19&20

155 8 0
                                    

🌺🌺🌺🌺

*JOINING TWO DIFFERENT THINGS*
                       "'Gamin Gambiza"'
       🎍🎍🎍

             *BY*

      *UMMU SUMAYYA*
               #Bintubaby
https://www.wattpad.com/user/Bintubaby

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏽*

                      *LAST 🆓 PAGE*
                1️⃣9️⃣➡️2️⃣0️⃣

*how to subscribe 👇🏽*
300 for normal group
500 for VIP group
1000 for special group
Via Lawal Shamsiyya
Eco bank 4210014214
And send the evidence of payment via
07017296839

Da sauri ta tare ta arud'e tafara girgizata amma babu alamun numfashi d'agowa tayi daidai Saminu yak'araso wajen hawaye shab'e shab'e kallon tuhuma tamai tana wani irin  zare idanu tafara k'wala kiran "Karima Karima kawo ruwa dasauri" tafad'a da d'an k'arfi,
Saminu ko  duk'awa yayi still yana kuka idanun shi akan Nahisa dayaga tayi mugun rama fuskan ta akumbure tabbas Allah yayi zasu kuma had'uwa shin menene ke rufe acikin tasu rayuwar firgigi yayi saka makon muryan Nahisa dayaji tana fad'in "ashe idanuna zasu sake ganin ka ashe zuciya zata sake jin bugun numfashin ka ashe rai da ruhi dasuke gayamin zan sake ganin ka ba k'arya sukai ba meyasa meyasa meyasa nasake ganin ka alokacin da hakan baida wani amfani agaremu?" Tafashe dawani irin kuka mai cin rai,
Gaba d'aya kan Fiddert ya kulle sun san juna kenan gyad'a kai tafarayi tuna Alhaji yace mata Saminu d'an garin sune kenan sunyi soyayya ada kenan hmm tab'e baki tayi tana kallon su gaba d'aya kamun ta mirtuke fuska tace "Saminu jeka bud'e min get zan futa ne"
Tana k'arisa maganar tad'aga Nahisa suka k'arisa parking lot d'in, itako Nahisa tana kuka tana waigen Saminu dake durk'ushe kamar andank'wafa shi awajen Karima dake tsaye takalle shi cike da tausayi ganin yana kuka tace "kayi hak'uri kamaida lamuran ka ga Allah saikaga komai yazo maka cikin sauk'i"
Asanyaye yakalleta yana share hawayen fuskar sa jiyake duniyar na juyawa dashi meyasa yasake ganin ta bayan kullun addu'ar sa Allah yacire masa ita mikewa  yayi yakarisa wajen get d'in danshi Duke jira dak'yar  yabud'e get d'in yana kallon Nahisa dake ta kuka kamar ranta zai futa kwata kwata baima lura da wata uwar hararan da Hajiyar ke jefo maiba.

Koda sukaje super market d'in amota Fiddert takulle ta tashiga ciki  tad'an jima kamun tafuto tashiga motar cikin tsawa tace "wallahi idan bakimin shiru ba zakisha mamaki na kuma daga yau sai yau muddun kika sake nuna kinsan Saminu saina maida ma mutumin nan n k'auye ke wawiya kawai narufa miki asiri kina neman ki ballatsa min nawa mtsss" tayi maganan cikin hargagi kamun taja motan atsiyace
Wanda hakan yasake firgita Nahisa tayi gum da bakin ta tana runtse idanun ta harsuka kawo bata saniba saida taji ance "fito" jiki na kyarma tafuto daga motar tana waigen inda taga Saminu yafito amma babu shi ba labarin sa harsuka shiga ciki waige take amma bata ganshi ba wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata bata damu data share ba haka  tazauna Fiddert dai sai aikin hararan ta take amma ita batama san tanayi ba.

yau wayar Dad ne tafarkar dashi akasalance yad'aga wayar yakara akunne dasauri yatashi zaune yana murza idanu yace "to ganinan zuwa" yafad'a yana kashe wayan sauka yayi agadon yanajan tsaki mik'a yayi cike da gajiya ga barcin be ishe shiba wayar shi yad'auka yabi ta k'ofar baya driver na hangoshi yak'araso yana fad'in
"Yallab'ai barka da safiya" yayi mgnr yana d'an rage tsawo,
Fuska babu walwala yace "barka dai muje airport Dad yana can yana jira" yak'arasa maganar yana nufan mota,
Da sassarfa driver yak'arasa yabud'e mai shima yazagaya mazaunin driver yatada motan yana horn cikin sauri aka wangale musu get.

Yau tun asuba Zainab take ta safa da marwa bata kitchen bata side d'in Dad saida ta tabbatar komai ready tagama barbad'e barbad'en ta sannan tafad'a wanka bayan tafuto tashirya cikin wani tsinannen halp gown me superget hand dayayi matuk'ar matseta kamar tayi nishi ta yage wankan turare tama kanta kamun tad'an jujjuya agaban mirror tasaki wani irin cool smile tace "you're highly welcome mataimakin cikar burina" sweet tad'auka tajefa abakin ta kamun tazauna cike da farin ciki da nishad'i horn taji dasauri talek'a ganin sune yasa taje main parlour tatsaya ak'ofa Safwan ne yafara shigowa da trolley guda biyu kallo d'aya yamata yad'auke kai yana neman tsari daga sharrin ta idanu yulumshe jin masifaffen k'amshin ta na shigan shi ihun tane yasa yabud'e idanu dasauri ya aje kayan yashige side d'in shi yanajan tsaki gadon shi yafad'a yanajin wani irin yanayi na buk'atuwa na shigan shi idanu ya lumshe yana tattaune lips d'in shi cike da tsanar matar Dad.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 08, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JOINING TWO DIFFERENT THINGSWhere stories live. Discover now