11&12

108 5 0
                                    

🌺🌺🌺🌺

*JOINING TWO DIFFERENT THINGS*
                   '''Gamin Gambiza'''
                        🎍🎍🎍

                     *BY*

           *UMMU SUMAYYA*
                   #Bintubaby
https://www.wattpad.com/user/Bintubaby

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...📚✍🏽*

            🆓 *PAGE*
      🅿️1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

Wani irin banzan kallo ta watsa mai tana shigowa d'akin ranta amatuk'ar b'ace tasa hannu tad'ago Nahisa dajikin ta yasaki kamar ta mace nan ko tsaban jigata ne hijab d'inta dake yashe tad'auko tayafa mata kamun takalli Garbati tace "tir dakai matar datake uwa gareka kake shirin haik'e mawa nayi nadaman haihuwar ka ban san  barbaran naka yakai nan ba Allah ya isa tsakani na dakai dan ba wannan tarbiyyar na baka ba"
Tana k'arisa maganar ta tallafi Nahisa suka bar d'akin,
Hajiya Tala tasake komawa d'akin ne dan jikinta bai bata da yaran ba dama nan ta iske Salele shi kad'ai koda ta tambaye shi Nahisa da Garbati nan yadinga mata kame kame shine fa tanufa can b'angaren cikin tashin hankali.
Ajiyar zuciya take ta sauke wa tana k'ara gode ma Allah dayasa wannan d'an iskan  bai keta mata haddin taba wani sashi suka nufa daban inda sukuma sashin ciki da rumfa ne akan gadon me rumfa dayaji katifa tamata masauki bakin ta bai d'auke daga yimata sannu ba tunda suka fito daga wancan sashin idanun ta dasuka mata mugun nauyi ta lumshe tana gyad'a mata kai kurum, murya atausashe take kwantar mata da hankali ganin kamar bata yarda da itaba "ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru dake anan dayardar Allah kinji"
Kai tasake d'aga mata btare data bud'e idanun ta ba dan yau kam sunyi munanan gamo,
Futa tayi ad'akin bajimawa tadawo ta lullub'eta da bargo still idanun ta na lumshe kamar me barci nan ko tunanin inda mahaifanta suka tafi suka wofantar da ita take gaba d'aya jitake gwamma mutuwa da wannan rayuwar data tsinci knta daga wannan sai wannam Allah shine masanin b'oye shi yasan abunda yab'oye atata rayuwar tarashin galihu da rashin y'anci ahaka gwanin iya sata yayi gaba da ita.

Sanyin asubahi ne yasake farkar da Alhaji Buba inda yawani tashi afirgice yana fad'in "Nahisa ta nizaki kashe to wallahi Rabe sai yabiya ni kud'ina dan bazan zauna da wacce keneman kaini lahira batare dana mori kud'i na ba k'arya  kike wallahi k'arya ne saikun biya ni abunda nakashe azzalumai macuta kawai kahad'ani da meneman yin ajalina" yafad'a yana zambarma da ihu kamar zai fasa d'akin har saida Salele yad'an danne shi yana hararan shi cikin takaici,
Hajiya Tala dake tsaye daga gefe cike da takaicin mijin nasu takauda idanun aranta tace "ia intak'amar namiji aure aure wataran sai ya auro wacce tasha k'arfin sa wannan saka mako ne kafara gani tun aduniya"
Daga haka yasake komawa barci duk ajiyan zuciya suka  sauke kamun tamik'e tafuta tana fatan idan zai sake farkowa yafarko cikin hankalin sa,
Koda takoma taga yanda numfashin ta ke futa lokaci zuwa lokaci takan d'an firgita addu'ah tad'an dinga tofa mata tsayin lokaci kamun tazuba tagumi cike da damuwa dan sosai takejin Nahisa cikin rai da zuciyar ta kuma zata tsaya tsayin daka wajen ganin Alhaji bai cutar da yarinyar dabata da maraba da marainiya ba.

****************

Aranar baiyi barci mai dad'i ba juyi kawai yake bisa gadon sa yanajan tsaki cikin takaici da b'acin ran da matar Dad tasa mai ak'arshe dayarasa mafuta dole yatashi yaje yad'auro alwala yafara mik'a kukan sa ga ubangijin talikai sai wajen k'arfe uku yakwanta inda bajimawa yasake yin makamancin mafarkin dayasaba akan wata yarinya dake ta kuka tana mik'o mai hannu kanta atsakanin cinyoyinta tun shekaru hud'u baya yake irin wannan mafarkin kuma yarasa ma'anar mafarkin sometimes idan yayi mafarkin yfarka yakan jima bai koma ba ajiyar zuciya yasauke yana kallon agogo dake nuni da k'arfe 4:43 tsaki yaja ganin asuba ta gabato sauka yayi akan gadon yasake fad'awa toilet al,wala yasake d'aurowa yazo yacigaba da mik'a ma Allah lamuran sa bashi yasamu barci ba sai bayan yy sallar asuba,
K'arfe tara yasake farkawa cike da damuwa saka makon mafarkin daya kuma yi ada saidai yaga yarinyar kanta atsakanin cinyoyinta tana shashshekan kuka but na yanzu d'in yasha bamban dana ko yaushe kan gwoyinta taduk'a tana rik'e da k'afafun shi tana fad'in "katai makeni dan Allah da darajan iyayen ka dake k'asa" kukan datake bak'aramin tab'a shi yayi ba duk dacewa acikin mafarki ne haka yafarka jikin shi jik'e da zufa duk da ac dake cikin d'akin kuwa idanun shi ya lumshe yana shafa suman kanshi kamun yasauka agadon cike da nastuwa wanka yayi yafito d'aure da tewol while dawani ahannun shi yana goge kanshi komai yau cikin laziness yake yin sa domin har yanxu yanajin sautin kukan ta cikin kunnuwan shi tana fad'in "kataimaka min!" Bai santaba bai tab'a ganin taba taya zai maka mata indeed ko amafarkin bai tab'a ganin fuskarta ba idanu yalumshe yayi shiru for some second kafun yashirya cikin suit yellow da neck tied fari takalmi half cover shoe fari gashin kanshi yataje yayi oiling nashi yagyara sajen shi yana kallon kanshi turaren white crystal yad'auko yashafa kad'an saboda k'arfin sa sannan yad'auki wayoyin sa da brief case yabi ta k'ofar baya,
Tunda yaje suka shiga meeting domin shi kad'ai eke jira kuma yaje vary late sai twelve suka fito daga meeting d'in yana zuwa sectaren shi ya mik'a mai sak'o sannan yace Madam Lubaila tazo neman ka but nace kashiga meeting shine tace zata jiraka tana visitor room,
Umarni yabada kan ace tashigo shikuma yashige office d'in nashi yazauna akan kujera mai uku dake cikin office d'in yana duba miss call's d'in da akai mai Dad biyu Sweet Momma uku sweet Momma yadanna ma kira yana kara wayar akunnen shi Lubaila na shigowa office d'in tana d'aga kiran idanun shi ya lumshe yana d'aura k'afa d'aya kan d'aya yace "Good evening Sweet Mommana the best in the world"
Daga can side d'in tasaki wani k'ayataccen murmushi  tana muskutawa daga kan hadadd'un sofa dasuka k'awata tamfatseten palourn nata tace "Son what's wrong with your"
Murya asanyaye yace "nothing else Sweet Mommana why did you ask?"
Kai tagyad'a cikin rashin yarda tace "Safwan something's is really happen to you inajin hakan ajikina kuma muryan kama tanuna hakan ko bankai  kafad'a min damuwar ka bane?"
Murmushi yad'an yi kad'an kafun yace "no Mommana kin wuce komai agareni you're the best in this world"
"Idan dagaske ne abunda kafad'a gaya min meke faruwa"
Ajiyar zuciya yasauke yana bud'e idanun shi akan Lubaila da itama shi take kallo kamar wata mayya yana kallon ta tawani d'auke kai kamar ba ita ba muryan shi yasake sanyayawa yace "Mommana aure nake son yi but Dad yace dole sai Mom tasan da mganar at the end dana gaya mata shine tace" nan yakwashe dukkanin abunda yafaru yagaya mata,
Shiru tayi for some second bayan yagama gaya mata cikin b'acin rai tace "don't worry Son insha Allah everything will be alright kuma zankira Basheer d'in da ita kanta Zainab d'in zamuyi magana ta fahimta insha Allah nan da two weeks zan shigo inyaso saina tsaya ayi bikin kamun na koma"
Cike da farin ciki yace "That's my Momma thank you so much"
Murmushi tayi jin yanda yake farin ciki tace "haba son don't mentioned it niba uwa bace kome zanyi dan ganin nasamar ma d'ana farin ciki zanyi shi ai matuk'ar bai kauce ma addinina ba"
Idanu shi yasake lumshewa kamun yasauke su akan Lubaila yace "okey Momma ga Lubaila ku gaisa"
D'an shiru tayi kamun tace "who is she"
Dariya yayi kad'an kamun yace "surikar ki mana"
D'an gimtse fuska tayi duk da baya ganin ta tace "where are you right known?"
"Ina office Momma"
"Metazo yi office d'in ka amatsayin ta na budurwar ka" tajefa mai tambaya batare dayayi tsammani ba
Jikin shine yayi mugun sanyi yace "Momma muna contract da company Dad d'in tane wanda itace CEO acan d'in"
"What?"
Idanun shi yad'an zaro yace "please Mommana don't say anything bad she's self-restraint at all"
Kai kawai tagirgiza tace "OK bring her phone"
Asanyaye yamik'a ma Lubaila wayar yana dana sanin fad'in gata su gaisa,
Lubaila da duk jikinta yayi sanyi dan tunda taji yafara  cewar Dad da Mom d'in shi basa son auren jikin ta yayi mugun sanyi and known taji wayar shi da wata d alamu tana da matuk'ar muhimmanci agaresa itama alamun kamar bata son ta itama ajiyar zuciya tasauke takarb'a wayar jikinta na wani irin kyarma duk da tana k'ok'arin b'oye yanayin ta kar yagane takara akunnen ta tace "Good evening màà"
"Evening how are you?"
"Fine"
Tafad'a atsorace jin yanda ta amsa ta,
Yatsina fuska Momma tayi gaba d'aya sai taji bata mata ba tunkan ma taganta murya ad'age tace "shekarun ki nawa?"
Sosai gaban Lubaila yafara dukan tara  tara tad'an d'ago takalle shi yamata murmushi knta tasake duk'arwa kamar bataji metace ba tace "hello"
Wani irin murmushi Momma tasaki kamun tace "am hearing you I said how old are you"
Jikinta yasake yin wani uban sanyi kamun cikin in'ina tace "am twenty four"
"Are you sure?"
Tace jin yanda muryn ta yake creaking,
Kai Lubaila tagyad'a kamar tana gaban ta kamun tace "am sure"
"Ok msha Allah any where inna shigo Nigeria zan zo har company ku"
"Oh...ohkey na..na..nago...de" tafad'a tana mik'a mai wayar gudun karta bijiro da wata maganar,
Jikin asanyaye ya amsa wayan sukai sallama da Momma ya kashe wayan yana kallon Lubaila yace "karki damu fa Momma naganin ki komai zai wuce dan tana da sauk'in kai k'anwar Mom d'ina ne"
"Ayya" tafad'a tana mik'a mai wasu document,
Amsa yayi yana mik'ewa yakoma kan kujerar sa kamun yaxauna akai knocking yace "yes"
Wani kyakkyawan handsome guy fari amma ba sol ba yashigo office d'in yana sanye da suit ash color bakin shi d'auke da sallama,
Amsawa yayi yana fad'in "Musty baka da mutunci fa sai yau kasamu sak'ona kenan?"
Dariya wanda aka kira da Musty yayi kafun yabashi hannu yn fad'in "wallahi am too busy that's why ban kira kaba kuma jiya jiyan nashigo Nigerian that's why but kaina bisa wuya saraki ikon Allah"
Murmushi Safwan yayi idanun shi bisa system kamun yace "ka kyauta ai"
Dariya Musty yayi yana d'an kallon Lubaila kamun yakauda idanun shi tuna inda suka tab'a had'uwa da ita sake kallon ta yayi ganin tacanza sosai fiye da kwanakin baya baki yatab'e yana dawo da kallon Safwan suka had'a idanu murmushi suka sakarma junan su Safwan yace "Buddy kazo adaidai ga Lubaila ku gaisa she's my wife to be insha Allah"
Wani irin kallon shi yake kamun yajuya yawatsa ma Lubaila da tunda yashigo tasake dana sanin zuwa office d'in murya ad'age yace "hi yakike hope you're doing well"
Asanyaye ta amsa da "fine" kamun tamik'e tana kallon Safwan tace "I want go"
Kallon yanda tayi yayi saiyaji babu dad'i dan gaisuwan da Musty yamata bai dace ba,  murmushi yasakin mata yace "ok letter i will call you take care"
Murmushin yak'e tamai kamun  tace "thanks byeee" tayi weaving d'in shi shima yayi nata kamun tadauk'i jakanta tana satan kallon Musty dake danna waya tafuta dafatan Allah yasa yarufa mata asiri,
Safwan kuwa aikin shi yaci gaba dayi batare dayama Musty magana ba,
Musty ne yace "Buddy are you sure Lubaila is your wife to be?"
Kamar bazai amsa shiba saikuma yace "yes anything else?"
Fuska sosai Musty yab'ata kamun yace "Lubaila fa kace are you in your own senses Safwan ?"
Musty yak'are maganar cikin takaicin abokin nnashi,
Kallon shi Safwan yayi kamun yace "ban fahimce kaba wani aibu take dashi yarinya kyakkyawa ga uwa uba diri ga hankali me ake nema ga macen aure bayan wannan?"
Kai Musty yarausayar kamun yace "Lallai kam kashige dayawa amma nizan gaya maka gaskiya dan bazan ga abunda zai cutar dakai nayi shir..."
Azafafe Safwan yace "enough Mustapha idan kai bata maka ba ni tamin dan haka ka kiyaye kalaman ka"
Murmushi Musty yayi cikin takaici yace "Safwan kai maraya ne ba uwa ba uba katuna mak'iyan ka suna zagaye dakai ne and menene zaisa ks auri Lubaila yarinyar da babu wanda bai san karuwar cikin gida bane and mezakai da guzuma y'ar 28 to 30 years dan narantse bazan tab'a kuma kaffara ba Lubaila koda ka girme ta da kad'an ne ga yammata nan masu hankali da natsuwa zaka k'are a tsohuwa sauran wasu to wallahi kasake tunani dan totally ma ban yarda da Lubaila ba turo ta akayi kasani baka da mai fad'in maka gaskiya sama dani"
Tunda yafara magana yawani k'ank'ance idanu yanajin kamar yana saran shi da wuk'a Lubaila yake aibatawa haka ya subhanallah lallai da wanine ba Musty ba da sai ya wulak'anta shi amma ko yanzu shi d'in ma sai yanuna masa kuren sa.....✍🏽

NEW YEAR PROMO
*GAMIN GAMBIZA*

*Normal group 200*
*VIP        group  400*
*Special group   700*
*Via 4210014214 eco bank and send the evidence of payment via 07017296839 y'an nijar sumin magana ta 07017296839 dan Allah banda vtu just numbers d'in VIP and special group inba yazama dole ba karku turamin kati kutura min ta bank ko pos kubada charges d'in acikin kud'in nawa*

Share it fisabilillah🙏🏼

JOINING TWO DIFFERENT THINGSWhere stories live. Discover now