P5

109 5 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

         _♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

            🅿️5️⃣

'''Ashe farhat ce ke mata sallama tana d'aga kanta ta kalli kofar parlourn tai arba da ita.

Murmushi tayi mata tashi tayi cikin sauri ta rungumeta tai mata oyoyo barka da zuwa k'awata.

Bayan sun gama rungume juna, sun gaisa.

Kai tsaye ta ja farhat suka wuce dinitable.

Wanda teburin ke cike da kayan breakfast, daman itama farhat, mai gidanta da wuri shima ya fita san mako yayi da asuba, ko breakfast baiyi bah, ganin haka daman itama ta fada mai, zata gidan k'awarta saudat.

Hakan yasa ko breakfast batai ba, tana gama yan aikace-aikacen ta, tayi wanka ta  shirya, ta nufa gidan k'awarta Saudat.

Bayan sunje dinintable, ko wacce samun wuri tayi ta zauna, Saudat tashi tayi tasa musu tea, hade da donut, suka shi suka sha, sukai Hamdalah.

Sanan suka dawo cikin parlour suka zauna, Saudat tana kusa da k'awarta farhat, suna jin dumin jikin junan su.

Da suka dawo parlour farhat, cigaba da zuba tai, tayi ta daman surutu tana bata labarai suna dariya.

Zuwa can Saudat taji shiru, ba ai maganar maganinta da,akace za,a kawo mata ba.

Bayan wani lokaci, bud'ar bakin, Saudat cema k'awarta farhat tayi bani labari, naji kinyi shiru ne?.

Haba dai ke kam k'awata saurin me kike haka,ina son ki kwantar da hankalinki.

Insha allah, Yau dai kam, Abban sadeeq, tamkar hannunki yake yau sai yadda kika ga dama kiyi dashi kuma zaki ce na fada miki.

Amma banso ki saurin bashi kanki haka cikin sauki ya kamata, a ce kidan ja,aji kemah tunda kemah sai da aka shamiki kanshi, ko kuma ince mah sai da kika siyoshi da kudin ki sannan kika samu kanshi.

Wow k'awata ina yinki gaskiya sosai, shiyasa kike kara burgeni, dad'ina dake kinsan abunda ya kamata mutum  yayi domin ampanin kanshi.

Sam bana dana sanin, saninki acikin rayuwata, a kullum ko da yaushe farin cikin kasancewa atare dake nakeyi, saboda kalar kwarin gwiwar da kike bani, ina fatan ko wacce mace tasamu, k'awa kamarki abun murna ne da farin ciki, ina alfahari dake k'awar amana.

Hmm kemah ai haka kike ta musamman awurina, shiyasa dole natashi na mik'e tsaye domin naga natabbatar da farin ciki a fuskarki, shine hankalina zai kwanta k'awata.

Allah sarki, k'awata karki ji komai, insha allah mafarkin mu zai cika nan ba da dad'ewa ba.

Ameen Allah yasa,
Insha Allah! Inaji cikin raina tunda na taho da maganin nan nakeji araina insha Allah zamuyi nasara k'awata.

Ameen suma ameen, nima ko da zanfi kowa farin ciki da hakan.

Hakane  k'awata, kuma aminiyata, farin cikin kinshine nawa, matukar kikai farin ciki nima daga lokacin nasan dacewa nayi nasara, domin idan kikai farin cikin tamkar da nima nayi ne abunda ya sameki ji nake nima ya sameni.

Zan hada k'arfi da k'arfe domin ganin kin samu biyan bukatarki kawata saboda haka, ki dai na hanzarin da kike shi ba gudu ba!..

Ga maganin da nazo miki dashi, zaki ban labari k'awata insha allah duk wani kuka naki, da wai-wai yazo k'arshe k'awata.

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now