page 8

347 11 0
                                    

*LAIFI TUDU NE*....!
          *NA SADNAF*🩸

*Page 8*

"yaro dai da kika sani na jawo jikina ke akan abinda Batula ta min har wayanda ban taba magana dasu ba wlh jawo su nayi jikina, bazaki gane komai ba Nazeema ki zuba min Ido kawai kiga yanda zan rama abinda ta mana"

"Amrah gaskiya halinki ba mai kyau bane har ki gano irin Wanan Abu ki kasa gaya mana har akayi bikin Batula dake Kika cashe Ashe da abu a Zuciyarki a kanta kinsan kuwa zaki iya kissan kai da kinsani tun lokacin kin mata magana  dan gani nake ai a yanzu ya hucce ba zakiji zafin da kamar zakiji a lokacin ba"

"Nazeema kenan har na mutu kuwa da ciwon abinda Batula ta min a raina wai ko duk bakiga Abubuwan da ta min bane naku nafila ne akan nawa

"Toh ya akayi Kika gane tana da ciki Yaron ne ya gaya miki?Naga Kuma yaro ko magana basa yi da Batula a makaranta damu kawai yake gaisawa

"Ai shiyasa nace miki bakisan waccce Batula ba,Batula ta wuce tunaninki da hankalinki yanzu dai ai Kinga videonta a wayata ko baki yarda ita bace"?

"Ina kokwanto Amrah wlh sai nake ganin kamar bazata aikata duk abinda Kika ce ba sai nake ganin  kamar ba ita nagani ba Amrah ki tuna Batula mana"

"Ke ai bakida tunani sam Sam a cikinmu dama ke wawuya ce ga abu nan zahiri kina gani kina cemin ba haka ba ko dan bake tayiwa Abunda ta min ba ko so kike kice min sim din saka mata akayi a Jakarta tunda baki yarda ba ina zuwa"

Amrah tace tare da latsa wayarta ta Kira Yaro a waya ta saka a handsfree

Bugu biyu ya d'auka Yana "Ta wajena ya akayi"

"Yaro nawa ni kadai ya labarine"

"Ba wani labari matuniyar tunda kin k'i zuwa a hadu ayi abin arziki"

"Waye yak'i abin arziki yaro ka bari na dawo daga jigawa zan baka mamaki".

"Allah matuniyar kinsan kuwa da Alhaji yaji dadi dan bakiga yanda ya rude yake damuna akan maganar ki ba ke kadai zaki saka ya manta kawar taki da yake min nacinta"

"Wai Batula"?

"Emana ita fa ko shekaranjiya sai daya tura mata kudi"

"To sabida me ya tura mata kudi da auren nata ma bibiyar ta yake"?

"Itace dai ta kira tana San kudin nace Mata banidashi sai dai a wajen mutumin ta Ina fada Masa jiki na rawa ya tura Mata shiyasa nace ke da Kika fita komai Kuna had'uwa zaki mantar dashi ita"

"Ba damuwa yaro karka damu Ina dawowa Zan kiraka gwara nima a dama dani a harkar nan tunda Mai Niqab ma ta daddana"

"Hahahaha wlh kuwa ke da bakya saka Niqab Zaki fi abin arzki nima Zan fi samu da yawa akanki"

"Toh ba damuwa yaro zan sake kiranka"

Daga haka Amrah ta kashe wayar tabi Nazeema data saki baki tana kallon wayar da kallo tana "Mai kika fahimta a wayar da mukayi da Yaro ko sai dai na fito na miki gwari gwari tunda bakida ganewa"

"Hmmmm Amrah tashi ki tafi yanzu tunanina ba daidai yake bani ba"

Dariya Amrah tasa ta mike tare da d'aukar Jakarta ta fito Nazeema ta rakata har bakin titi ta tare mata abin hawa ta tafi har lokacin mamaki bai gama sakinta ba duk da wayar da akayi da yaro hakan bai saka taji ta yarda ba.

Sam ta kasa yarda wai Batula zata iya musu haka video data gani ma gani take Kamar ba ita ba bace.

Abinda ta kasa ganewa shine mai dalilin daya sa duk ta musu haka.

LAIFI TUDU NEWhere stories live. Discover now