page 5

346 10 4
                                    

*LAIFI TUDU NE*....!
          *NA SADNAF*🩸

*Page 5*

Nazeema

Tana fitowa daga shagon chuku ta tare napep ta hau jikinta na balain rawa ta kasa yarda da abinda ta gani ta kasa yarda wai Batula of all people  da kowa ke mata kallon salaha ke d'auke da cikin shege yau badan ta gani ta Kuma ji daga bakin Batulan ba da rantsuwa zata ringayi tana karya ne.

Tunanin yanda Batula ta kware a waazi ta tafi lokacin suna level one kafin su shiga wani lectures sunje Cafteria cin abinci.

Duk sun dau gayunsu da siraran mayafansu Batula ce kawai ke Sanya da Dogon hijab da niqab.

Sun fara cin abinci kenan aka Kira Amrah a waya tana gama amsa wayar ta kalli Salma da Nazeema tana "Suwai ce ta kirani za'a yi  Casun wata kawarta gobe  tana gayyatar mu"

Wani irin tsalle Nazeema ta doka tana "Kamar kuwa tasan na siyo wani tsallelen doguwar riga"

"Karfe nawane goben dan wlh naji mama na cewa zan rakata gidan wan babanmu Kuma da alama kwana zamu yi"

Salma tace tana ajiye cokalin hannunta

"Ku dai ku shirya kawai Goben ni sai na Shiga kasuwa zan samo kayan da zan saka Nazeema ko zan samu na sawa a wajenki da baa sanki dashi ba dan.naga ke anan kudinki ke tafiya"

Amrah tace da murmushi

Tunda suka fara magana Batula bata ce komai ba sai da Hibba ta nuna itama zata je casun Batula ta dago tana "A gaskiya ya Kamata kuyi wa kanku fada wlh wanan ba rayuwa ce mai kyau ba  bakuda aiki sai zuwa party ne  tsakani da Allah iyayen ku  su turo ku makaranta amma a madadin kuyi abinda ya kawo sai dai ku ringa sheka aya wlh wanan ba rayuwa bace"

"Allahu Akbar ustaziya mai Niqab Nan ba islamiyya bane ko Massallaci idan kina so kiyi waazi kije can kiyi waazi kawai zuwa party shine haramun a wajenki"?

Salma tace tana harara Batula

"Hmm Salma kenan ai ke kin riga da kinyi nisa bakya jin kira ai ba iya partyn kuke zuwa ba Kuna hadawa da sheka aya iya Samarin nan dake shigowa su fita dake a mota ai ba karatu suke koya miki ba"

"Banida lokacin ki Batula mu Kam party yanzu Muka fara zuwa idan Kinga baki iyawa ki nemo yan uwanki ki Shiga cikinsu dan abokin dan iska shima dan iskane Kinga kenan kema itace tunda kina cikinmu"

Daga haka Salma ta mike tare da d'aukar Jakarta ta bar wajen

Batula Kuma ta dawo da kallonta kan Amrah da ta saka earpiece tana k'ok'arin Magana Amrah itama ta mik'e ta bar wajen hakane yasa ta dawo da kallonta kan Nazeema tana "Nazeema gaskiya dacine da ita dole na fada muku wlh kuyi wa kanku fada dan baku san a lokacin da mutuwa zata riske ku ba"

Murmushi Nazeema tayi tana "Batula wlh duk zargin da kike mana ba haka bane ki barmu dai muje casun iya abinda muke aikatawa kenan sai dan kulle kullen samari amma insha Allahu zamu daina"

Ta karasa da murmushi tab'e baki Batula tayi ta kalli Hibba dake ta dariya kasa kasa tana "Usztaziyarmu Allah ya bamu itaki wlh kina burgeni"

Ajiyar zuciya Nazeema ta sauke data dawo daga tunanin da ta tafi.

Wayar ta dake ta ringing a jaka ta d'auko misscal ta gani wajen goma duk daga wajen Amrah

Tana k'ok'arin kiranta Kiran Amrah ya Kara shigowa

Tana daga wayar Amrah tace "Nazeema bana san iskanci tundazu inata kiranki baki dauka ba cikine da Batula ko"?

"Hmmmm Ina hanya Amrah bari na sauka zan kiraki"

LAIFI TUDU NEWhere stories live. Discover now