kuma wallahi wallahi ni ɗin tasa ce kamar yacce shi ɗin yake nawa, bayan shi kuma babu wani agefen sa." Ta ƙarasa maganar tana mai juyawa daniyyar tafiya.

Caraf taji Yarima ya cafki yatsun hannuwan ta adai dai lokacin da ta ɗaga ƙafa danniyar yin gaba.
Cak ta tsaya ai'nda take ba tare data juyo ba ranta na tsantsar ƙuna, yayin da shi kuma ya saki yatsun hannun nata yana mai sake komawa daga gaban ta.
Ɗauke kai tayi daga kansa tana mai kallon gefe tare da sakin huci, domin kuwa aduk lokacin da zata kalli fuskar sa ji take tamkar ta shaƙesa ya mutu dan baƙin ciki.

BAƘAR MASARAUTA Where stories live. Discover now