13&24

121 5 0
                                    

🌺🌺🌺🌺

*JOINING TWO DIFFERENT THINGS*
                 "'Gamin Gambiza"'
       🎍🎍🎍

             *BY*

      *UMMU SUMAYYA*
               #Bintubaby
https://www.wattpad.com/user/Bintubaby

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏽*

                  🆓 *PAGE*
            1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣


Cike da takaicin sa yace cikin d'aure fuska "Abunda nake so kake aibatawa kaban mamaki Mustapha koda shike ba laifin kabane laifina ne dana sake dakai har nake gaya maka sirrina matuk'ar zaka soni dole kaso Lubaila idan kuma kaima dawata manufar kake sona to dan Allah karka sake zuwa inda nake domin akan Lubaila babu abunda baxan iyaba dan haka kafita min a office d'ina kafun nasa afidda kai"
Yak'arisa maganar yana had'a hannayen shi biyu waje d'aya,
Da mamaki tsoro dakuma al'ajabi Musty ke kallon Safwan da gaba d'aya yacanza alokaci d'aya anya yarinyar nan ba wajen y'an bori takai sunan abokin shiba kwafa yayi kamun yace "Safwan nikake kora dan nagaya maka gaskiya to na na rantse da Allah babu inda zanfuta saidai ka kira afutar dani mtssss" yawani ja tsaki yana gyara zaman shi yacigaba da dannan wayar sa,
K'wafa shima yayi yana hararan shi yacigaba da aikin shi tabbas Musty wani jigone na rayuwar shi dako yarabu dashi dole sai yanemo shi domin su d'in harshe da hak'ori ne tun suna yara suke tare kuma Musty yakan tayashi son abunda yake so akoda yaushe amma why yake son soke auren shi da Lubaila table d'in yabuga da d'an k'arfi yana fad'in "no" kafun yajingina da kujerar idanun shi ya alumshe afili yafurta "insha Allah ke alkairi CE agareni kuma wataran zanyi alfahari da auren ki hakama wad'anda basu so auren ba zasuyi alfahari da auren" yak'ara sa maganar yana jujjuyawa akujeran,
Baki Musty yatab'e kamun yace "Buddy yakamata kasan abunda kake kana da kyau kanada kud'i kanada natsuwa uwa uba kwarjini ga yammata nan dayawa nasan duk wacce kataya baka za'ai amma ka k'are aguzuma sa'arka haba dan Allah wallahi ko k'anwar Samira kanema tsaf za'a baka yarinya ga kyau ga kamun kai but kayi tunani ni nabarka lafiya tunda kafasa sawa afidda ni d'in" yayi maganar yana tashi daga kujerar sa,
Tunda yafara magana yawani bud'e idanun shi ya kafe she shi dasu kamar meson karantar wani abu ganin zai tafi ne yasa yad'an sauke ajiyar zuciya kamun yace "excuse me Alhaji Mustapha nasha gaya maka cewar bazan tab'a auren wacce karatun ta bai haura degree ba burina auren mace classis wacce tasan kanta wacce zata kula dani burina in auri fara kyakkyawa coca cola shape taya zaka dinga min tayin bak'ar mace mezanyi da bak'ar mace kuma kwaila ma kai kanka mekake samu awajen Samiran? Inace kai ke kula da ita inkayi tafiya kadinga k'iranta kenan baby kinci abinci kinyi kaxa kinyi kaxa komai kai ke mata ba ita ke maka ba shine kake so na auri k'anwar ta wanda ko 20 years bata haura ba bata gama ma secondary school ba bata san menene luv ba nine zan koya mata ko? So  sorry to said again black women is not my type farar mace coca cola shape mastering degree itace burina najima ina searching right known Alhamdulillah domin addu'ah ta bata fad'i k'asa ba nasamu kuma dukkanin bincike nayi komai daidai dan haka idan kasake aibata min Habibati na wallahi rufe idanu xanyi namaka rashin mutunci dan haka zaka iya tafiya" yak'arisa da nuna mai k'ofa,
Murmushin takaici Musty yayi yakalle shi yace "Buddy kenan daga yau bazan sake zuwa inda kake ba bangani ba balle na tanka and maganar gaskiya wanda kasa yamaka bincike akan Lubaila koma waye yayima shigo shigo babu xurfi ne kuma yanxu nasake tabbatar wa cewa ba Lubaila kake so ba surar jikinta kake so kayi tunani wannan jikin dakake gani daga zarar an haihu magana tak'are kuma ko rantsuwa nayi bazan tab'a kaffara ba duk yarinyar data wuce secondary school ta tafi jami'a bako wacce bace virgin akwai but sunyi k'aranci balle wacce takai masters awannan lokacin wad'anda suke under secondary schools d'in bako wacce take kammalawa lafiya ba saboda suna shekaru mafi hatsari sai wacce Allan yatsallakar tabbas kana ruwa kusa da kada, malam bak'ar mace duniya CE Alhaji Safwan sai wanda ya aura bak'ar mace zai san quality d'in ta test and truth munji mun shaida komai zamzam atashi lafiya angon Lubaila''
Yak'arisa maganar  yana nufan k'ofa yana wata iriyar dariya ta shakiyyanci,
Da idanu yaraka shi kamun yad'an dafa kanshi dake sara mai dan arayuwar shi yatsani hayaniya tsaki yaja yamik'e cike da takaici wayoyin shi da brief case yakwasa afusace yabar office d'in lifter yahau sai uban tsaki yakeja dan yau kam amb'ata mai rai yana sauka yaba driver kayayyakin yashiga masjid yin sallah dan har antada bayan ya idar ne yana azkar yaji andafa shi waigowa yayi yaga Musty dasauri  yamik'e yanajan tsaki yafita Musty mezaiyi ba dariya ba,
Koda yashiga mota idanun shi yalumshe yanajin wani irin ciwon kai ga zafin maganganun Musty tsaki yaketa ja har suka isa gida,  yanzuma ta k'ofar baya yashiga dan yasan matar Dad na iya k'ara mai wani tension d'in.

JOINING TWO DIFFERENT THINGSWhere stories live. Discover now