P27

32 1 0
                                    

🌼  *WANE YARO* 🌼

    
               BY
       NASRULLAH

®🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚📚*
[Ƙungiya Domin wayar da Kan mata, Farin Jini writer's domin ci gaban Mata.]

     *♡°F .J .W .A°♡*
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
        
              *Sadaukarwa*
                   *Gareki*
           '''Maman Haneef'''

                🅿️2️⃣7️⃣

Abban Sadeeq tsaye yake bai kai ga yanke shawarar kwanciya zai ba, ko zauna zaiyi ya huta ba, sai ji yayi an kamashi da hannu ana ƙokari zaunar dashi, sakin jikinshi yayi aka zaunar da shi domin ya huta, bakowa bane yayi hakan face matarshi farin cikinshi Saudat.

Ana gama zaunar dashi za,a  juya atafi kallon da zai yaga ai Saudat ne matarshi kallon junansu sukai tare da yiwa juna murmushi mai narkar da zuciya.

Sanan Saudat ta wuce taje ta cigaba da aikin shigar da kayan cikin mota tana saka wasu cikin boot ɗin motar, haka tai ta zuwa ta kai komo, saboda ita macace  ma saɓanin ba namiji ba sai faman tiɓi tiɓi take akan hanya, saboda kayan na da yawa dai dai gwargwado.

          ★★★    ★★★

Abban Sadeeq kwantar dashi saudat tayi ya samu hutu , har zuwa  yanzu kwance yake bai kai ga tashi ba,har saudat ta kammala shigar da kayayyakin su duka...

Sanna tazo daf dashi inda yake kwance dafa jikinshi tare da dafa jikin gadon, budar bakinta ce, " Hubbyna Please wake-up,na riga da na kammala shirya mana komai yanzu kawai tashi zakai muje mushiga cikin mota, ni sai na taho da momy kaji pls bbyna nasan kagaji amma daurewa zakai." Wani ɗan karen bacci ne mai daɗi ya so ɗauke Abban Sadeeq wanda har ya fara saka shi cikin cakwakiyar gyangyaɗi, wanda shi mai bacci, ko in cemai gyangyaɗi akwai shi da uwar gaddama, ace mai bacci yake yace shi, "a'a ba bacci yake ba!" duk abunda ake yana saurara kuma yana ji...

Ta dashin da  saudat tayi bata ranshi yayi ya mirtike fuska, alamun bacci daɗin katse mai bacci da ya soma ɗibarshi tayi bah, baccin ya fara mai daɗi kenan Saudat tazo ta tada shi, ita kawai ba ruwanta abunda ke gabanta shi take....

Ko da ta tada shi ta lura yana cikin mood fuskarshi wani iri, kallonshi tayi da dara daran idanuwanta masu matuƙar kyau da ɗauke hankalin mutum, haka dai ta cigaba da kallonshi tana murmushi cikin sansanyar muryata fara, "Please wake-up I'm sorry bbyna, naga lokacin yayi nena kammala aikin shigar da kayan gwara mu wuce tun yanzu,in yaso mukaje gida komai kenan agida muke ba kamar nan ba......"

Jin muryata cikin yanayi mai daɗi yasaka shi sakin fuskarshi wacce take mirtike da....

Ƙarisa tashi yayi bismillahi daga gadon da yake kwance itama momy haka bacci ne ya ɗauketa amma ita nata bai fara nauyi ba kamar na Abban Sadeeq, tashi yayi ya wuce can parkin space bai kai ga buɗe motar ya shiga ba nan ya tsaya jikin motar ko jiran me yake?, Can sai ga Saudat ta taho riƙe da Momy suna tafe, ko da ta kariso inda yake tsaye binshi tayi da idanu harya buɗe kofar kujerar baya ta saka Momy cikin sannan ta mai da ƙofar ta rufe.

Ko da ta kalleshi cemi shi tayi, "Please Hubbyna jiran me kake kuma, baka shiga mota ba? Gashi ni har nazo na shigar da Momy ciki pls ka shiga kaji bbyna, idan ma so kake kayi mana driving pls nidai banso ka tsaya nan kazo mushiga muje kaji pls!.."

Kallonta ya yi suka haɗa ido yayi murmushi yace, " Daman nima ai ba kowa nake jira ba face, tauraruwata ɗaya tilo tamkar da dubu cikin mata acikin mata, wacce ba kowan kowa bace ba sai ke farin kina, kai hannunshi yayi jikinta tare da rungumeta ajikinsa tare da kwantar da kanta bisa chest nashi, yana mai da numfashi, shafa gashin kanta ya yi baki wulik, wanda yayi matukar burgeshi  da kuma jan hankali shi lumshe ido yake.

Babu wata gargada ko gaddama yana jawota jikinshi ya rungumeta, bata ce mai uffan ba hasalima itama daɗin hakan tashi ƙwara kwanta da kayin nata tayi a ƙirjinshi da kyau sosai domin ba karamin daɗin hakan takeji bah, sai da suka kwashi tsawon mituna biyar a haka sannan Saudat ta zare jikinta cikin nashi tace, " bbyna pls yanzu kazo muje, Dan Allah pls!"

Ta ɗan ɓata ranta tana magana, saboda itafa wallahi ta ƙosa tabar wannan asibitin, yadda kasan ana tsikarinta ana mata allura haka takeji ajikinta yanzu kuma duk ta tsanai ma asibitin.

Murmushi yake yana kallonta yace, "I'm sorry honey, shigar mota muje, amma sai kin sakin fuskarki sannan" Saudat ko da jin haka kallonshi tayi suka haɗa idanu, wani zazzafan murmushi tayi mai sannan ta sumbace shi a kumatunshi ta wuce ta zagaya wurin ƙofar driver,da alamun dai itace nan zatai tuƙin nan ba Abban Sadeeq ba!...

Cikin fara,a da annuri a fuskarshi faɗi yake, " shiga ki tuka mu muje koh?" Jin hakan daga gareshi yasaka ta buɗe kofar motar ta shiga sannan ta mai ƙofar ta rufe, shima haka ya buɗe kofar ya shiga sannan ya mai da ƙofar ya rufe.

Ko da su biyun dukansu suka gama shiga cikin motar zaune suke ciki, suna kallon junansu Saudat kasa haƙuri tayi sai da ta sake sumbatar kumatunsa sannan tasaka key, ta kunna motar diba bayanta  tayi ta fara revose da motar duk da dai Abban Sadeeq na kalle mata bayanta itama haka.

Tana gama revose ɗin ta fara driving nasu cikin harabar asibitin nan suka zo bakin ƙofar get na asibitin ko da zuka zo Saudat horn ta matse, sai ga mai guard na ƙofar Asibitin su bayyana, suka buɗe musu ƙofa suka fita daga cikin harabar asibitin baki ɗaya, wow masha Allah Allah yayi su Saudat   an fito daga cikin asibitin, suka hau kan titi ta tuƙasu har zuwa gida, basu wuce gidan hajiya ba Momy abban Sadeeq sakamakon itama ba cikakkiyar lafiyar gareta ba kuma ɗan sauƙi taji, hakan yasaka suka wuce gidansu su Saudat gabaki ɗaya.

Mai gadin get  ya buɗe musu suka shiga daga cikin harabar gidansu, parking space Saudat ta nufa dasu ko da ganin haka mai gadin gidan nasu ko da yaga haka cin sauri mar maza ya je ya buɗe musu ƙofofi suka fito lokacin da Saudat tayu parking ɗin motar.

Sannan ta buɗe mai boot, tare da cemishi ya kwaso musu kayan duka ya shigar musu dashi daga ciki, su zasu wuce daga ciki Saudat tana gama faɗin haka ta kama hannun Momy suka nufa ƙofar parlourn  gidan...

Shima haka abban Sadeeq yana biye dasu abaya, har su kazo bakin ƙofar parlourn Saudat ta ɗauko key acikin jakarta tasa ta buɗe musu sannan suka shiga daga ciki.

Suna shiga Saudat tsabar murna da farin cikin da take ciki ɗaga hannun tayi sama tana faɗin, "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mamallakin mamallaka wahidul qahar ameeen." Sannan suka ɗaga hannuwansu a tare sukayi addu,ah Ubangiji Allah Ya karesu da kariyarshi ya tsaresu da tsarewarshi duk wasu masu binsu da sharri li-ilafi ƙhuraish aniyarsa ta bishi.

Abu kamar wasa yau 1 week kenan, sanan Saudat ta ɗauki Momy ta kaita cikin ɗakinta inda zata zauna kafin lokacin komawarta can gidanta yayi saboda ita sambata son zama acikin gidan ɗanta ba tun yau ba Abban Sadeeq yana son hakan tazo su zauna tare a gida ɗaya amma taƙi amincewa, shima wannan zuwan da tai harda ƙarin bata lafiya ne yasaka.

Ta kaita bedroom nata, ta nuna mata tare da nunnuna mata toilet da kuma bathroom,  sannan Saudat ta fice daga cikin ɗakin ta nufa kitchen domin ta samu da ɗan haɗa musu abunda zasu ci na anjima tunda dai tasan duk wanda tace mishi ga abinci buɗar bakinshi Alhamdulillah zai ce mata.



Nasrullah✍🏻✍🏻✍🏻

WANE YARO !!!Where stories live. Discover now