*LAIFI TUDU NE*....!
*NA SADNAF*🩸*Page 7*
"Ta layin nan nasan itace"
"Wane layine wanan"?
Amrah karamin wayarta ta d'auko daga Jakarta ta cire layin dake ciki ta saka sim din.
Tare da shigar da lambar Nazeema a karamar wayar tayi dailing
Nazeema kallonta kawai take sai da wayarta ya fara ringing tana ganin lambar ta mik'e tsaye hannunta biyu dafe da kirjinta tana "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amrah Ina kika samo lambar tsinanen"?
Murmushin takaici Amrah tayi ta d'auke hawayen daya zubo mata tana "Tsinaniya dai zakice ba tsinanne ba Batula ce take amfani da layin shiyasa nace miki ba iya ni tayi wa ba har daku"
Nazeema jikinta rawa kawai yake tama kasa magana sai kara kallon wayarta take dan ta tabbatar da wai layin da take gwadawa kusan kullum tana san taji ranar da zai Shiga ta zagi wanda ya tona mata asiiri a wajen iyayenta
Take ta tafi tunanin ranar da bazata tab'a mantawa ba
Amrah lokacin ta daina zuwa makaranta ya rage iya su hudu ke zuwa dak'yar suka saba da rashinta Nazeema ma Sam makaranta ya daina Mata dadi sabida balain sabon da tayi da Amrah.
Ko a yau sai da suka je makaranta suke Jin labarin ashe lecturan nasu bazai samu shigowa ba gashi lecture daya ne dasu.
Cafteria Suka nufa wajen goma aka dafa musu indomie da zumar idan sun gama ci sai su tafi gida.
Inda hibba tace musu dama tana da Abubuwan da zatayi a gida gwara ma ta koma da wuri Salma kuwa tace Sam bazata koma ba zata yi ta zama a makaranta sai uku zata koma gida idan ta koma yanzu aiki zata yi ta sha
Nazeema itama Zama tace zatayi a makaranta Batulan ce dai bata ce komai ba suna dab da gama cin indomie.
Rabia ta musu Sallama,duk da ba wani kawance suke da ita ba suna gaisawa wani zubin har ta zauna dasu suyi hira.
Duk a cikinsu tafi sabawa da Nazeema da Amrah sabida yanayin sakin fuskarsu da barkwanci tana zama Batula ta had'e rai tare da kau da Fuskarta
Rabia bata bi ta kanta ba ta hau Jan Nazeema da Salma da hira a cikin hirar suke maganar rashin shigowar lecturan har Nazeema da Salma nace mata bazasu koma gida ba yanzu za suyi zaman su a makaranta idan ba haka ba suka koma ma yanzu aiki zasu je su sha a gida.
Rabia washe baki tayi tana "Wlh nima ba gida zan koma ba yanzu katsina nayi daga nan"
Hada baki sukayi wajen tambayarta Katsina"?
Gyada Kai Rabia tayi tana "ee wlh katsina zani amma a yau zan dawo zanje na dubo wata kawata mai zai hana ku rakani"?
"Zanso zuwa wlh badan Aleee ya kirani zai shigo yanzu ba"
Salma tace
Nazeema kuwa tayi caraf tace "Aikuwa zanje wlh indai yau zamu dawo kin tabbata Kuma zamu dawo da wuri"?"Mai zai hana zamu dawo da wuri hud'u ma muna garin nan"
"Mik'ewa Rabia tayi tana "to tashi mu tafi sabida Kar mu dade"
Ido Hibba ta ringa yi wa Nazeema da jikinta keta rawa zata je katsina dan bata tab'a zuwa ba dama amma Nazeema ko kula batayi ba.
Tunda suka fara magana Batula bata d'ago ba sai data ga alamar dagaske Nazeeman bin Rabia zatayi tace "Nazeema sabida bakida hankali ke yanzu sai Kibi wata can garin katsina kamar bakida mafada?karki manta fa iyayenki karatu suka turoku ba yawace yawace ba idan Rabia bata san darajar Aurenta ba zata na bibiyar mata kema sai ki biye Mata"?
![](https://img.wattpad.com/cover/289969461-288-k751509.jpg)