*LAIFI TUDU NE*....!
*NA SADNAF*🩸*Page 3*
"Taimkona kike nema tofa Ina jinki"
Ji nayi maganar ma ya min nauyi taya ma zan soma ce mata Inda ta zubar da cikinta nake so ta min kwatance anya na Kara haka ban mata cin fuska ba tunda waiwai Wai ne ko da ta zubar da cikin ba wanda ya tare ta da zancen
"Nifa bana san iskanci idan kinsan kin kirani ne kawai dan ki b'ata min lokaci ne zan kashe wayata"
"Bushira wata cousin dita ce aka yiwa fyad'e abin yazo da tsautsayi ashe ta samu ciki bata sani ba sai da cikin ya girma sosai ta gane tana da ciki,gashi an kusa bikinta shine nace bari na kiraki Bushira ko zaki taimaka min idan akwai asibitin da Kika sani ko Wanda kika san zai iya zubar Mata da cikin ki taimaka mana dan Allah"
"Kan uba amma Batula kin raina min hankali duk kawayenki da mu ke harka daya baki neme su kin ce su hadaki da mai zubar da ciki ba sai ni, Batula Ina Kika Kai iliminki da tsoron Allahnki da har zaki nemawa Yar uwarki hanya da zata zubar da ciki da ke kinsan haramune,na dauka zaki yiwa Yar uwar taki wa'azi akan ta hakura ta haifi cikin jikinta kila kaddararta kenan tunda nasan kin kware a waazi Batula da ace wata ce tayi cikin nan haka zaki yita zaginta kina kyamatar ta batare da kinsan dalilin daya sa tayi cikin ba,amma yau da yake abin ya fado Kan jininki hankalinki ya tashi har kina neman yanda zata zubar da cikin, kila baki tab'a kawo wa wani naki zai fada cikin irin wanan halin ba shiyasa a baya kike ta aibata duk wanda ya kauce hanya ko ni da kike wa kallon watsatsiya har nayi cikin shegen toh ba zubarwa nayi ba wlh zub'ewa yayi dan Ina tsoron na Kara dorawa kaina wani zunubin kauye na koma akan na haife cikin Allah cikin ikonsa kuma ya fita da kansa dan haka mallama mai Niqab bansan Inda ake zubar da ciki ba"
Daga haka naji ta yanke wayar.
Dafe kaina nayi Ina jin kamar ya fado wacce nake tunanin zata iya min hanyar na zubar da cikin gashi ta gaggaya min magana.
Ganin biyar tayi gashi banyi sallah laasar ba yasa na mik'e dak'yar na tari abin hawa ya maidani gida.
Yanda cikina ke ta motsi da bak'ar yunwar daya sa jikina rawa yasa na had'a shayi na sha na dan samu nutsuwa nayi Sallah na baje Ina cigaba da tunanin hanyar da zan bi na zubar da cikin jikina.
Ko da Mahmud ya kirani Sam bai gane kaina ba Inda ya d'auka duk b'acin ran abinda mahaifiyarsa ta min ne sai rarrashina yake yana bani hakuri,akan idan ban saki raina ba zai dawo a goben nan.
Tuni na danne tashin hankalin da nake ciki na biye Masa muka tab'a hira Kiran sallah Magriba yasa Muka ajiye wayar na cigaba da tunanin yanda zan zubar da cikin jikina.
A ranar bacci bai ga idona ba sabida tunanin asibitin da zanje na zubar da cikin.
Koda gari ya waye Sassafe na fice daga gidan asibitin dana fara zuwa ban samu ganin likita ba sai wajen tara na safe sabida sammakon da nayi gabana sai fad'uwa yake Ina tunanin ko zasu yarda ma su zubar min da cikin tunda ba kowane asibiti ake yarda a zubar da ciki ba.
A lokacin da likita ya tambayeni abinda ke damuna bayan ya rubuta sunana kasa magana nayi har sai da ya sake tambayata tare da dagowa Yana kallona
Kasa nayi da muryata na fada Masa abinda nake so ayi min
Kallon da yake min yasa jikina d'aukar rawa ya zare glass din fuskarsa Yana "Asibitin nan ya miki Kama da Inda ake zubar da ciki? toh bama zubar da ciki a asibiti nan tashi ki fitar min daga office next"
Yace yana maida glass din fuskarsa yanda yayi maganar cikin fada fada yasa na mik'e da sauri na fita Waje Ina jawo nikaf dina dana daga sama dana shiga office din.