P21

35 2 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚📚*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           '''Maman haneef'''

                🅿️2️⃣1️⃣

Shikenan toh naji kuma na amince, zan tafi kamar yadda kace mun, buɗar bakishi cewa yayi, "yauwa ko kefa kin gani, maza ki koma nima sanan zan wuce na koma office ɗina" ta ce " Toh shikenan ai babu komai babu sauran wata damuwa kuma" tana gama faɗin haka tai murmushi, ta kama hanya ta juya zata koma cikin ɗakin da take jinyarsu Abban Sadeeq aciki.

Ganin haka cigaba da kallonta yayi, har sai da ya ga ta koma ta shiga ɗakin baya ganinta sam ko alamunta sanan shima ya gyaɗa kanshi ya ɗan murmusa ya cigaba da tafiya zuwa office, shima yanzu yadda yake tafiyar da alamun sauri yake yi ya manta sam yayi late.

Mamanshi tana can gida tana jiran dawowarshi gida, tasan dai duk lokacin da ɗanta yayi Night Duty asibiti to ranar da sanyin safiya ya ke dawowa gida, amma yau kash!...Saɓanin haka ko meke shirin faruwa? Har yanzu dau bai kai ga dawowa gida ba,Mamanshi tsayawa tayi tsuru ta zurawa ƙofar falon nata idanuwa ko zata ga dawowarshi, taji kafiya meke faruwa ne ya yayi late wurin dawowa?.

Ɓangaren Saudat kuwa haka ta koma cikin ɗakin, ta tararda Abban Sadeeq shi da Mamanshi suna hira, alamun hira tai daɗi sosa ko wanne ka kalli fuskanshi zaka ga alamun fara'ah atattare dashi.

Kallon da tayi musu, ta gansu a haka abun yayi matuƙar faranta mata ranta sosai, ba ƙaramun burgeta hakan yayi ba yadda ta gansu, Ɗa da Uwa suna hira abun gunin ban sha'awa.

Gashi batan son abunda zai katse musu hirarsu da suke, gashi kuma yana da kyau tayi musu sallama, rashin hakan ba daɗi sam ace mutun yazo wuri baiyi ma mutanan dake wurin sallama ba.

Hakanan dai ta daure, ta ciccije bakinta, ta numfasa hannunta na saman chest nata breathing deeply tayi, zuwa can kallonsu tayi tai sallama, suka amsa mata.

Kana ta shigo daga ciki, ta samu wuri ta zauna tana faɗin, "hira kuke kenan?" Har suna haɗa baki suka ce mata, " Eh Wallahi hira muke, daman ke ce abokiyar hirar toh kuma gashi kin raka Doctor Sani kina mai godiyar abubuwan da yayi mana na alkhairi, cigaba da cewa yayi ƙwarai kuwa da gaske hakane nima naji daɗin ganin haka da nai Allah yayi miki albarka matata, kallon juna sukai tayi murmushi, ta ƙariso bakin gado ta kamman hannunshi ta riƙe tana murmushi tare da kissed nashi.

"Honeyna ai duk saboda kai ne da kuma momyna, shiyasa nayi hakan, saboda sam bana son na rasaku, saboda kune ni bana jin zan iya rayuwata muddin idan baku, kun zama mun wata duniya wacce a cikinta nake rayuwa kuma na ke komai na, muddin ba wanan duniyar to nima bani.

Abban Sadeeq cewa  yayi, "Hmm ki dena faɗar haka, ya ke kyakykyawar matata, ba ma hakan zata faru ba insha Allahu, ako da yaushe zamu kasance tare dake domin kasantuwar farin cikinki hubbyna a wannan kyakykyawar fuskartaki.

Murmushi tayi tana faɗin, "Wow Masha  Honey ina alfahari da kai, ina sonka idan ina tare dakai kana sani farin ciki da nishaɗi, kana ɗebe mun kewata duk kasa naji bana da sauran wata damuwa lokacin da muke tare, kai ne fatilar ganina madubin zuciyata kai ne na bawa amanar rayuwata a hannunka makusancin ruhina.

Kama hannunta yayi yana kissed nashi, tare da lumshe idanu yana faɗin, "Insha Allah zan kula dake sosai, zan baki kulawar da wani ɗa namiji bai taɓa bawa wata “ƴa mace ba"

Yana rufe bakinshi tace, " Allah yasa hakan hubbyna" ta tashi daga inda ta ke zaune, tayi kissed nashi agoshinshi muah!.. muah!... muah!...

Mama ko da ke gefensu tuni Bacci yayi awon gaba da ita,daman jia ta daɗe bata samun bacci ba, lokacin da Saudat ta dawo hayyacinta, hankalinta ya komo jikinta kunya ce ta ka mata, ƙasa tayi da kanta saboda ta tuna ɗaki ɗaya suke tare da Mama.

A hankali cikin satar kallo ta ɗago da kanta sama, ta ɗan waiga baya ta diba ko Mama tana kallon duk abunda suke, ko da ta diba gani tayi Mama har bacci tuni ya kwashe ta, ji kake ras gabanta ya faɗi, hannunta tasa aƙirjinta wanda ke bugun uku-uku ta ɗan numfasa, sanan ta saki ranta tana murmushi.

Abban Sadeeq kuwa, yana sane da Mama bacci ya kwasheta shiyasa ma ya biye mata. Yana kallonta mood ɗin data shiga, yi yayi kamar bai lura da ita ba, zuwa can tambayarta yayi, "tawan? Meke damunki ne naga kin ɗan shiga wani yanayi"

"Humm kai dai bari wallahi, in fada maka har gabana ya faɗi karkaso kaji yadda naji ƙirjina namun"

"Ayyah! Allah Sarki, meyasa hakan?"

"Tunawa nayi da Mama kilah tana kallon mu duk abunda mukeyi, da kuma abunda muke cewa"

Duk da dai Abban Sadeeq ba wata cikakkiyar lafiya ya cika ba yana gadon asibiti ne, amma hakan baisa shi ya fashe da dariya ba, kallonta yayi yana faɗin, aini ina sane wallahi tayi bacci shiyasa ma na biye miki.

Duk da dai ya mata dariya bataji haushi ba ko ɗaya, hasalima murmushi tayi tace, " shikenan naji sai kayi shiru karka tada mana da Mama, daga bacci ka ga dai Maybe bata samu hutu ba sai yanzu shiyasa ma nake tunanin haka"

"Alright hakan ma dai-dai ne" zai shiga cigaba da magana ta hannunta ta rufe bakin nashi, tasa hannunta abakinta tana shiiiiiiiiit, sanan yayi shiru  ya haƙura da maganar da zai.

Haka yayi shiru bai ƙara cewa komai ba, hannunta dake bakinshi yasa haƙoranshi cikin salo ya ɗan cijeta, ka ga sauri cikin zafin nama ta cire hannunta tana fadin wai...wai... Tare da yarfe hannunta alamun zafin cizon.

Zata fara mai kukan shagwaɓa yace, "tsaya wannan ne?" Ya taɓa bakinshi tace, "Eh shine"

Humm!...yana murmushi yasa hannushi yana bugun bakin nashi, cikin wasa tace, "nidai a'a ba haka ba nake so ba"

" To kamar ya kenan kike so nayi"

" Shikenan tsaya bari na nuna maka" ta tashi ta matso daf dashi sanan tace, "kulle idanunka masoyi"

Yana rufe idanunshi, sai dai kawai yaji ta kwanto kanshi, da jikinta ba duka ta sakarmai nauyinta ba, tasa bakinta cikin nashi tana tsotsa, shima haka yayi da yaji saƙon kai tsaye ba shiri buɗe idonshi yayi tare da dafa kanta cigaba da mai da mata martanin tsotsar bakin da ta ke mai yayi.

Nishi kawai suke suna tsotsar bakin juna, yayi da taji zai kaima breast nata capka, ta riƙeshi tare da kama hannunshi, sannan ta cire bakinta ta tashi ta koma inda take zaune kan kujera ta zauna, nishi kawai take.

Shima hakan Abban Sadeeq nishi kawai yake yana lumshee idanu, ba ƙaramun daɗin hakan ya fara ji ba, sai gashi lokaci ɗaya kuma ta katse musu jindaɗin.








*Nasrullah*✍️
07055852908

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now