P24

18 2 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚📚*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           '''Maman Haneef'''

                🅿️2️⃣4️⃣

Ko da ta fita murmushi ya kama yi yana Jindaɗi fuskarshi cike da annuri babu alamun ɓacin rai ko wani abu saɓanin haka ko ɗaya yana zaune har 12:30pm tayi yana diba agogan hannunshi ya ga wannan lokacin yayi maza yayi sauri ya tashi harhaɗa ka yayyakin da zai ɗauka xuwa gida sanan ya fito yasa key ya kulle office nashi ya fita zuwa harabar asibtin can ya biya wurin su Saudat yayi ma masu jiki sannu Allah Ya basu lafiya ameen, sannan ya fita zuwa harabar asibiti wurin parken  din motoci ya nufa ko da je wurin motarshi yasa key ya buɗe yashiga revose yayi sanan ya tuƙa motar ya fice daga ciki asibitin sai kuma dare kai tsaye gida ya nufa.

Saudat zaune take bakin gefe gado inda ta saba zaman gefen Abban Sadeeq,kamar kullum yanzu ma haka can take zaune hira suke suna ma juna murmushi, ko da 1pm tayi rana aka kira sallah karfe ɗaya Saudat tashi tayi tashiga toilet tayi tarki sannan tayi alwaka ta fito can harabar masallci ta fita akwai msallacin mata nan taje tayi sallah data idar shine ta dawo ɗakin da take jinyarsu abban Sadeeq, tana dawowa shima Abban Sadeeq ya shiga bathroom yayi wanka ya tsarke kake jikinsa domin yadda zaiji daɗin jikinsa kwana 2 kenan babu wanka jikinsa, sanan shima ya gama wankan yayi alwala ya fito masallacin maza dake harabar asibitin shima ya fita yaje yayi sallah ya idar sanan ya dawo inda su Momy da Saudat suke.

Har yanzu Momy bata farka ba baccin nata yayi nauyi sosai, Abban Sadeeq shi da Saudat hira suke tsakanin junansu mai ban daɗi gunin ban sha,awa idan ka gansu abun saiya birgeka.

                 ★★★★★

Washe gari da safe Mama  idonta biyu harta farka daga bacci  yau batai bacci ba kalar na jiya, Saudat da Abban Sadeeq zaune suke kan kujera suna shan tea da donut, itama haka Momy tana shan ruwan tea zallah babu komai sai madara kuma bata haɗa da komai  ba, haka take shanshi tana gasa bakinta akwai zafi sosai domin ita daman can tana son abu mai zafi sosai a rayuwarta.

Gama shan su tea ke da wuya, Saudat tayi ma Abban Sadeeq magana zata ga doctor kan a maganar ko mawarsu gida yau,Abban Sadeeq ko da ta faɗa mishi haka bai ce kata komai ba face, yayi mata murmushi yace, "Eh badamuwa tashi muje tare nima nayi excersice" Saudat ko da taji haka tuntsurewa tayi  da dariya tana faɗin, " Momy pa? Waye zai kula mana da ita kenan? Idan mu dukan mu mukatashi muka tafi ko kuma tana buƙatar wani abu?  Waye zai mata kenan pls dear ka tsaya anan naje nadawo kaima ɗin nasan ɗangwalolo ne jikinka ba wani kwari ke da....." Tana cikin faɗin haka batai auneba sai dai ji tayi an muntsuleta ajikinta zafi wayoooo ihu zatayi, saurin da yayi ya rufe bakinta nata yasakata shiru, itama ganin datayi ga damar ramawa tayi hannunshi abakinta ta ganna mai cizo a yatsanshi hankali cikin salo, dariya taka mayi tana faɗin ɗaya da ɗaya kenan zai yinƙura yatashi ta jawoshi tana faɗin yi hakuri karkasa jinya tadawo baya nashiga ukuna...

Ko da jin haka ce mata yayi, " lallaimah yarinyar nan nine kike cema ɗangwalolo wato ma na zauna karna dawo da jinya ba mai kike ɗaukata ne wai? To bara kiji wallahi ko tseren gudu zamuyi sai na wuceki Allah ina faɗa miki saboda haka ki denamun wani gani²...."

"No!.. ni duk ba wannan ba yanzu Abunda nake so dakai duk da naji ka samu sauƙi  sosai, ina son katsaya kai da Momy pls naje yanzun naje na dawo insha Allah yanzu zanje na dawo, ba wani jumawa zanyi ba" tana faɗin haka shikenan yace mata, " alright bakomai kije sai kindawo nima ba zuwa zan ba amma ki sani ni ba ɗangwalolon da ki ke cewa bane" tace, " toh naji, koma menene dai ai zanu haɗu anjima zan tester ka naji hakane.." ta faɗi haka tare da ɗaga mai gira, tashi tayi zata fita cikin ɗakin, jin haka da yayi tayi magana yana kallonta suka haɗa idanu ta ɗaga mishi gira ga kuma kato ɓarar datayi ɗaga hannunshi yayi ya dafa kanshi yana fadin a'uzibillahi, ko da ya kalli inda Momy take gani yayi hartayi bacci shayin nan data mai zafi har sakata bacci, Momy dake kwance bisa gadonta na asibiti wani bacci ne mai daɗi ya kwasheta sai baccinta take abunta bata san abunda ke wakana ba...

Tuni ashe Saudat ta lura da Momy tayi bacci, shiyasa take sakin magana iya son ranta, wanda shi Abban Sadeeq bai lura da hakan ba sam kwatakwanta, ko da ya diba inda Momy take gefensu kenan yaga tai bacci girgiza kanshi yayi yana mata nuni da hannunshi yana faɗin "ke koh? Tom!..." Sannan ta wuce ta fita cikin ɗakin tana faɗin kamar da gaske zaka iya wani abun kirki, ta tuntsure da dariya ta wuce ta cigaba da tafiyarta.

Abban sadeeq samun wuri yayi bakin gadon asibiti da yake kwance ya ɗan kishin giɗa kafin masoyiyarsa ta dawo su cigaba da hira tsakanin junansu, zuwa can Saudat bata dawo ba, Momy ta fara juye juye sai gashi ta tashi ko da ta farka gani tayi ɗan tane kaɗai buɗar bakinshi tace  mai, " Wanan yaron bakai bacci ba?" Ko da jin haka ce mata yayi, " Eh Momy ban kwanta ba muna zauna ne da Saudat muna hira, shine ta tashi taje taga likita akan maganar sallamar mu muje gida yau" kasa kunnenta tayi tana sauraron shi tace, " Allah sarki baiwar Allah yarinyar kirki, mutuniyar arziki  ubangiji allah shiyi mata albarka, ka gani ko mai sunan Babana yarinyar daman ni kaina na yaba da hankalinta shiyasaka ma  na zaɓa maka ita matsayin matar da zaka aura, Alhamdulillah gashi kana yau kaima kana ganin hankalinta da natsuwarta da sanin ya kamatanta daman ni na yaba da hankalinta nasan kuma tunda akazo nan asibitin take ta ɗawaini damu koh?" Ya amsa mata da " Eh Momy Hakane wallahi ni kaina ina ganin ƙoƙarinta da kuma jajircewarta akan hakan, Allah yayi mata albarka ni kaina nasan da cewa nayi sa,ar samun matar aure wacce ta fahimceni nima kuma na fahimce ta sosai.." Momy ko da taji haka murmushi tayi, yayi da farin ciki mara misaltuwa ya mamaye birnin zuciyarta.

Momy ɗaga hannuwanta tayi sama tayi tana faɗin, " Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillahi! Nayi matuƙar farin ciki da jikin haka sosai daga gareka, kullum addu,ata itace ubangiji Allah ya haɗe kanku ya ƙara muku son da kaunar junanku ya baku zaman lafiya ya kuma kawo muku zuri,ah ɗayyiba" tare suka ɗaga hannu suna faɗin ameen suma Ameen.




Nasrullah ✍🏻
07055852908

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now