P6

124 3 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®️🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]

         _♡F.J.W.A♡_

https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/

            🅿️6️⃣

'''Saudat, Samun kanta ne, da tayi bayan ta gama cin abinci, yasa ta nufa bedroom nata, domin ta samun tayi, alwala tayi sallah.

Sanan Saudat tasamu tayi, alwala tayi sallah, bayan ta idar da sallah, zaune take kan nadduma, d'aga hannunta sama tayi, tana addu,ah ubangiji Allah Ya cika mata burinta.

Kana ta gama ta shafa addu,ah, tayi tashi daga kan naddumar, ta ajeta nan cikin bedroom, nata inda ta idar da sallah, dawowa tayi  parlour ta zauna.

Zaune take cikin parlour, shiru tayi ta  zurawa ikon Allah idanu,yanzu misalin 4:40pm kenan yamma tayi.

Lokacin tayi wanka taci ado  tayi matuk'ar kyau sosai abun masai wanda ya gani zankad'aziyya.

Zaune take , alamun bud'e gate taji anayi mai guards.

Cikin hanzari ko Saudat ta tashi tsaye domin taga waye daman tasan za,a rina shine.

Ashe abban sadeeq ne ya dawo daga wurin aiki.

Amma abun yayi matukar bata mamaki, yadda taga bai tab'a dawowa gida akasin 5pm ba, dai-dai indai kuma ba wani abu ne ya faru bah?.

Cikin ranta tambayar kanta take anyya lafiya kuwa? Wata zuciyar kuma tacs mata ko da yake bakomai ai daman.

Sauran duka minti nawa?, k'arfe biyar din tayi dai-dai.

Bayan abud'e ma, abban sadeeq gate ya shiga zuwa yayi aje motar a wurin da yake parked motocin shi.

Yana gama parked nata ya bud'e murfin k'ofar ya fito daga cikin motar had'e da jakarshi, kai tsaye ya nufa parlourn gidan.

Saudat, ganin hakan yasa wani farin ciki mara misaltuwa ya mamayeta, rasa abunda zatayi tayi tsabar farin ciki.

Abban sadeeq, bud'e  k'ofar parlourn yayi tare da sallama, Assalamu alakaimu.

Saudat tana tsaye bakin kofar cikin fara,a da murmushi ta amsa mai cikin san sanyar murya, Ameen wsalam habibyna, Oyoyoyo  k'arisawa tayi kusa dashi rungumeshi cikin farin ciki da murna.

Abban sadeeq, ganin wanan bazata haka da kuma wanan tarba haka ta musamman abun yayi matuk'ar bashi mamaki sosai, hakan bai nuna wani damuwa bah cikin murmushi mai karya zuciya shima ya bayyana afuskarshi, ba k'aramun kyau yayi ba da yayi murmushi,sanan ya sa hannunshi d'ayan da babu komai akanta, yana shafa mata liyaliyan, gashinta wanda tai attached dashi.

Kwantawa tayi akan k'irjinsa, yana shafa mata gashin kanta, ba k'aramun dadi hakan take ji ba.

Bayan sun kwashi wasu Seconds a haka, cikin san sanyar murya tana sa bakinta dai-dai kunnenshi kamar zata cije shi,budar bakinta ce mai tayi.

Hubby kawo jakar  kaje kayi wanka ko,gashi ka gaji allah sarki kasha aiki sosai masoyina, kasamu kayi wanka kaji dama-dama,kaga sai ka kintsa kazo muci abunci koh gashi can a dinitable na aje mana, daman kawai kaine nake jiran naga zuwanka masoyina.

Tana rufe bakinta,ta fara sa harshenta cikin kunneshi ta fara lasa kunan cikin salo wani yanayi da yaji ya fara ziyartashi lumshe idanuwa ya fara yi.

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now