3&4

150 6 0
                                    

🌺🌺🌺🌺

*JOINING TWO DIFFERENT THINGS*
                   '''Gamin Gambiza'''
                        🎍🎍🎍

                     *BY*

           *UMMU SUMAYYA*
                   #Bintubay

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏼*

🅿️3️⃣➡️4️⃣

"Tsinanniya irin tsiya watakan bak'in ciki kike mana karmu k'aru dake ko to karya kike sai munje hajji dan auren ki da Alhaji Buba ba fashi ko gawarki ne sai ankai inyaso inyagama abunda zaiyi dake a kaiki makwancin ki" tana maganan tana dukanta da hannu tana kuma haurin ta da k'afa saida tamata lilis taga ko k'wak'waran motsi batayi tamik'e tana haki tajuya tana fad'in "y'ar banza irin tsiya wacce basu gaji arziki ba mtsss maza kitaso kimin wanke wanke kinbarmin gida k'uda nata  bi!"
Tana kuka tamik'e dak'yar tafuto ko ina na jikinta ciwo yake mata tabbas tasan tayi bankwana da farin ciki daga lokacin data shiga gidan Alhaji Buba, ruwa tad'iba tana wanke wanken tana kukan tausayin rayuwar ta  da take acak'ud'e kawai takeyi dababu mataimaki sai Allah,
Jummai ne tasake futowa tana fad'in "baki dakuba kenan har kike k'ak'alo kukan munafurci ai kad'an na miki wallahi muddun kika k'ara kwatan ta bin namiji saina bud'e ki nasa miki attarugu inga yanda zakiyi iskancin inbanda zamani ma yo yaushe mace take fira da namiji har tabishi hmm" tayi k'wafa tana zama akan kujera y'ar tsugunno tana hararan ta,
Gum tayi da bakin ta taci gaba da wanke wanken sai kukan zuci datake, saida ta kammala kaf tad'auki tsintsiya da niyyar shara suka tsinkayi miryan wasu tsofaffi na fad'in
"Gafaran ku dai masu gida"
Jikin Jummai na kyarma ta watsa ma Nafeesa wani irin kallon dayasa tashige d'akin ta babu shiri, 
Su ukune d'auka da akwati na roba da alamu dai sababbine guda uku da d'an kit,  da fara'a Jummai take fad'in
"Lale marhabin kune da maraici haka zuwa babu sanar wa marhabin lale da zuwa da abun arzki ku zauna inkawo muku ruwa!"
Tafad'a tana shimfid'a musu wata yaloluwar tabarma da duk tazare tanufa madafa da niyyar d'ibo musu ruwa,
Saida suka sauke akwatinan sannan d'aya daga cikin tsaffin tace "a'ah basai mun zauna ba Jummai dama Alhaji ne yace mu kawo sannan ga wannan kud'in lalle da kitson amarya ne"
Jiki na kyarma Jummai ta fito daga madafa ta amsa kud'in ta tofa miyau ahannun ta tafara irga kud'in saida tagama tsaf taga dubu hamsin tad'ago ta rangad'a wata gud'a tana fad'in "Kai gaskiya Nahisa tayi goshi irin wannan arziki haka kuyimin godiya wajen Alhaji ayirriiiiiii" tasake rangad'a gud'a cike da farin ciki da murnan samun wamnan mak'udan kud'ad'en tabbas sun isheta tayi wata tana cin maikyau tanashan mai kyau ga kaya duk saida akwatinan zatayi tahad'a kan kud'ad'en ta,
Godiya tasake musu sannan suka juya suka tafi suna jinjina son kud'i irin na Jummai.
Tana ganin futan su wuf tafara d'aukan akwatinan zuwa d'aki watsa watsa tama kayan zannuwa guda goma shabiyar gyale hud'u hijab biyu sai uban kayan kwalliya wanda ita inbanda kajal ma bata san komai aciki ba takalmi da jakukkuna guda hud'u sai alkur'ani da tasbaha,
Jikinta na wani irin kyarman sauri tajanyo wani buhun taki green takwashe zannuwa goma shabiyu tabar uku dasuke d'inkakku takwashe duka gyaluluwan tabar hijab d'aya jaka da takalmi d'aya tabari kayan kwalliyan kuwa duka ta had'a musu kai hijab tasaka tafita waje dasauri babu kowa duk antafi gona kasantuwar safiya ce kuma farkon damuna tana tsaye taga wani almajiri tace yazo yad'aukan mata kaya,
Dakyar ta kulle bakin buhun tad'aura ma almajirin akai sannan suka futo tare bagazan bagazan take tafe gudun karsu had'u da Rabe yarage mata buri! kallo d'aya zaka mata ka gane bata da gaskiya sun yi tafiya sosai kafin tasamu mashin naira hamsin taba almajirin tahau mashin d'in bayan tagaya mai Turunku zai kaita batare dataji kud'in taba mai mashin yaja.

Duk abunda ke faruwa tana kallo ta kafan k'ofan ta k'uryan d'akin takoma tana sake fashewa dawani irin sabon kuka cikin rashin mafita da tunanin shin ita menene tushen ta suwaye asalin iyayenta ahannun su ta taso bata san kowa nataba gashi zasu aurar da ita ga tsohon mutun dabe k'aunar haihuwa Alhaji Buba yana auran yara k'anana y'an shekara 13 dazarar yarinya tasamu ciki zai koro ta gidan iyayen ta,  dayawa yaran dayake aure wajen haihuwa suke mutuwa, Wasu kuma su samu cutan yoyon fitsari suzama abun gudu cikin y'an uwansu da al'umma gaba d'aya kauyukan andaina bashi aure duk kuwa da kud'in dayake sauke ma iyayen yara inyaga d'iyarsu yana so ko shekara ba'aiba ya auri k'awar Nafeesa Tani wacce tana samun ciki yakorota da takardar sakinta uku yakuma fara neman auren Nafeesa dan tun abikin su da Tani miyan shi yatsinke akan yarinyar dan akwai diri kuma kallo d'aya yamata yasan zata bada wuta agado irin macen daya jima yana nema kenan ba b'ata lokaci yafara bincike akanta saida yatabbatar bata da galihu sannan yafara sauke ma Kawu Rabe kud'i ba b'ata lokaci yabashi auren Nahisa akasa rana sati biyu duk kuwa dayasan tanada wanda suke soyayya jira yake ta kammala primary school ayi maganar aure dan anjima dayin baiko amma yakauda zancen Saminu ak'arshe agidan mai gari suka rabu da iyayen Saminu bayan yabiyasu kud'in baikon su,  hawayen fuskarta tashare takwanta tana lissafin yau sauran kwanaki biyu kenan akaita gidan mutumin data tsana sama da komai aduniya shike nan itama takusan mutuwa kota kamu da cutar yoyon fitsari wani irin sabon kukane ya kufce mata ta toshe bakinta tanayi harda shashsheka shike nan bazata tab'a jin d'ad'in rayuwa ba shikenan rayuwar ta atambal tamb......,
Wani irin bankad'o k'ofa kawu Rabe yayi yana kallon ta yana haki kamar wanda yayi gudun fam falak'i yace "ina Jummai?"
Jikina tsuma ta tashi zaune tana zare idanu tace "ban san inda ta tafiba"
Wani irin k'wafa yayi yajuya yasake banko k'ofar fale falen,
Takure kanta tayi atsakanin cinyoyinta tana sake fashewa da kuka,

**************

Kusan five minute da d'aga kiran amma kowanne yakasa tanka ma d'an uwansa tsaban yanda kowa kejin kanshi shi wani ne,
Wani irin ajiyar zuciya Lubaila tasaki tana dafe zuciyar ta cikin jan aji da gwalli tace "Am Lubaila Shehu who's on the line?"
Saida yad'an sauke ajiyar zuciya shima kamun yad'aura k'afa d'aya kan d'aya yace "i know kin san waye yake magana if har yanxu baki gama jan ajin ba i will keep my self"
Murmushi tasauke tana wani irin juya idanun ta tayi akan makeken gadon nata dan tun safe da sakataren shi yagaya mata yafa amsa number ta take tsumayin shi har yammacin nan kuwa idanu tad'an lumshe kamun tace "oh am so sorry i saw your massage yesterday Safwan right"
"Hmmm"
Yace yana kallon yatsun hannun shi saikuma yace "any where menene amsan tambaya ta?"
Murmushi yak'i b'acewa afuskarta tace "amsar tambayar ka shine na amince dakai Allah yatabbatar"
Kanshi yashafa yanajin wani irin happy yace "Amin ya rabbi hope babu wani agabana"
Dariya tayi wannan karon tace "gaskiya kam babu kowa ka kasance mai matuk'ar sa'ah"
"Masha Allah to yanzu kisamun lokaci inxo muhad'u dan ni am serious aure nakeso nayi in the next one month hope you're ready"
Cike da farin cikin dacen da tayi tace "any where sai kazo ma tattauna maganan nasan Dad d'ina ashirye yake baka da matsala"
"Ok tell me something"
Saida takalli wayar sannan tace "like what"
Murmushi yayi yace "ok forget about it letter"
"Okay bye" atare sukai cutting wayar.
yanajin shi as happy wani irin dadda d'an iska na shigan shi,  Murmushi yasaki yace "finally zan cika burin Dad d'ina soon insha Allah" lumshe idanun shi yayi yana hango fuskar Lubaila ahankali yafurta "she's cutie at all"

***********

Wani irin tsalle ta daka akan makeken royal bed d'in dake barazanar cinye k'aton bedroom d'in,  cike da farin ciki maras misaltuwa lallai tacika mai sa'a Safwan Bashir *Director of NARJESA CORPORATION* burin ta na gab da cika matuk'ar ta auri Safwan zata fantama aduniya taje k'asar data so tabbas tama k'awayen ta fintinkau tasamu young millionaire kamar yanda suke kiran shi a company,  mik'ewa tayi takarisa gaban makaken mirron dake d'akin tana kare ma kanta kallo tana murmushi mai cike da yarda dakai tajuya tasake juyawa tace "tabbs Allah yayi halitta anan kota ina nacika mace,  macen da duk wani lafiyayyen namiji zaiso yamallaka ya kasancewa da ita tabbas inkana da kud'i saika so kazauna a mummuna kud'i sunyi shiyasa nake matuk'ar son ku,  tak'arisa maganar tana sakin wani irin dariya cike da nishad'i
Dasauri tafuta daga d'akin tun daga downstairs take fad'in " beautiful Mom where are you kiji da dadda'an labari Safwan Bash........" Wani irin had'iye sauran maganan tayi saboda abunda tagani a d'akin Mom d'in dasauri tafuto afujajan tana yamutsa fuska cike da takaicin Mom d'in.........✍🏼

*This book is for sale N300 for normal paid 500 for vip 1000 for special group inda zamu kammala book d'in in 3week*

JOINING TWO DIFFERENT THINGSWhere stories live. Discover now