*LAIFI TUDU NE*....!
*NA SADNAF*🩸*Page 9*
"Da Adda Maryam nake waya"
"Da Adda Maryam kike waya shine zaki fita har waje bazaki iya wayar a gida ba"?
"Katine bani dashi a waya shine na fita dan na siyo Ina hanyar komawa ta kirani"
"Yaushe kika fara siyan Kati Batula naga ni nake saka miki katin duk bayan kwana biyu and ba yanda zaayi katin Dubu daya ya Kare cikin kwana uku dan nafi kiranki a waya ba Kuma kowa kike Kira a waya ba ballantana ace anan kudin ke tafiya,Koda ma katin ne babu mai yasa zaki fita da kanki bazaki bawa Jidda ko Nura su siyo miki ba? Batula bana san irin haka na fada miki"
"Toh wai zargina kake Mahmud mai yasa kake min haka shikenan dan Waleeda na satar fita da kulle kullen samari da aurenka lailai ne nima haka nake kai dai fi kowa sanin halina ya Kamata Koda fitar nayi ban gaya maka ba ka kyautata min zato,Taya Zan aiki Jidda da ta raina ni tunda ta dawo gidan nan bata tab'a gaisheni ba kallon banza ke rabani da ita,nida gidana ban isa na sake ba sai dai na Shige daki haka Nura zai zo da abokanan sa su cike gidan Jidda tayi ta musu girki"
Nace a fusace Ina jin raina na b'aci yanda mahmud yaga na hau yasa ya sauko yana "Batula kinsan Ina da kishi ko ganinki bana so wani yayi shiyasa kike ganin kamar takuraki nayi kinsan idan miciji ya sare ka sau daya ko tsumma ka gani zabura kake yi shi yasa amma dan Allah ki daina fita batare da izinina ba sanan jidda kanwata ce kina da right din da zaki aiketa har aiki ma ki sakata,and a ganina ba wani Abu bane dan su Nura na zuwa gidan Kinga hakan zai rage miki zaman kadaici Mmn Afnan ce tace ya Kamata ma azo a zauna dake Sabida yan biyun da kike d'auke dashi Ina ganin Kamar hakan zai saka kiji dadi kina Jin motsin mutane a gidan"
Bance masa komai ba ya gama surutansa sai daya tabbatar da na Shiga gida ya kashe wayar.
Ina shiga gidan na watsawa Jidda wani mugun harara dan nasan ita ta Kira mahmud tace Masa na fita dama nasan zuwanta gidan ba alheri bane samin Ido kawai zata ringayi
Itama hararar tawa tayi tana magana kasa kasa ban bi ta kanta ba na Shige d'akina tare da kullo k'ofar dan so nake na kawo karshen Kiran da Alhaji ke min.
Bandaki na Shiga na sake Kiran layin Yaro Yana dagawa na hau masa magiya "Yaro dan Allah dan annabi ka yiwa Alhaji magana ya daina Kiran wayata yaro Ina da Aure sabida mai zai ringa kira na? ko so yake ya kashe min Aure?dole sai dani zai yi Hulda Yaro na hadaka da girman Allah ka Masa magana Kai ma neman ka da nayi a waya da Aurena wlh tsautsayi ne"
"Ba fa ni na bawa Alhaji lambarki ba ki yarda nima bansan mai yasa duk Yan matan da Alhaji ke muamalla dasu ya kasa rabuwa dake ba Batula wani labari nake ji wai dagaske da ciki kikayi Aure"?
Haka kawai naji gabana ya yanke ya Fadi "Yaro wane irin magana ne wanan Kamar ya da ciki nayi Aure a Ina kaji wanan labarin"?
"A gari naji Batula kinsan zancen duniya baya b'uya Abunda zai bani mamaki shine idan har dagaske ne da ciki kikayi Aure baki Mana adalci ba dan rantse Mana kikayi bakya yi akan ki bamu gwara ki bawa wasu kenan"
"Yaro wane irin magana ne wanan duk shegen daya ce maka da ciki nayi Aure karya yake yi nidai duk ba wanan ba dan Allah dan annabi ka masa magana ya daina kirana a waya karku kashe min Aure yaro"
Daga haka na kashe wayar har lokacin jikina rawa yake gabana na fad'uwa taya Yaro yasan da ciki nayi Aure? Ya akayi Rabia itama ta gane watanin cikina"?
a Ina duk suka ji labari?ya akayi da ciki a jikina har na tsawon wata hudu bansani ba kafin nayi Aure mai yasa gwajin da naje asibiti da kaini dasu inno sukayi duk baa ga ciki a jikina ba"?Ko dai duk Wanda yasani ya san da ciki a jikina nice bansani ba"?
Duk abinda zanyi Ina takan tsantsan taya Zan samu ciki?