LAIFI TUDU NE

863 35 2
                                    

*LAIFI TUDU NE*

        *NA SADNAF*🩸

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM*

*Page 1*

Bugun da ake yiwa gate din gidana da k'arfi yasa na ajiye cokalin da nake kwashe dankalin da nake soyawa nayi waje da sauri Ina mamakin mai buga gidan haka dan ba Wanda nake sa rai da zuwansa goma ma na safe waye zai zo min gida.
"Waye"?

na ce a fusace a daidai lokacin da nake k'ok'arin bud'e k'ofar Ina masifa kasa kasa

Wayanda na gani yasa na saki fuska ta na matsa daga bakin gate din dan su samu damar shigowa

Hajiya bilki ce mahaifiyar mijina da yayar mijina Maman Afnan sai kanwarsa jidda

Kallon da Hajiya ke min idonta kur akan cikina yasa nayi kasa da kaina tare da Jin kunyar rigar baccin da ke jikina shap na manta ban dora zani akai ba kasan raina kuma inata mamakin abinda ke tafe dasu da safen nan Mahmud baya nan ballantana ince sabida shi suka zo

"Hajiya kindai gane wa idonki ko"?

Mmn Afnan tace itama tana kallo cikina

Hajiya bata ce mata komai ba illa shigowar da tayi ta nufi cikin gidan suka mara mata baya suna magana kasa kasa haka kawai naji hankalina ya tashi dan da gani wani abun ke tafe dasu na tashin hankali iya sanina ban musu komai ba

Cikina na kalla daya fito Sosai  nabi bayansu Ina tunanin Mai kalmar mmn afnan ke nufi da ta dai gane wa idonta ko

Ina Shiga palon naga duk sun zauna akan 3 seater Hajiya Kuma nata girgiza kafa duk da bansan mai ke tafe dasu ba sai da jikina ya dauki rawa cikin karfin Hali nace "Sannunku da zuwa Hajiya Ina zuwa dan Allah"

Nayi hanyar d'akina da Sauri jikina na cigaba da rawa Ina Shiga na jingina da k'ofar tare da dafe kirjina iya sanina ban musu komai ba dan sati biyu ma da suka wuce nida Mahmud muka je muka gaisheta.
Sleeping dress din jikina na cire na zura doguwar rigar da nayi Sallah na jawo hijabina na saka nayi waje

A kitchen na fara tsayawa na kashe gas din na bud'e fridge na dauko ruwa na nufi palon Ina sallati a raina.

A gabansu na ajiye ruwan Na saci kallon Hajiya dake min wani irin kallo haka ma Mamn Afnan jidda kuwa latsa wayarta kawai take tana taunar cingam

"Hajiya Ina kwananku"

"Batula tashi ki zauna akan kujera"

Hajiya tace Fuskarta a had'e

Tashi nayi na zauna Akan kujeru Ina "Allah yasa  ba laifi nayi ba Hajiya"

Mmn Afnan ce ta fara k'ok'arin Magana hajiya ta daga mata hannu
"Batula watanki nawa yanzu da Aure"?

Hajiya tace cikin wani irin muryar daya sa jikina fara rawa cikin rawar murya nace " wata uku kenan"

"Batula cikin jikinki ba na wata uku bane  wanan cikin da nake kallo a jikinki zaiyi wata shidda ko bakwai da ciki kika auri Mahmud kenan abinda nakeso na sani shin Kun fara sanin juna da Mahmud a waje ne?ko Kuma wani ne ya miki ciki kika zo wa da Mahmud cikin gidansa"?

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun bangane ba"

Nace tare da zamo wa daga Kan kujeran nayi zaman dirshan a kasa hawaye ya hau zubo min Ina "Hajiya wlh cikin jikina na Mahmud ne a gidansa na samu cikin dake jikina

"Karya kike batula wlh Tallahi cikin nan ba wata uku bane ko yaron da bashida wayo ne ya kalli cikin nan yasan cikin nan ya tsufa kifito ki gaya Mana gaskiya sai a taru a rufawa juna asiri,idan har kinsan kunyi mua'mallar banza da mahmud a waje kafin kuyi aure ki gaya mana.kawai mu san yanda zamu yi"

LAIFI TUDU NEWhere stories live. Discover now