page 2

512 14 2
                                    

*LAIFI TUDU NE*  ....!
       
  *NA SADNAF*🩸

*Page* 2

"Bbynki is healthy macece gata katuwa Masha Allah"

"Wata nawane cikin nawa Dr"?

Nace gumi na karyomin

Murmushi tayi ta cigaba da yawo da abin a cikina tana rubutu a cikin wani takarda idan ta Kara yawo da abin a cikina sai ta Kara rubutu a haka har ta ga ma ta ajiye tare da cire handgloove din da ta saka a hannunta ta jefa a waste bin din dake wajen kofa tana tashi muje"

Wani irin mik'ewa nayi ko nauyin cikin jikina banji ba na dira gabanta ina "Dan Allah dan annabi ki gaya min watanin cikina ki taimaka min"

Murmushi tayi mai had'e da mamaki tana "toh saurin Mai kike ki bari muje office mana"

Zub'ewa nayi agabanta Ina "ki fara gaya min Aunty likita dan Allah dan annabi akwai dalili"

"Wai lafiyarki kuwa"?

Tace tana rage faraar Fuskarta ni kuwa na durk'ushe a gabanta  na fashe da kuka Ina "Dan Allah dan annabi aunty ki gaya min ki rufa min asiri "

"30weeks cikin jikinki bi maana wata bakwai da sati biyu"

"Likita banji mai kika ce ba kina nufin wata uku ko dai kunnena ne bai ji Mai Kika ce ba"

"Bani hanya na wuce ana jirana a office"

Wani irin damka na kaiwa kafarta cikin azabar tashin hankali na fashe da kuka ina "Wata na uku da aure likita taya na samu cikin wata bakwai har da sati likita uwar mijina ce a office dinki da yayarsa da kanwarsa taya zaki kai musu scaning dinan su  gani Aunty likita na Shiga uku na lalace ki taimaka min Kar Aurena ya mutu ki rufa min asiri kice cikina wata ukune dan bansan yaushe nayi cikin wata bakwai ba ki rufa min asiri kamar yanda Allah ya rufa miki"

"Allah mai iko baiwar Allah toh Ina ruwana a cikin duk abinda kika lissafa min nan asibiti ne aikina kawai nake yi ki sakar min kafa dan Allah ki daina b'ata min lokaci"

Tace fuska a hade tana k'ok'arin fusge kafarta da na rik'e gam

"DR ki dubi girman Allah ki rufa min asiri kar Aurena ya mutu wlh bansan ya akayi na samu ciki ba dan ban tab'a b'atan wata ba sai da nayi aure bansan ya akayi na samu ciki ba"

"Kila a ruwa Kika Sha kafin kiyi auren Allah ya b'oye kayansa yanda bazaki iya sanin kina dashi ba,dan kila da kinsani tun kafin kiyi aure da tuni kin zubar na rasa mai yake damunku Yan matan nan kuyita zubar da mutuncinku kafin kuyi aure haka yan mata ke layi a asibitin nan dan a dinke su bansan Mai kuka maida kanku ba abinda Kika shuka shi Zaki girba yanzu har ni zaki cewa baki san ya akayi kika samu ciki ba mtsss"

Ta fusge kafarta a fusace tayi waje

Ni kuwa rawar da jikina yake yasa na kasa bin bayanta na rufe fuskata da tafin hannuna Ina rusa kuka,wata uku da cikina wata bakwai toh garin Yaya,inno da baffa dana tuno yasa kirjina wani irin bugawa uwa uba mahmud"

Dafani da akayi yasa na dago a firgice

"Zan rufa miki asiri sabida nima inaso Allah ya rufa min asiiri amma kisani kin jefani nima a  cikin hatsari idan kuka je wani wajen aka miki scaning aka ga watanin cikinki zaki batawa asibitin mu suna yanzu ya za'ayi kenan"?

"Aunty likita Allah yasa ki a Aljanna yanda kika nemi rufamin asiri insha Allahu Allah zai rufa miki bazan bari mutuncinki ya zub'e ba yanzu a gaban uwar mijina nake so dai kice kinyi scaning din Yan biyune a cikina dan Allah"

Mik'ewa tayi bata ce min komai ba ta d'auko farar takarda ta fara rubutu sai da ta gama ta cukwikuye na hannunta tasa a watse bin ta d'auki Wanda ta sake rubutawa tayi hanyar waje  tana taso mu tafi amma zan baki shawara karki gwada zubar da cikin jikinki dan kina haka kin jefa rayuwarki a hatsari cikin jikinki ma  yanzu ya isa haihuwa karki dorawa kanki wani zunubin kiji da guda daya"

LAIFI TUDU NEWhere stories live. Discover now