P19

29 3 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚📚*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           '''Maman haneef'''

                🅿️1️⃣9️⃣

Nurse ɗin ta amsa takardar ciki ladabi da biyayya, sannan ta fito daga cikin office ɗin nan ta barshi shi da Saudat a cikin office tare suna hira ta barsu.

Cikin hikima Doctor Sani ya cigaba da satar kallonta sunayi suna hira,  idan suka ɗan haɗa fuska Doctor Sani murmushi yake mata.

Hira ta fara daɗi, tuni Saudat ta fara mancewa da abunda ya faru a tsakaninsu, ta fara sakin jikinta dashi.

Haka suka cigaba da hira tana ma Saudat daɗi sosai, shiru ta mai tana sauraronshi tana jin abunda yake cewa, kwatsam suna cikin haka again sai ga wannan Nurse din ta dawo daga inda aka aiketa siyo magani. Kamar dai  ɗazun da farko bata kai ga buɗe ƙofar ta shigo ba, nan ta tsaya bakin ƙofar tayi knocked karo na biyu, sannan ya ce, "come in" buɗe kofar tayi ta shigo ta zo dai dai bakin teburinshi ta miƙa mai sir gashi, ya amsa ya ce mata, " Please thank you, zaki iya tafiya shikenan"
"Ok sir thanks, na barku lafiya"
Ta buɗe ƙofar ta fito nan ta barsu ciki Doctor sani, ya buɗe ledar data siyo mai maganin ta bashi, domin ko bai dibawa ba kawai dai yasan har indai ance ɗin ansamu to shine ilai kuwa shine ɗin ko da ya diba, yasa hannunshi ya ɗauko maganin duk ko wanne ya ci roshi cikin ledarshi ya gama zana musu dosage na shan maganin sanan ya yi mata ƙarin bayani ya haɗa mata ya mai da mata shi cikin leda ya bata. Miko hannunta tayi ta amsa cikin fara'ah fuskarta cike da annuri, ta mai sai anjima zata tafi kenan Doctor Sani ya dakatar da ita.

"Shikenan kuma sai ki tafi ke kaɗai kuma ko wada escort naki baki so? Haba ke kuwa ni da ke ba faɗa muke ba mun shirya, mai zai hana nazo nai escort naki zuwa can kinga sai ma na sake diba marasa lafiyan naga?"
Kallonshi tayi ta ce, "Hmm Okay to please sorry, yi haƙuri na shafa'a kuma bugu da ƙari yanzu bansaniba ko za kai wani aikin ba, shiyasa kawai na ce na tafi da kaina tunda dai ba wani abu bane ba"
"Don't mind duk da haka ko aikin ni dai idan kin bani dama ina son nazo mi dai nayi escort naki pls kimun wanan alfamar" ya faɗa yana rokonta.
" Alright ba matsala na maka basai ai ta kaimu ga haka ba, wanda ya neme ka da abota to masoyinka ne"
"Nagode Allah da ki ka gane hakan, keta musamman ce"
"Uhmm kamar ya dai, banda, tsokana fa?"
" Nima ba tsokana nake ba"
"Shikenan Allah yasa da gaske ne"
"Hmm ki dena tantama a kai na Allah ya riga da yasa hakan"
"Allah ko saurin me ka ke ne?"
"Shikenan bazan sauri ba"
"A'a ni dai amma mamakin abu ne nake samun canji farat ɗaya haka"
"Haka ne daman kisan shi yadda al'amarin Allah yake"
"Ƙwarai kuwa da gaske"
" Yauwa ko kefa kinga ya kamata mu wuce mu tafi, saboda naga alamun idan muka tsaya wasa wasa hakan zai ci mana lokaci sosai"
"Ok Bismillah ko mu tafi" tana  faɗin haka ta wuce gaba ya biyota a baya suka tafi.

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now