page 4

338 11 3
                                    

*LAIFI TUDU NE*....!
          *NA SADNAF*🩸

*Page 4*

Amrah

       Wani irin damka ta kaiwa kafadar Nazeema da take yiwa kitso tana "Batula ce ta kiraki ko"?

"Eee itace wlh ya akayi Kika san ita ta kirani"

Wal tayi da Ido ta ajiye kibiyar hannunta akan tabarma tana sakin murmushi

Nazeema Kuma ta mik'e tana hade gashinta da kitson da ake mata cikin Sauri

Tana "Bari naje na dawo ki karasa min"

"Hahahaha Alhamdulillah Allah Nagode ma ka Nazeema kin tuna ranar da Batula ke raban katin bikinta mai nace Miki"?

Nazeema yamutse fuska tayi ta tafi tunani

Ana sauran sati biyu daurin Auren Batulan ta fara rabar da katin gayyata inda ita da wasu yan uwanta ke rabar katin.

Koda taje gidansu Amrah Kai katin anan ta tarar da Nazeema da ita Kuma taje amsar dinki a unguwarsu Amrah dan anan ta ke kai dinkinta tunda Kuma taga Amrah ta iya kitson ita ke yi Mata.

Batula da shigar Hijab da Niqab dinta Suka Shiga gidansu Amrah bayan sun gaisa da Mahaifiyar Amrah ta yiwa Batula Allah ya Sanya alheri tace Mata ta Shiga daga d'akin Amrah da Nazeema na ciki.

Tana Shiga d'akin ta tarar da Amrah da Nazeema nacin abinci.

Nazeema ce ta fara washe baki tana "Amarya kin sha kamshi"

Amrah ta mata kallon kasa kasa itama ta washe baki tana tunda ga waje nake jiyo kamshi ayiriri abu namu maganin a kwabe mu"

A gefen gadon Batula ta zauna tare da dage Niqab din fuskarsa tana murmushi Nazeema ta tsame hannunta daga abincin tana "Bari na wanke hannuna nazo naga katin"

Amrah kuwa cokalin hannunta ta ajiye ta hau kan gadon tare da jawo katunan da ta shigo dasu ta hau dubawa.

A daidai lokacin da Batula ta cire hijabin jikinta sabida mugun zafin da take ji

Tana idda cire hijabin Amrah ta dago tana "Kuut ya naga kirjinki ya cicciko haka kamar mai ciki  Kinga yanda kika yi  wani fresh kuwa"?

Amrah ta kai hannu kirjin Batula da zummar tab'a kirjinta dan ita bata dau hakan a bakin komai ba Batula kuwa ta mak'e hannunta tana " Allah ya shiryeki an gaya miki kowa irinki ne gyaran jiki aka min shiyasa kika ga haka"

Kada Kai Amrah tayi ta cigaba da Kare mata kallo kasa kasa tana kallon yanda cikinta ya dan taso a cikin rigar
"Lailai mai gyaran jikin nan ta iya hadani da ita pls"

A daidai lokacin da Nazeema ta dawo daga wanke hannun itama ta d'auki Kati daya tana dubawa

Batula kuwa ta mik'e tana "Tafiya zamu yi ma daga nan gidan Hibba muka yi zamu Kai Mata katin ga gidansu jameela ma wlh inasan zuwa ba kuda mutunci wlh ku fa ya Kamata kuyi rabon nan"

"Sorry amarya wlh muna ta preparation  yau ma na karbo dinkina daga wajen tela Kinga"

Nazeema tace tana nunawa batula da ke k'ok'arin saka hijabinta

"Kai Kai kai Batula ya naga cikinki a kumbure"?

Nazeema tace tana kai hannu cikin Batula da ta saki murmushi tana "Nidai na Shiga uku da Wanan shegen tumbin daya fito mun kowa sai yayi min magana wlh wani magani Adda fatsuma ta bani wai Yana saka kib'a Ina fara Sha wlh ya fito min da tumbi na hau kib'a Mahmud har sai da ya Nemo min slim tea na rage kib'a da maganin rage tumbi dasu ma nake yawo a jakata Kinga"

Batula tace tana zarosu daga cikin jakar dake rataye a kafadarta

Murmushi Nazeema tayi itama tana tab "Amma maganin nan ya miki tsiya ke da cikinki ke shafe sai gashi ya fito miki da tumbi ku jirani mu fita gabadaya hanyar mu daya,"

LAIFI TUDU NEWhere stories live. Discover now