P13

32 3 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚📚*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
          *Sadaukarwa*
               *Gareki*
         Maman Tasleem

                🅿️1️⃣3️⃣

Bai wata-wata ba suna faɗa mai haka, Ya amsa da "to shikenan" cikin sauri ya juya jikinshi na tsuma da karkawa.

Ya koma can wurin motarshi, da sauri ya fara kici-kicin fito da ita, sai da kusa fiddo da ita waje, sai ga nurses ɗin nan da suka ce mai suna zuwa, suna ɗauke da gadon asibitin sun turo shi, wanda ake ɗaukar marasa lafiya dashi? Especially ma wanda rashin lafiyar nasu ya yi tsanani sosai bama su iya tashi ko miƙewa, su yi tafiyar da kansu, Nurse ɗin bakin ƙofar motarshi su ka ci burki da gadon.

Shi kuma lokacin ya riga da ya ɗauko Mamanshi a kafaɗarshi, su ka matso mai da gadon, Abban Sadeeq ya saka ta ciki ya kwatar da ita, sannan nurses din su ka cigaba da tura har zuwa ciki asibitin, su na shiga kai tsaye ɗakin emergency room aka Kai ta ciki, daga bakin ƙofa a nan a kai ma Abban Sadeeq Gate, ya tsaya nan waje.

"Abban Sadeeq ya zauna nan kan kujerun da ke gefen ɗakin, da aka sata ciki, kama hannuwanshi ya yi ya nannaɗe, zama ya yi, yai shiru abunshi shi kaɗai, rasa ma abunda ke mai daɗi ya yi."

Daman wata daga cikin Nurse ɗin, ta je kiran babban doctor bayan sun, umarce shi da kada ya shiga, ya zauna nan waje idan lokacin buƙatar hakan ya yi, sai ga baban doctor ya zo nan  su ka gaisa da shi,  Abban Sadeeq ya faɗa mai abunda ke faruwa doctor ya ce, "Insha Allah kar ka damu, yanzu abunda na ke so shi ne, ka kwantar da hankalinka insha Allah Mahaifiyarka za ta samu lafiya." " Allah Yasa Ameen su ka ameen."

Saudat matarshi da ya bar ta cikin wani hali, wanda ya motsa mata sha'awarta hankalinta ya riga da ya gama tashi lokacin babu abunda ta ke ɓukata kawai ta ji , banda ta ji ya fara buga mata lafiyyan gwatso yana shigarta da Honey J. ɗinsa.

Kawai sai ga shi wayarshi tana ringtone, mantawa ma ta duka bata da wayoyinsu a silent ba, saboda tsaro ba dan tsoro ba.

Ya na zaune kwatsam, sai ga tunanin ta ya faɗo mai a ranshi, ciro wayarshi ya yi cikin aljihunsa na jallabiyar da ke jikinshi, har yanzu dai jikinshi bai dawo dai-dai ba, har yanzu a kiɗime ya ke.

Da ya ɗauko wayarta shi ya samu number matarshi Saudat, ya kira numberta. Saudat ta na zaune bakin gado fuskarta a murtuke, babu ko alamun fara'ah, tsabar abunda Abban Sadeeq, ya yi mata bai kyauta mata ba, ya ɓata mata rai sosai. Haka nan tana zaune wanda ba tai  aune ba kwatsam sai, kira ya shigo cikin wayarta, tsaki mtwssw!...duk da dai bama ta san komawa waye ba? Di ba wanda za tai ba kowa ne ke kiranta ba, illah banda mijinta Abban Sadeeq.

Haka tai kamar ba za ta ɗauki kiran ba, cikin shagwaɓa ta amsa mai sallamar da ya yi mata, kana ta ce mai, "lafiya ƙalau masoyina, kawai wanan fitar haka ko tsayawa ka yi ka faɗa mun ina ne inda zaka amma ya gagara?", Ya ce "Please I'm so sorry dear, wallahi nima kiran na gaggawa ne" , ya faɗa muryarshi tan rawa,“ shiyasa ban tsaya na samu miki maganar abunda ke faruwa ba?".

Ta ce "Subhanallahi me ke faruwa ne dear?", Kafin ya ce mata wani abu, sauke ajiyar zuciya tare numfasawa ya yi  sanan ya ce "Uhmmm in faɗa miki ɗazun nan wallahi sam hankalina baya jikina, shi ya sa ki ka ga ko na tsaya, nai miki magana kasawa na yi, please I'm so sorry."

Ta ce " Dear kar ka damu na haƙura, amma ni wallahi ƙosa na ji meke faruwa ne sai hankalina ya kwanta, saboda ni na san da cewa wannan futar da kai, ba lafiya ba akwai abunda ke faruwa?" "Shikenan kar ki damu za ki ji abunda ke faruwa, amma kafin nan ina son kema ki kwantar da hankalinki".

"Kar ka damu nawan wallahi hankalina a kwance ya ke, tunda na jika na san koma maye da sauƙi insha Allah,"

"Allah Yasa, Ameen suma ameen, ba komai ba ne ba, ɗazun nan kiran da na  gani an kirani ne da wayar momyna, sanna kuma akai mun text message abun ba daɗi" , fashewa ya yi da kuka, ya na faɗin ki bari sai na dawo gida zan faɗa miki duk abunda ya faruwa?," cikin rawar murya kafin kace mai jikinshi ya fara karkarwa ya yi zafi rau, shima jinshi ya ke kamar bai da lafiya.

Sadaut da Abban Sadeeq ke ba ta labari, tuni harta fara ƙwalla tana faɗin  “wayoooooo momy Allah Sarki, Allah dai ya sa kina lafiya?".

Su na cikin wayar rawar sanyi ya fara, jikinshi yana kyarkyarwa, bai ma san lokacin da ya kashe kiran ba, barin Saudat ya yi ta na ta, "Hello! Hello! Hello! nawan pls talk to me manah, jin shiru da tai, ƙwallah ya fata kwaranyo kan kumatun ta," ga shi da ƙari bama ta tambaye shi ba wanne asibiti ne ba? Gashi kuma, ya kashe wayar ta sake kira ba,a ɗauka ba, da ta sake kira  ta ji wayar switch off!....Hankalinta yayi matuƙar ƙara tashi.

Ashe Abban Sadeeq shiru da ta ji ya yi su na cikin waya shima, zazzaɓi ne mai zafi ya rufe shi, suna cikin waya bai ma san ya kashe kiran ba nan ya kwanta kan kujerar da ya ke zaune yana kyarkyarwa da rawan sanyi, Allah ya sa, sai ga wata nurse ta zo wucewa ta wurin ta ganshi aiko shi ma nan take aka bashi gado aka sa mai drip, tare da allurai

Saudah, tana zaune sai trying number shi ta ke bata shiga a kashe, ji ta yi sam ba za ta iya zama ba cikin gidan, tashi tayi tai maza ta gyara jikinta ta sanya kaya, ta fito daga cikin falon ta sa mabuɗin ta kulle ƙofar.

Sanan ta nufa parking space, cikin sauri sai gashi ta ƙaraso ta ɗauki motarta wacce ya siya mata tun tana budurwa, a gidan su ta na hawa.

Hanzari ta yi ta buɗe murfin ƙofar motar, sannan ta shiga ciki, da sauri tsigar jikinta na tashi, ta jawo ƙofar ta rufe, sai sa key motar ta ke ashe tsabar saurin da ta ke , ba dai-dai ba ne ta ke sawa ba?. Sanna ta ɗauko wayarta ƙirar android ta kunna flashlight, ta haska u da ta ke sa key ta ga ashe ba dai dai ba ne inda ta ke sawa ba, ta dafa kanta da hannunta kash!......cikin ranta tana faɗin “wai meke damuna ne, Oh ni ya su".

Sannan ta dai-daita, ta saka keyn motar dai, ta tada motar, tayi reverse, ita ma kamar shi ma cikin sauri ta fizgi motar ta fara  tuƙi, haka ta fita cikin gidan da sauri daman kofar gate din nasu, a buɗe ta ke , ko ɗazun da Abban Sadeeq zai fita da ya fita bai tsaya ya rufe ba kawai titi ya hau ya cigaba da tuƙi.

Itama haka ta na fita ta hau kan titi ta ci gaba da tuƙi, cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga ta asibitin ita ma, duk da dai ba ta tambaye shi ba wane asibitin ne ba ya kai momyn.

Ta shiga cikin asibitin da motarta, ta nufa parking space ta yi parking na motar, ta fito cikin sauri, ta nufa cikin asibitin ta na shiga asibitin ta tarar da Nurse guda biyun nan na ɗazun  har sun gama abunda sucke sun dawo bakin aikinsu, tai musu sallama, su ka amsa ta ce musu "dan Allah ƴan uwana tambaya na ke ?" Su ka ce mata "Allah ya sa mun sani yar uwa", buɗar bakinta ta ce mu su insha Allah ma kun sani na san inda ya zo baya wuce nan asibitin kawai ina so ne kafin na ƙarisa can ciki nayi confirming  nan ne?, Wani mutum ɗazun nan ba jimawa bai zo da wata mata ba haka tsohuwa ce ta kwana biyu", Nurse ɗin nan haɗa fuska su kai su ka kalli junan su, sanan suka ce “Eh nan ne, baiwar Allah meke faruwa ne?", Ta ce "to shikenan bakomai na gode , shi mijina ne ni matarsa ce." Su ka ce mata " Allah sarki, wallahi ɗazun muna zaune kawai kamar yadda kika gan mu  ɗin nan, shima kamar haka ya zo ya same mu a haka ya faɗa mana mu ka ce mai muna zuwa, mu ka je mu ka ɗauko gado shi kuma ya koma can motarshi yana ƙoƙarin fito da ita da ga cikin motar."

Haka suka ci gaba da bata labarin abunda ya faru, da ya zo nan asibitin, ƙwallah ta fara sauran ƙiris ta fara kuka!.... ɗaya daga cikin Nurse ɗin ta zo tana lallashinta tai hakuri ta ja zuwa cikin asibitin ta nuna mata inda akwai kwatar da Momyn nasu, babu halin shiga sai ta samu kanta zuwa anjima ko da safe, sannan kuma shivma mijin nata ta nuna mata ɗakin da aka kwantar da shi, a nan Nurse ɗin tai birki ta bar ta ta dawo bakin aikinta.




Share & comments
Fisabilillahi
07055852908
★★★★★★★★★★★★★★★

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now