15&16 ➡️17&18

124 5 0
                                    

🌺🌺🌺🌺

*JOINING TWO DIFFERENT THINGS*
                              "'Gamin Gambiza"'
       🎍🎍🎍

             *BY*

      *UMMU SUMAYYA*
               #Bintubaby
https://www.wattpad.com/user/Bintubaby

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏽*


                         🆓 *PAGE*
                1️⃣5️⃣ *&* 1️⃣6️⃣  ➡️ 1️⃣7️⃣ *&* 1️⃣8️⃣

Babu Nahisa ba labarin ta acikin d'akin cikin sauri ta k'arisa shiga tad'aga zanin gadon amma babu almun ma akwai me rai cikin d'akin wurjanjan tafito tsakar gidan inda takalli Hajiya Harisa dake ta zuba ma y'ay'an ta koko akofuna dan itace me k'anann yara dan tana haihuwa ma murya na makyarkyata tace "Hajiya bakiga amaryar Alhaji ba?"
Arud'e ta waigo dan atunanin ta wani abun takuma yi tace "innalillahi metakuma yi? Badai tak'arisa shiba" tafad'a jikinta na d'an tsuma,
"Nabarta ad'aki ne nadawo babu ita bakiga futar taba?"
Ajiyar zuciya Hajiya tasauke kamun tace "Alhamdulillah gwara data tafi can sushawo ta dan ni bazan iya da bala'en Alhaji ba dan bake kad'ai abun zai shafa ba harda mu" tak'arisa maganar tana wani irin mere baki kafun takoma kan aikinta tana y'an wak'ok'inta cike da nishad'i,
Kai kawai Hajiya Tala ta girgiza kamun tajuya d'aki cike da tausayin Nahisa dan tabbas sai andawo da ita gidan shiru tayi na d'an lokaci kamun tad'anyi k'wafa tazauna batare data karya ba.

Nahisa kuwa fuskan ta talullub'e ruf take tafiya bama tasan Inda take jefa k'afan ba tana tafe tana share hawayen da tasan da suna k'arewa da NATA sun k'are ahaka tak'arisa gidan zuciyar ta na wani irin lugude tafad'a cikin gidan batare da sallama ba kallon d'akin nada tayi kamun ta waiga atsoroce jikin tan yad'auki kyarma taduk'a awajen tana had'e hannayen ta biyu hawaye nazuba a idanun ta dasuka k'ank'ance tama kasa magana tsaban yanda bakin ta ke kyarma,
Ita kanta Jummai jikin nata kyarma yake kawu Rabe ne yalek'o ganin yanda jikin Jummai  ke kyarma idanu yazaro ganin Nahisa murya na makyarkyata yace "Na.....Nah.....Nahis....sa"
Murya adishe cikin kuka gunun ban tausayi tace "kayi hak'uri Kawu karka kore ni dan girman Allah"
Afusace Jummai tace "inbai kore kiba kijawo mana bala'e muna zaman zaman mu to wallahi k'arya ne ton kan ma asan kinzo nan ki goga mana masif...." Bata gama rufe bakiba taji sallama ai dagudu tashige d'aki Kawu  yarufa mata baya da wani irin sauri suka sama d'akin kuba jikake shiru kamar ba wata halitta agidan sai shashshekan kukan ta dake tashi atsakar gidan,
Wata farar mata ce tashigo gidan bakin ta d'auke da sallama tana k'are ma tsakar gidan kallo, kyakkyawa ce wacce kallo d'aya zakai mata kasan hutu dajin dad'i dakuma kud'i sun zauna mata wanda hakanne yab'oye ainihin shekarun ta kallon Nahisa dake kuka tayi tana sake duban gidan kamun tace "INA masu gidan inata sallama kinyi banza dani ko kurma CE ke?" Tak'arisa maganar agadaran ce,
Cikin kuka tace da dasasshiyar muryan ta "kiyi hak'uri"
Kallon sama da k'asa tama Nahisa kamun tace "masu gidan fa?"
"Suna ciki" tafad'a atak'aice daidai nan aka bud'e k'ofan d'akin Jummai tace "muryan wanakeji kamar Aunty Fiddausi?" tafad'a tana rik'e baki cikin mamaki kamun tad'aura da fad'in "maraba marhabin lale yau agari shigo shigo" tafad'a tana bata hany'a,
Baki tawani tab'e kamun tace "lallai duniya yanzu kece kika koma haka Jummai koda shike zaman k'auye babu dad'i kam hmmm" takwand'e baki tana k'arisa shiga d'akin,
Kawu Rabe dake rab'e agefe kamar wani almajiri yagaisar da ita ta amsa ayamutse tana mai wani irin kallo shikuma yasa kai yafuta d'akin Nahisa yashiga yace tabiyo shi aiko da sauri tabi bayan shi.

Baki Fiddert ta tab'e tana k'are ma d'akin kallo da ruwan da aka aje mata wanda tabbas tasan matuk'ar tasha shi saita amayar da dik abunda taci da safiyar kai tajinjina kamun tace "Jummai wai koda yaushe nazo gidan nan ayamutse nake ganin ki kodai bakyajin dad'in auren nan ne?"
"Uhm kedai bari kawai abubuwa sai ahankula saidai Allah yasa mudace"
Da amin Fiddert ta amsa kamun tace "wallahi kinsan dalilin zuwa na k'auyen nan kuwa?"
Da sauri Jummai tasake matsowa kusa da  ita da sonjin  abunda zata fad'a tace "a'a kam ai saikin fad'i ko aikatau aka samu intura wannan tsinanniyar data d'auko mana abun fad'i ak'auyen nan"
Cikin takaici Fiddert tace "dad'i na dake wutar ciki ba wannan ba bazawara nake nema maras wayau wacce duk abunda akace tayi zatayi batare da bin kwakk'wafi ba"
Shiru Jummai tayi kamun tace "bazawara?"
Yamutsa fuska Fiddert tayi kamun tace "kud'i zan biyaki naira dubu d'ari biyu cash matuk'ar kina da tabbacin wacce zaki had'amun sannan idan komai yatafi daidai zan k'ara miki naira dubu d'ari uku dubu d'ari biyar kenan"
Wani irin zaro idanu Jummai keji kamun tace "kanta akeso kome?"
Tsaki Fiddert taja tana hararan ta tace "wani yaron yayan mijin k'anwata ne yace anema masa bazawara zai aura kin san zawara sunada hankali"
Shiru Jummai tayi tana tunanin kodai Fiddert tafara yankan kaine dasauri ta girgiza kanta tuna inma yankan kanne yayan tama yanayi kenan dan Fiddert yayan ta take aure to kodai kodai dasauri ta ce "wacce kika gani atsakar gidannan bazawara CE auren ma bai mutuba taso kashe mijin shine tagudo idan badamuwa mezai hana kitaimaka idan muka kashe auren sai inbaku ita kutafi duk yanda kukeso saikuyi da ita"
Wani irin kallon baki da hankali Fiddert ta mata kamin tace "shekaran ta nawa har amata aure taso kashe miji sokike muma idan akayi auren takashe shi ko yaya kinga idan bazakimin hanya ba zan kame kaina dan ma ina son sirrine yasa nazo wajen ki amma badan hakaba ina yaushe can gidan zanje ai"
Dasauri ta rik'eta ganin tana k'ok'arin mik'ewa tamata talek'o takoma INA bazai yiwwuba murya arikece tace "meyayi zafi shiba wuta ba zauna zauna kiji"
Zama Fiddert tayi tana fad'in "koke fa amma arzki na kiran ki kina k'i amsawa uhmm" tawani tab'e baki,
Ajiyar zuciya Jummai tasaki kamun tace "akwai wata bazawara anan bayan layin namu auren ta hud'u kuma bawata babba bace batafi 23 ba"
Kai Fiddert tajinjina kamun tace "dakyau tashi muje inganta saina tura mata hoton ta intayi shikenan"
Ba musu tad'auki gyalen ta dayaci uban datti yafara tattarewa tayafa
Batare data nema izinin mijin nataba sukai waje duk da tana cikin fargaba amma hakan bai hanata fitanba dan daga anbata dubu d'ari biyun nan zata biya Alhaji Buba kud'in sa ne tahuta daga nan kuma tasan inda zata karwad'a Nahisa dan kam tagama zama mata agida addu'a tafara yi aranta Allah yasa Fiddert tayarda tatafi da ita can birni tadinga mata aikatau,
Kasantuwar babu nisa yasa tacema Fiddert din sutafi ak'asa basai sun shiga motan ta ba,
Gidan su Halillaya sukaje yarinya CE k'arama ba laifi kyakkyawa CE dan ba bak'a bace haka ba faraba sannan tana da hanci Halillaya y'ar balaja'u CE wanda hakan yasa take ta yawon aure domin y'ar bala'e CE na bugawa ajarida shiyasa idan tayi aure maza suke sakin ta sbd bala'en ta awaje sika sameta tana toya k'osa suna k'arasowa tafara fad'in "Hajiya Jummai ikon Allah tasha baki ab'oye lumbu lumbu wutar k'aik'ayi daga ina zuwa ina nasan banza bata kai zomo kasuwa saikuma naji Nahisa taso kashe Alhaji uhm bara nayi shiru dai ina zuwa kota samu ne?" tak'arisa maganar da d'an satan kallon Fiddert dake danna waya kamar bata san da mutun ba nan ko kallon k'asan ido take mata,
Yak'e Jummai tayi da ace bada Aunty Fiddausi suka zoba saitaci kutumar uban Halillaya amma taci bashi baki ta tabe kamun tace "Halillaya idon gari kowa yazo K'uje bai gankiba yasha haushi matar yayana narako" tak'arisa maganar tana kallon Aunty Fiddausi,
Tun daga yanayin ta Fiddert taga bata mata ba dan haka tama Jummai alamun su wuce,
Ahanya ne Jummai takalli Fiddert jiki asanyaye tace "batayi ba ko?"
Baki tamere tana yamutsa fuska tace "wacce bata waye ba nake so gaskiya wannan dagani idanun ta yabud'e dayawa"
Jikin tane yasake sanyaya tace "aiko dai ita kad'ai CE bazawara anan k'auyen saidai ko a turunku kilan kisamu"
Tsaki taja tana d'aga wayarta ganin Zee ne ke kiran asanyaye tace "sister ba'a dace ba fa amma zan bincika kafun nadawo insha Allah" shiru tayi kamun tace 'karfa ki d'aga hankalin ki komai zaizo da sauk'i"
Shiru tasake yi alamun sauraro saikuma tace "to zanyi k'okari kinji k'anwas"
Yanke wayar tayi daidai suna shan kwana k'ofan gidan acike da mutane suka hango k'irjin Jummai ne yafara dukan tara tara tana wani irin zare idanu kamar ace kek ta arce amma saita maze,
Fiddert ne tace "a'a taron menake hangowa acan?"
Yak'e tasaki hawaye na gangaro mata tace "akwai matsala nidai daga nan zan juya Aunty Fiddausi Allah yatsare" tafad'a tana juyawa dan jitake kamar tazura aguje, Da sauri Aunty Fiddert d'in tarik'ota tana fad'in "wai meke faruwa ne Jummai tunda nazo naganki awani firgice gaya min menene yafaru?"
Kuka Jummai tafashe dashi tana fyace majina da gefen gyalenta tafara kora mata bayani,
Kai kawai tagirgiza cike da mamakin son kud'in Jummai da mijin nata nisawa tayi tana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ashe akwai wad'anda sukafisu son kud'i lallai kallon yanda Jummai take afirgice tayi kamun tace "muje muji meke faruwa dan ko kingudu kinsan hukuma zata binciko ki dan haka muje insha Allah tunda inanan komai zai tafi daidai"
Gaba d'aga itadai Jummai afirgice take babu yanda zatayi ne yasa tabi bayan Fiddausi suka k'arisa.




JOINING TWO DIFFERENT THINGSWhere stories live. Discover now